*°🔘°K'AWAYE NE SANADI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*SHAWWAL/JUNE.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMMY M. NA'IGE✍🏼**SADAUKARWA GA:-*
*FAUZEEYA M NA'IGE*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SHAFI NA 7📑*
*__________📖* Yana ganin ta fara bacci ya ɗauketa ya kai bedroom ɗinsa, kwantar da ita yayi sannan shima ya kwanta haɗi da jawota jikinsa yana wasa da ita har bacci yayi awun gaba da shi.
Shine bai farka ba sai ƙarfe biyar na yamma, driver yasa yayimasa take away guda biyu, ɗaya yaci ya bar mata ɗaya, sannan yayi wanka, ya zauna yana aiki da laptop ɗinsa.
Yananan zaune yana aiki har ƙarfe taren dare, mutsi da yaji yasa ya ɗago kansa, ido biyu sukayi da ita, amma yana kallonta yasan har yanzu abin da ta sha bai ida sakinta ba, murmushi yayi haɗi da tashi ya rungomuta ya ƙarasu da ita kan kugera sannan yaje ya ɗauko mata nata take away ya buɗe ya fara ciyar da ita har sai da ta kushi, firij yaje ya ɗauko irin lemon jiya tare da ruwan gora yazo ya tsiyaya mata ya bata a baki tashi, sai da yaga tasha sosai, sannan ya zuba ruwa ya bata, ba tasha ruwan da yawa ba, nan ta sake faɗawa jikinsa sai bacci.
Ɗaukar ta yasakeyi ya kai toilet, wanka yayi mata sannan ya naɗe ta da towel kamar wata ƴar Baby , bedroom ya kaita, saida ya shafeta da mayuka musu ƙamshi sannan ya kwantar da ita saman gado haɗi da gyara mata kwanciyar ta.
Sai da ya kammala akin da yake sannan yaje yayi wanka ya kwanta.
Tun ƙarfe biyar na yamma Mama ta ake Awal tace yaje gidasu sakina ya kiramata Jamila amma a kace batanan, dan kosu su Sakina ɗin basunan sunje bikin mutuwa a church , sosai ran Mama ya ɓaci, dan a tunanin ta tabisu church ne.
Har goman dare Mama tasake aikawa a kace basu dawo ba Baba yace, "tunda basu dawo ba mu kulle ƙofar gida, dan ko sun dawo nasan can zata kwana".
Sai Mama tace, "ni gaskiya bazan yarda na bar ƴata budurwa ba ta kwana wani gida, kuma ko gida kidan ƙabila wada bata addinin musulunci ba".
Dubanta Baba yayi yace, "to ni dai bawan da zaki saki aika cikin yaran nan, kuma ni bazanje nemanta ba, dan haka sai da safe".
Yana faɗar haka ya tashi yashiga ɗaki ya kwanta.
Hawayen da suka zuba a idonta ta goge, dan itakam yadda takeji bazata iya bacci batare da taga Jamila ba, gayarama yaranta mukwancirsu tayi sannan ta ɗau mayafi ta fita.
Koda ta fita ba kowa a unguwar, tsit kakeji, kuma gashi ko wutar nepa babu, kuma ba fitala a hannunta, haka ta fara tafiya cikin duhun dare har ta kai gidansu Sakina, kuma akwai ɗan nisa kaɗan da gidan su da nasu, bata damu dawani dare ba, ita dai burinta taga ƴarta ga hannun ta.
Koda tashiga gidan Mamar su kaɗai ta sama, gaishe ta tayi haɗi tambayar ta su Sakina da Antonia , sai Mamar su tace,
"basa nan sunje wajan ƴan uwansu kuma zasuyi kwana biyu su dawo ba".
Dubanta Mama tayi tace, "har da Jamila suna tare?".
Sai Mamarsu tace, "a'a basu tare da Jamila dan tare dasu muka tafi church ".