PART TWO

3 0 0
                                    

                         BABI NA BIYU
     A can birnin Wanaka kuwa, A yayin da yake waɗannan shirye-shirye ne ya ji labarin cewar har wasu sarakuna sun fara kai ziyara Jadarwa domin su ga Ikhleemah ido da ido, su kuma ƙayatar da mahaifinta Whabi Khazri da irin kyautukan da za su iya kai masa na nuna arziki, kafin a fara zancen ƙasa ko kuma yawan dukiyar da Whabi Khazri zai nema a maimakon ƙasa don musanyar hannun ƴarsa ga aure.

     Nan da nan Aadil ya fara tunanin yadda zai fitowa wannan al'amari. Wasu suka ba shi shawarar ko ya nemi taimakon Abul Yusfar domin a hanzarta sato wannan yarinya, amma ya san wannan ba za ta yiwu ba duk da zumuncin da ke tsakaninsu, saboda sarki Abul Yusfar dattijo ne, kuma ba wasa a halayensa, sannan kuma kamar uba yake ga Aadil. Saboda haka, sai ya ga gara shi ma ya je Jadarwa ya gwada sa'arsa ya kuma yi masu alƙawarin zaman lafiya da juna da kuma yarjejeniyar tsaro da kai caffa, tunda ya san Jadarwa za ta buƙaci waɗannan a gaba. Maiyiwuwa ne a ci sa'a, Whabi Khazri ya auna waɗannan alƙawura a hankalce ya kuma amince. Wazirai suka ce kuma sun tabbata in dai har aka ba wa Ikhleemah zaɓi, toh Aadil za ta zaɓa, saboda ya fi duk sarakunan kwarjini da tsari da kyawun kamanni. Sai dai in ba ta ganshi ba. A jarumta kuwa da ma babu irinsa, kuma kowa ya san haka.

     Da wannan a zuciyarsa, sarki Aadil Al-Hudaifi ya shirya tafiya Jadarwa. Ya haɗa ayarin raƙuma masu yawa, duk ɗauke da kayan alatu iri-iri na alfarma da ya yi niyyar ya kaiwa Whabi Khazri da Ikhleemah.

     Sannan ya kwashi barada fiye da ɗari biyar ƴan rakiya ya kama hanya, wasu a kan dawakansu, wasu kuma a kan raƙuma. Tafe da su, akwai shanu fiye da hamsin da kayan abinci iri-iri. Saboda buƙatun hanya a duk inda suka yi zango.

     Ƴan kwanaki a kan hanya suka isa Bikiram, inda sarki Abul Yusfar ya yi masu masauki wanda ya dace da matsayinsu. Aadil da ma kamar ɗa yake gareshi, saboda haka, suka zauna suka tattauna wannan al'amari sosai, har ma da irin gudunmowar da Abul Yusfar zai iya.

     Aadil ya yi godiya, amma a duk hirarsu bai sanar cewar ko ta tsiya sai Ikhleemah ta zama tasa ba. Abul Yusfar ya yi masa fatan alkhairi da yarda cewar shi ne ma zai zama babban waliyi a wannan aure, sannan ya kawo wasu kyautukan ya ƙara masa, har da irin waɗanda za a iya ba wa ƴaƴan-sarki.

     Aadil ya ƙara ƙarfinsa, da kuma wannan zaton nasara, ya ɗaura sirdi suka doshi ƙasar Jadarwa. A kwana a tashi, har suka iso iyakar Bikiram Da Jadarwa, washegari kuma suka fara hango gine-ginen birnin. Daga nan ne, Aadil ya tashi jakadu goma, barada, suka garzaya gaba, domin su isa su sanarwa sarki Whabi Khazri labarin isowarsa ƙasarsa. Kafin magariba kuwa, Aadil da tawagarsa sun iso dab da garin.

     A nan bayan gari gabas, Aadil ya yi zango, ya kafa tantuna na ƙasaita, layi layi daga wata babbar da'ira wadda ta zama tamkar dandali. A gaban wannan dandali sai tantin Fadarsa kawai, wanda ya cika da kayan alatu da dardumomi irin na Isfahan da Bagadaza. Butocin shayi da finjalansu da farantai da cokula na gwal da na azurfa gasu nan birjik.

     Fitulu kuwa, ba a cewa komai, sai wanda ya gani. Nan da nan hadimai suka shiga aiki, masu dafa abinci suka fara yanka shanu, masu kaɗe-kaɗe da raye-raye kuma suka hau nasu. Kafin ɗan lokaci ƙankani, kai ka ce dama wannan alƙarya ce wadda aka santa gurin.

     Nan da nan labari ya shiga gari, har zuwa ga sarki Whabi Khazri, wanda tuni ya sami saƙo daga jakadan Aadil. A wannan lokaci da labari ya zo cewa har Aadil ya iso ya kafa tanti gabas da gari, Whabi Khazri, yana tsakiyar yi wa abokansa, sarki Yumsur na Yamalan liyafar girmamawa, tareda wasu sarakuna biyu, sarki Ashur na Jigawal da kuma sarki Zubair na Zumfur, waɗanda duk suka iso tsakanin jiya da shekaran-jiya, su ma a kan wannan buƙata.

     Dukkanin waɗannan sarakuna, a masaukan fadar Whabi Khazri suka sauka, kuma har yanzu ana jiran wa su sarakuna, aƙalla biyu da za su iso yau ko gobe da safe. Akwai Isaini na Yarwal da kuma Musabu na Kataiguma.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 05, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MASARRAFAR IKOWhere stories live. Discover now