*°🔘°K'AWAYE NE SANADI°🔘°*
             *1441H/2020M.*
        

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMMY M. NA'IGE✍🏼*


*SADAUKARWA GA:-*
*FAUZEEYA M NA'IGE*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*


*SHAFI NA 2📑*

*__________📖* Sai da tagama raba musu kuɗi sannan tace, "kobari naje wajan principal naji miyake nemana".

Sai ɗayar wadda ake kira Maryam tace, "tatsoniyar gizo bazata wuce ta ƙoƙiba, nasan ba abinda zai ce sai dai araba kayan da akakawo na visiting dashi".

Sai Ruƙayya tace, "kubarshi yaci, saura kwana nawa mubar makarantar, inya isa yaje gida idan inkawo yace zaici".

Murmushi Jambe tayi wanda yaƙara mata kyau da annuri, tace, "ku kyaleshi ba komai, idan ma duka yace yanso, to ni zanbarmasa".

Kafin tarufe baki Safiya dake kallonsu tunda suka fara magana batace komaiba tace, "kutumar uba, wallahi baki isa kiyimuna ƙwaleleba koda ke aka kawoma sai yadda mukayi dasu".
Tafaɗi haka haɗe da jifar Jamila da harara.

Murmushi Jambe tayi, haɗi da tashi tafara tafiya tana faɗin, "sai mun haɗu hostel".
Batajira jin me zasuce ba takama hanyar office ɗin principal.

Da sallama tashiga ciki, amsawa yayi tare da bata izinin ta ƙarasu daga ciki, bayan ta shigo sannan ya dubeta da kyau yace, "kuɗin da senator yabaki zaki bani nawa kaso".

Murmushi tayi haɗi da sanya hannuta cikin aljuhun wandanta ta ɗauko ƴan ɗari biyar² masuyawa ta ɗora masa kan  table ɗin dayake zaune.

Ɗauka yayi ya ƙirga, sannan ya girgiza kai, sannan yace, "to yanzu sai araba waɗannan kayan ko?".
Yana faɗa yana nuna kayan da aka kawo mata na visiting.

Tace, "karaba sai kaɗau naka, nawa ƙason sai abawa juniors sukamin ɗaki".

Tana faɗar haka ya watse haƙura sannan yace, "to² kije yanzu zan raba nabusu sukaimiki".

Tau tace dashi, sannan tajuya tayi hostel batare da ta koma wajan ƙawayen taba.

Batajima da zamaba sai ga juniors sun shigo ɗakin dauke da kaya akansu, tun basuyi maganaba ta nuna musu wajan da zasu aje mata kayan, sai da suka gama ajewa sannan ta ɗauko ɗari biyar ta basu tace suje suraba, bayan sun fita tazo taga yadda kayansuke, sosai taɗanji zafin abin,sabida yaɗibi fiya da rabi kayan, wato ƙaso uku yayi ya ɗau ƙaso biyu ya bata ɗaya.

Tana cikin haka sai ga ƙawayenta sunshigo cikin ɗakin suna faɗi, "Jambe ina kayanmu?".

Kasa buɗe baki tayi sai dai tanuna musu da hannu almar gasu.

Ƙarasowa sukayi wajan kayan, dubansu sukayi da kyau, sannan sukace, "wallahi basu kaɗaibane".
Sun faɗin haka tare da kallonta.


Sai da ta haɗe fuska sannan tace, "iyasu ya aikomin, amma idan kuna so ku ɗauka gabaki ɗaya na barmuku".

Sai Safiyya tace, "tau bari muɗauka muraba har ke, dan yanzu inmuce munci, dan nan bada jimawa ba kowace zata kama gabanta, wasu aure zasuyi wasu ko karatu zasuyi, amma nikam aure zanyi".
Taka ƙarshin zanci ɗauke da murmushi afuskar ta.

ƘAWAYE NE SANADI.Where stories live. Discover now