1

48 3 2
                                    



Bismillahir-Rahmanir-Rahim


Tafiya takeyi cikin sauri kasancewar hadarin da ya hadu a garin. Iska ke tashi ta ko ina, wanda a kowani lokaci ruwa na iya sauka. Ta karyo kwana kenan ruwa ya ballo, gudu ta shigayi don saura kadan ta isa gida. Da sallamarta ta shiga kofar gdan nasu a lokacin har jikinta ya soma jikewa. Kofa ta shiga knocking tareda kakkape hijabin nata. Wata mata ce ta budo kofar, ita ba fara ba kuma ba baka ba dan madaidacin tsayi. Tsaki matar ta saki tanaima wannan yarinyar wani irin kallo wanda daka gani kasan bana mutunci bane.

"Ke  'yar nan sai yanzu kika ga damar dawowa ko? Na aikeki tun tuni sai da kika gama shashancin ki zaki dawo min gda" marairaice fuska yarinyar da ake ma fada tayi, idan da sabo ta saba jin irin maganganun.

"Kiyi hakuri Anty, rashin chanji ne ya tsaidani" ta fada cikin karamar muryarta.

"Rufemun baki, abinda kika iya kenan. Maza ki ficemun daga gaba kije kiyi abinda ya kamata" sidip sidip yarinyar ta bi ta gabar matar tayi wucewarta. Shiganta  ciki kenan sukayi karo da Sa'adatu.

"Ke kuma meye haka? Baki gani ne? Ta fada tareda watsa mata wani harara.

"Kiyi hakuri Anty Sa'a bansan kina zuwa ba"

"Better watch your front next time" tana fadin haka taja tsaki ta wuce tana yar wakarta kasancewar akwai earpiece a kunnen ta. Wani kallo ta bida dashi. "Allah kyauta" abinda ta furta kenan. Karasawa tayi kitchen ta fara shirin daura girkin rana wanda Taliya ce da sauce. Ta daura tukunya kenan taji a kirata.

"Abida yau ma zaayi girkin bani?" Yarinya ce wanda bazata wuce tsayin Abida ba. Ita Abida tana da haske, da tsayi dan madaidaici ba kamar dayar ba wanda tsayinsu zaizo daya amma baka ce.

"Kai Nana Yanzu ma na daura tukunyar kinga ma ruwan bata tafasa ba" bude tukunyar tayi tana nuna mata.

"Toh bara na tayaki daka su kayan miya" katseta Abida tayi. "Idan Anty ta ganki, zansha fada" wani harara Nana ta Kai mata.

"Toh sai me idan ta gani ai duk mu zamuci, share kawai" karba kayan miya tayi ta soma gyarawa.

**

Bayan Abida da Nana sun kammala girkin, aka zubama kowa a nasa plate din. Nana ta tayata suka Kai parlour.

"Ke Nana me kikeyi a kitchen dinnan?" Mahaifiyarsu kenan wanda suke kirada Anty ta tambayeta.

"Ina taya Abida ne naga aikin zai mata yawa shine na tayata"

"Toh ina ruwanki da aikinta?" Cewan Ramlat wanda ke faman danna waya.

"Yaya Ramlat kufa kunsan Amana aka bamu Abida bai kamata ace ana mata irin wannan abin ba wannan ma gidan-" bata gama karasa maganar ta ba taji saukar mari a fuskarta. Ta sauri Abida tayo kanta.

"Daman ni nasan bakida hankali, ki guji shiga maganar da ba taki ba"

"Anty yanzu dan na fadi gaskia shine zaki mareni?" Nana ta fada hawaye na bin kuncinta. Ita ma Abida hawayen ne ya zubo mata, yanzu duk a kanta ne aka mari Nana.

"Kiyi hakuri Anty, hakan bazai sake ba" cewan Abida cikin rawar murya kokari take ta rike kukarta.

"Rufemun baki ke kuma munafukar banza munafukar wofi. Ai nasan ke ke kara zugata ta min raini" kasa magana Abida tayi ta zubama Anty nasu ido.

"Ai daman tun farko na fadama Salisu kada ya dauko ki, amma baiji ba wai bakida kowa toh muma da iyayen namu suka rasu waya kular da mu. Ai kima gode da kularwa da Salisu yake maki, idan da tani ne da tun farko ma baki gidannan. Kice can ki yi rayuwarki" idan akwai abinda Abida ta tsana shine a zageta akan rashin iyaye. Toh shin Ladi batasan mutuwa na kan kowa bane, ko kuwa tsana ya hanata ganewa.

"Ke Anty ma kina bata bakinki a magana, ai ita tasan matsayinta a nan gidan so kada ma tayi tunanin ko nan gdan ubanta ne." Cewan Sa'adatu wanda zai yanzu tayi magana.

Haka dai sukayita jefa mata kalamai munana, wanda bai cika damunta ba don ta saba jinsu safe, rana dare. Dakinta ta koma wanda yake one single room da katifa sai jakar kayanta dake gefe kuda. Wani takaici taji ya ziyarci zuciyarta, haushin mari da akama Nana taji wanda a sanadiyarta ya faru. Sake fita tayi don dauro alwala.

**
Ta bangaren Ladi kuma tana daki ita da da Ramlat

"Anty gaskia idan baki yi yadda zakiyi ba yarinyar nan zata bata Nana. Ki jibi yadda Nana ke kallon idonki tana fadin maganganu" Ramlat ta fada, fuskar nan yaji Mai har ta somayin Ja.

"Hmm... Nima abin ya bani mamaki, ace 'yar da na haifa ta kalli idona wai tana fadamin abinda ya kamata"

"Ai duk miskiniyar nan ce ke sakata don taga Baba na daura mata baya shiyasa"

"Muna zaman zaman mu lafiya Salisu ya dauko mana wata wahala, kuma kinsan abinda ke bani haushi, idan ya dawo Abida yake fara nema. Komai Abida" Ladi ta fada have dajan tsaki.

"Ni kaina abin ya isheni"

Mota ce ke gudu a kan titi cikin high speed, inda kasan ana buga race. Sai da yakai daidai kan layi sannan motar tayi slowing down. Gate din bakace baka ganin wanda ke ciki, watace ta fito daga motar sanye cikin matsatsun kaya, gaba daya sun kama ko ina na jikinta. Kan nan nata an kitsashi da Attachment sai dan karamar mayafi da ta daura a kan.

"Gaskia I had a great night" mutumin ya fada yana riko hannunta. Wani irin murmushi ta saki.

"Ko?"

"Yes, hope zamu sake haduwa ko?"

"Karka damu indai zaka ajiye masu tsoka shikenan"

"Toh an gama"






**
Kuyi manage da short chapter nan and brief introduction. Insha Allah a upcoming chapters zakuyi finding out more.

Rayuwar AbidaWhere stories live. Discover now