44

3.6K 201 1
                                    

              💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 45

Binsa tayi dakallo tana k'unk'unai, amma baijitaba Dan yayi gaba abinsa.
    Safna tana dagacan saman kujera tana kallonsu, hawaye suka cika mata ido taisaurin saka handkyn daya bata jiya tagoge, ta Yanke shawara yau zatabi su Ameera sutafi gida, Dan inhar tana ganin bobo bata tunanin sonsa zai ragu azuciyarta barema ayi tunanin fita gaba d'aya, amma idan tayi nesa dashi k'ila taji sauk'in zuciyarta, Dan insha ALLAHU tayi tuba na gsky kenan.

Rahma tahad'a musu abincin Wanda dama tun d'azu ta tanada domin su, ihsan da Basma ne suka tayata d'auka zuwa 6angaren inna.
      Duk sunacan harda Ammar dawasu mutum biyu dabata saniba, bayan sun ajiye suka gaidasu, idanun bobo nakan matarsa, itama tasaci kallonsa ganin idonsa akanta yasa ta kauda idonta tareda Jan hannun su ilham suka fice.

...........................÷
      Bayan sallar isha'i su anty Hafsat sukace zasu wuce, Safna data gama had'a kayanta tamik'e itama, kallonta kawai Rahma takeyi amma batace komaiba, su dama su aunty Ameera tafad'a musu zata bisu Dan gidan yacika damutane kuma Rahma anan zata kwana itama, basu kawo komai aransuba sukace eh gara kawai tatafi gida.
      Har harabar gidan tarakasu saida suka Shiga mota taga fitarsu sannan takoma ciki.
       Amota Safna cikin dabara take share hawayenta, wata zuciyarta tana fad'a mata anya zata iya daurewa kuwa?, da sauri ta ce, "insha ALLAHU zan iya.

.+.+.+.+.+.
      Tafiyarsu Safna babu dad'ewa sosai bobo yashigo falon, wasu kallo sukeyi wasukuwama harsun kwanta, yagaidasu sannan ya haura sama, afalo yatarar dasu zaune sunata kulla kayan rabo, zama yayi yana fad'in wai Kodai yau anan zamu kwanane?.
     Kallonsa ammi tayi, ta ce, " nidama zaku barsu su kwanan Aida yafimin, idan bamu gamk'ullin nan yauba nasan zuwa gobe gidannan zai d'inke da mutane.
     Kansa yashafa yana d'an murmushi Ammi sudai gama kawai saimu wuce ko zuwa 12 ne.
     Hararsa Ammi tayi cikin wasa, ta CE, "fin k'arfi za'a nunamin akan 'ya'yana?.
       A'a Ammi mu mun isane.
    Hira sukaitayi har su ya ishaq suka shigo suka had'u gabad'aya sukayi k'ullin sannan kowa ya d'auki matarsa sukai gida.

Biki yacigaba da kankama cikin farin ciki, komai yana tafiya yanda yadace, washe gari da safe akayi k'unshi, zuwa yamma gida kam ya d'inke da bak'i na nesa Dana kusa, su Rahma kam aii ko ganinsu ba'ayi Duk sun zama busy, to barema su bobo manya manyan yayye.
     Da daddre k'arfe takwas aka fara d'ibar mutane zuwa wajen brother's night dasu bobo suka shirya, abokansu sosai suka gayyato, taron 'yammata da samarine kawai saikuma irinsu bobo masu mata, amma babu yara bare tsofaffi.
    Taro yak'ayatar kam masha ALLAH, amare da angwayensu ansha k'yau abin sai Wanda yagani, su bobo suntaka rawar gani irinta manyan yayye, ko INA yashiga yana mak'ale da matarsa abin zak'yk'yau da burgewa, 'yammata kam dayawa sun k'yasa, saidai ganinsa mak'ale da matarsa yakansa sushiga taitayinsu.
    Alhmdllh dahaka taro yatashi lfy kowa Yakama gabansa.

_washe gari_
     Aka d'aura auren khairiyya Aliyu Abdulmaleek hamshak'i da angonta Ahmad m sadiq, sai Khursiyya Aliyu Abdulmaleek hamshak'i da angonta Zaharadden usman Aliyu.
      Masha ALLAH d'aurin aure yatara d'unbin jama'a nanesa Dana kusa 'yan siyasa da masu mulki, 'yan kasuwama ba'a barsu abayaba.
    To khairiyya da khursiyya saimuce ALLAH yasanya alkairi yabada zaman lfy da zaman hak'uri.
    Hummmm abun mamaki wai harda alhaji sunusi dala a 'yan d'aurin aure, (araina nace su alhaji sunusi anji yaji🌶🤣 ahanun bobonmu😎😂😜) aiko bobo sai antaya MASA kallon banza yakeyi.
    Shidai baimasan yanayiba.

Bayan kammala d'aurin aure su bobo sukaima anguna  jagora zuwa cikin gidan, shidasu Yaya ishaq duk wankan farar shadda sukayi, masha ALLAH daka gansu kaga 'yan uwa jini d'aya.
      Har cikin falon suka Shiga anata gaisawa da 'yan uwa da abokan arzik'i, bakin anguna yak'i rufuwa hakama su ya sulaiman suna cikeda farin cikin yau k'annensu sunyi aure.
     Tunda sukashigo falon bobo yaketa baza ido domin hango Nusfulhayat d'insa, rabonsa da ganinta tun jiya bayan sun dawo daga faty.
    Ganin duk d'unbin taron Matan falon bai Gantaba har sama dasuka haura aka gaisa dasu ammi nanma bata nan baimaga Matan yayyensaba ko d'aya.
          Sakkowa yayi yabarosu a can, wayarsa yaciro a aljihu yafara kiran number ta amma bata d'aukaba, yana nan tsaye yanad'an waige waige saiga Nasiba zata shige itada wasu 'yammata, Nasiba ta gaidashi ya bobo ina yini.
   Juyowa yayi danson ganin wanene, oh Nasiba dama kinzo?.
   Wlhy nazo jiya Yaya, tunda nazo bangankaba kaida ya sulaiman, amma naga ya hamza da ya ishaq.
   Muna nan muma munyi busy ne da yawa, Dan ALLAH ko kin ganemin Rahma?.
   Aunty Rahma, naganta anan baya itada umminta da Ammi dawasu mata, saidai ban saniba ko sun koma ciki.
    Kai a'a bata ciki, amma ummi da Ammi nagansu aciki.
   Okey bara na duba maka ita.
    Ok thanks.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now