Page 1

917 46 3
                                    

*AL'AMARI! Book 1* 
           *1441H/2020M.*      
                *SHAWWAL/JUNE.*                                                           

*©️Halima H.z*

*IN THE NAME OF ALLAH*
_The most Beneficent and the most merciful. Praise be to Allah lord of the words. The beneficent the Merciful. Master of the Day of judgement. Alone we worship Alone we ask for help. Ya Rabb show me the straight path._

*P-01*

*FUFORE LOCAL GOVERNMENT, ADAMAWA STATE, WAIRO DISTRICT, WAIRO FAMILY HOUSE...*

Sunturi kawai ta ke faman yi a tamfatsetsen parlon ta, ta kai mari ta kai gwauro, duk da AC ɗin da ke bugawa a parlon amma zufa ce ke karyo mata, kai da ka ganta kasan a kwai babban *AL'AMARIN* dake yawo a ranta.

Can ta nemi ɗaya daga cikin kujerun parlon ta zaune tare da harɗe ƙafafunta ta na girgiza su.
Sai da ta sauke doguwar ajiyar zuciya sannan ta ɗauko wayar ta, cikin contact ta shiga ta danna kiran wata lamba, sai dai ko da ta kira wayar a kashe ta ke.

Ƙaramin tsaki ta yi da ganan ta fita daga ɓangaren kira ta hau manhajar whatsapp, Searching suna tayi tana dubawa kuwa tagan shi online, ganin hakan ta fara rubutu domin aika masa da saƙo.

"Abdallah kana ina? Na kira wayar ka a kashe".
Babu ɓata lokaci ya dawo mata da amsar saƙonta kamar haka.

"Mama ai ɗazu na faɗa miki zan kai motata gyara, yanzu haka ina can wurin, ƙaramar wayar kuma da ki ka kira babu caji ne".

"Oak to kaga ka baro wurin nan yanzu ka dawo gida a kwai maganar da nake so muyi".
"tom shikenan Mama. Ina fatan dai lafiya ko?".
"kusan hakan, ni dai abinda na ke so da kai ka hanzar ta don Allah".

Daga nan ta kashe data ta sauka, shima kuma cikin hanzari ya miƙe domin zuwa amsa kiran mahaifiyar ta shi.

Bai ɗauki rabin awa ba yana tuƙi ya iso gida, sai da ya ɗauki kusan minti biyu yana danna horn kafin mai gadi yazo ya buɗe masa.

Ransa ya yi matuƙar ɓaci domin idan da abinda ya tsana shi ne ya zo yana horn a jinkirta wajen buɗewa, ba don a kwai abinda ke gabansa ba, da sai ya ci zarafin tsohon mutumin nan.

Shi kansa mai gadin hamdala ya yi cikin ransa ganin Abdallah ya wuce bai ce masa komai ba.

"Mama! Mama".
Shine sunan da ya ke kira a lokacin da ya shigo parlo.

Jin bata amsa ba kai tsaye ya wuce zuwa ɗakin ta, bai shiga kai tsaye ba ya tsaya daga bakin ƙofar yana knocking, yana tsaye har sai da mahaifiyar ta shi ta ba shi izinin shigowa sannan ya shiga, domin kare hakkin addininsa, domin yana da kyau kafin ka shiga ɗakin mahaifiyar ka, ko da ba ita ba ka fara neman izini tukunna saboda baka san a irin yanayin da zaka sami mutum ba.

Wuri ya nema ya zauna a kan kujera mai zaman mutum biyu.
"Mama sannu da gida".
"yauwa sannu Abdallah, ka dawo?".

Abin da ta ce da shi kenan ba tare da ta dube shi ba, kuma tana mai ci gaba da zuba kayan dake hannunta cikin akwatu.

"Mama mai ke faruwa ne na ga yanayin ki kamar da damuwa, kuma naga kina haɗa kaya?".

"ehhh zaka tafi ne, Soja ya na kan hanyarsa ta dawowa".

"kumawa dai Mama! Wai shin har sai yaushe wannan wasan ƴan ɓuya tsakani na da Hammah Saddam zai ƙare? Da zarar ya shigo cikin garin nan daga lokacin zama na cikinsa ni kuma ya ƙare sai lokacin da ya bari, gaskiya Mama na gaji".

A kai-kaice ta ɗago ta dube shi kaɗan sannan ta maida idonta ƙasa ta ci gaba da haɗa masa kayansa, tana mai tattare da matsananciyar damuwa, cikin hanzari take komai, tana gamawa ta miƙe tare dace mishi,

AL'AMARI! Completed.Where stories live. Discover now