PART ONE

11 0 0
                                    

                       BABI NA FARKO
     Ƙasar Wanaka ƙasa ce mai arziƙin gaske, kuma ta mayaƙa ce tun fil azal.
Yawancin dukiyarsu ma sun sameta ne a
ganimar yaƙuna da suka yi ta yi, kuma yawanci su na samun nasara. Amma yanzu yaƙuna sun lafa ana cikin matsakaicin zaman lafiya da duk ƙasashe, har ma wasunsu sun ƙulla zumunta da maƙwabta.

     Sarkin Wanaka, Aadil Al-Hudhaifi, dogo ne kyakkyawa, sai dai shi mutum ne mai saurin fushi da nuna ƙasaita. Duk waɗannan ba su nesanta shi daga jama'arsa ba, saboda alhairinsa da kuma son nishaɗi.

     Ɗaya daga cikin abubuwan da aka fi
saninsa da shi shi ne son mata, waɗanda labarin kyawunsu da isarsu ya kai ko'ina a wannan ɓangare na duniya. Kuma duk inda ya ji labarinsu, toh ba shakka zai yi duk abinda zai iya, zai kashe duk kuɗin da ake buƙata, domin a kawo masa wannan mace. Hatta a cikin ƙasarsa, an saduda cewar duk wata mace mai kyawun gaske, toh abar kawancensa ce, kuma zai iya duk abinda zai iya domin ya sameta. A dai wajen tara mata a gida, ba shakka Aadil Al-Hudhaifi tuni ya keta iyakoki.

    A gaskiya, mafi yawancin hira a fadarsa,
hiƙayun mata ne masu kyau na ƙasashe daban-daban. Sarki Aadil Al-Hudhaifi ya kan raba kuɗi masu yawa ga mutanen da yake kira ''Fataken Nishadi'' domin su zagaya maƙwabtan ƙasashe neman labarin mata masu kyawun gaske. Duk wanda ya dawo masa da cikakken labarin wata kyakkyawar gaske da shawarar yadda za a sameta, ya kan sami kyautuka na ƙasaita.

     A irin wannan bincike nasa ne, labari ya iso masa cewar akwai wata budurwa wadda ba a san wadda ta fita kyau a ƙasashen kusa-kusa ba. Sunanta Ikhleemah. Sai dai kuma, mahaifinta, Sarki Whabi Khazri na Jadarwa ya sa sharuɗɗa ga duk mai son ya aureta. Waɗannan ƙa'idoji kuwa ya sa su ne da manufar faɗaɗa ƙasarsa, domin Jadarwa ƙaramar ƙasa ce wadda arziƙinta ya gaza na maƙwabtanta nesa ba kusa ba. Ance duk a wajen yaƙi ya yi waɗannan asarori, amma yanzu tunda yana da ƴaƴa mata kyawawa, ya maida su ababan shan fansarsa.

     Sharaɗinsa na farko shi ne: Lallai duk mai son Ikhleemah ya kasance sarki ne shi mai arziki. Na biyu, lallai sadakin ƴarsa ya kasance ɗaya bisa biyar na ɓangaren ƙasar daga inda suke da iyaka da Jadarwa.
Na uku, wani ɓangaren ƙasa haɗe da dukiyar kuɗi a cikin dinare da duwatsu irin su murjani, ko kuma na huɗu, dukiya zallah wadda za ta iya fansar wannan ƙasa, in ba su da iyaka, ko in ba a son ba da ƙasar.

     Jin waɗannan sharuɗɗa, sarki Aadil ya san wannan yarinya ta yi masa nisa a halin yanzu. Da farko dai su ba maƙwabta bane,
domin ba su da iyaka ɗaya. Akwai ƙasar Bikiram daga arewa a tsakaninsu.

     Na biyu, ba yadda za a yi ma ya iya yanke wani ɓangare na ƙasarsa ya miƙawa wata ƙasa da sunan sadaki. Kuma tunda Wanaka babbar kasa ce, fansar kashi daya cikin biyar ɗinta yana buƙatar dukiya mai yawan gaske, wadda in ya bayar toh kuwa Baitul Malinsa za ta duƙufa. Amma kuma, saboda ya tsimu da labarin kyawun wannan yarinya, sai ya tara waziransa a irin wannan harka domin su ba shi shawarar abinda zai yi. Shawararsu ta ƙarshe wadda ya yarda da ita, ita ce, ya san yadda ya shirya aka sato masa wannan yarinya tun kafin wani sarki ya aureta.

     Dalili kuwa, zai yi wahala ga ƙasar Jadarwa ta yaƙesu domin kuwa Wanaka ta fi ƙarfinta. Na biyu kuma kasancewar Bakiram a tsakaninsu, zai zama katanga, ballanta kuma sarkin Bikiram, Abul Yusfar, abokin marigayi sarki Al-Hudhaifi ne, wanda ya haifi sarki Aadil. A kan haka suka fara shirye-shiryen yadda za su sato wannan kyakkyawar yarinya, Ikhleemah.

*****     *****     *****    *****     ***** 

     Haƙiƙa duniya da faɗi take, haka kuma abin cikinta yawa gareshi. A can wata lahiyar daban kuma akwai wani gawurtaccen sarki mai suna, Subur Ibn Shahzaib wadda yake mulkin wata ƙasa Aksas.

     Birnin Aksas ya bunƙasa da ƙarfin arziki, yawan al'umma da kuma kasuwanci har ya zama abin kwatance a ko'ina cikin duniyar nan.

     Sarki Subur ya kasance mai tausayi, taimako da jinƙan talakawansa, Allah ya hore masa arziki mai ɗimbin yawa gami da kaifin hankali da hasashen gaba.

MASARRAFAR IKOWhere stories live. Discover now