3

13 4 0
                                    

Da misalin karfe uku da kwata Abida ta shirya zuwa karban karatu. Akwai dan zaure a kofar gidansu inda abokin kawunta ke koya masu karatu itada kawarta Maimuna. Kwata kwata gidansu Maimuna baifi tafiyan minti biyarba. Yawanci ita ke dan lekota idan ta ji Abida shiru. Ita kanta Abida ta jinjina ma kawarta ta saboda idan da ta nata ne sai suyi sati ko wata basu ga juna ba kasancewar rashin samun lokaci da batayi. Al-Qur'ani ta ciro daga karamar drawer dake kebe a dakinta sannan ta zura hijab tayi hanyar parlor. Nan ta tsinci Anty tareda yaranta guda biyu. Sa'adatu da Ramlat. Inda Sa'adatu ke makale a gefe guda kanta ko dan kwali babu illa Attachment dake zube a kanta. Tana latsa latsan waya kamar yadda ta saba. Ramlat kuma ta kefe ido a tv. Gyara hijabinta tayi sannan ta soma tafia hanyar kofa. "Zani amsar karatu Anty" abinda ta fadi kenan ba tareda ta kalli gefensu ba kuma. Amma ina tasan ba anan zasu barta ba. Sa'a ce ta fara magana. "Sai ayitayi kamar salihai amma kuma ana wani abun chan na daban" Yanayin yadda tayi mamaki cike da habaici. Sabon datayi da maganganun masara dadi da suka saba fada mata baisa tayi wani magana da. Dukda dai maganganun suka shiga ranta amma haka take danne su. Watarana sai labari.

Batace uffan ba tayi hanyar waje. Gigiza kanta tayi jin kalaman da suke fadi. Fitanta bata zarce ko ina ba sai Zauren. Mainuna ta tarar a gaban mallam, da Qur'ani a gabanta. "Ina yini Mallam" dursawa tayi cikin girmama ta gaidashi.

"Lafia lau Abida. An taho" ya amsamata dashi cikin far'ansa. Dan murmushi ta sakin ma Maimuna wanda ke nuna alamun gaisuwarta gareta. "Bismillah mu fara ko" Ko wannensu ya gyara zamansa dole fara karanta Al-Qur'ani mai girma.

Bayan sun kammala karatun nasu, sukama Mallamin godia sannan suka kama hanyarsu ta tafia gida. "Wai Abida ke bakida kirki. Wai ace gidanmu na kusa amma ko dan lekani bakiyi saidai idan munzo amsar karatu ko kuma mun hadu a hanya. Haba Abida" Murmushi kawai Abida ta saki don ita kadai tasan dalilin haka. Kawance su ya kulle da Maimuna tun zuwanta unguwan. Bawai bata yarda da kawar nata bane kawai bata ganin zata iya fada mata damuwarta. "Kedai bari. Mamaki zan baki watarana. Yini zanyi a gidanku idan nazo"

Harara Maimuna ta kai mata. "Kamar da gaske" kai ta girgiza. "Kwarai kuwa da gaske ne"

"Toh Allah yasa hakan. Kuma ya nunamin ranar dai da zaki bani mamaki" Dai dai nan suka zo kofar gidansu Abida. "Ameen. Bari na je. Sai anjima"

"Ko dai ince gobe ba" Maimuna ta amsa mata dashi. Koda ta shiga gida, yadda ta barsu Sa'a da Anty haka ta gansu. Sai dai yanzu tarkace abun ciye ciye a gabansu. Abida tasha share ledojin su. A saninta dai Sa'adatu bata aiki. Ramlat ma. Kuma da kaga abin ciye ciye kasan ba karamar kudi ake siyardasu ba. Toh amma abinda ke daure mata kai shine kullum da yamma sai Sa'adatu ta fita wanda batasan ina take zuwa ba. Ba aikin nurse ba balle ace shifting. Mahaifiyarsu kuma bata cewan komi abinda ke kara bama Abida mamaki kenan.

Kawarda kanta tayi daga tunanin, tayi ficewarta don tasan idan tayi yinkurin magana toh ba magana mai kyau zai biyo baya ba. Shiganta daki, ta ajiye abin karatunta sannan ta fara shiryan shiryan daura musu girkin dare. Abincin nasu da bai wuce shinkafa ba ko taliya. Mijin Anty na bata kudin cefane na wata amma baifi ta kashe kadanba ta saka sauran a adashe. Adashen da babu wani illa da take mata ko 'ya 'yanta.

Already akwai stew basaita yi wata wahalar jejjegen kayan miya ba. Stove ta kunna, ta daura tukunya da ruwa daidai gwargwado. Sa'anan ta koma kan wasu dan aikin kafin ruwan yayi zafi. Hankalinta gaba daya ya tsaya kan shikafar da take gyarawa. Bata ankara ba taji saukan bugu a bayanta. A fisge ta mike dubanta yakai kan Anty wanda ta kafeta da ido.

"Shegiya yimun asara kinji" cikin rashin fahimta Abida ta bude bakinta zatayi magana kenan Anty ta yo kanta. Har tayi ready jin bugu sai kuma taji wayam. "Wato saboda bake ke siyan kalazir dinba shiyasa kike min Albazaranci dashi ko." Kai idonta tayi wajen rishon inda tukunyar ke rawa alamar tausa sai wutan dake ci sosai har tukunyar tayi soma baki. Day sauri ta rage gudun wutan. "Kiyi hakuri Anty bawai albazaranci nakeyi ba. Bansan sanda ruwa ta fara tausa ba"

"A daman ina zaki sani. Kinacan kina shashancinki. Aiki kadan da zakiyi sai kin bata ma mutane rai" Abida ji tayi kamar tace ma toh kisa 'ya 'yanki suyi amma sai tayi shiru. Ganin masifar da matar ke balbalawa inta fadi haka kara adasa shi zatayi.

"Amma Anty kinsan ai ina kokari, duk aikin da kika sani inayi bana bijire miki. Don ruwan zafi na tausa ai ba abinda zaki tada hankalinki a kaiba" Maida dubanta tayi ga matar. Inda kallo zai kashe mutum toh da tuni ta mutu da irin kallon da Anty ke watsa mata. Batasan ta yaya abin ya faru ba, jin kanta tayi kamar an tsaga a buga mata electric. Hannayenta biyu ta rike kanta dashi wanda nan take jiri ya kwasheta. Cikin yan second bata sake sanin inda kanta yake ba.

Gajiyanyan Iska ya furzar hade ta mike kafafunsa kan center table dinda ke gabansa. Idonsa manne kan screen din laptop dinda ke gabansa yana wasu yan dube dube. Daga gefensa wayoyinsa ne jere. IPhone da Android wanda kullum suna taredashi in case of emergency. Aiko kamar jira suke a tabosu. Android dince ta dau kara. Baiyi wata wata ba yayi picking call din don yasan kiran daga wajen aiki ne tunda shi yake using specific na office Kuma ganin time din kusan magrib yasan call din is important. Saitashi yayi a kunne sa. "Haidar Naseer speaking" Abinda ya soma furtawa kenan cikin gajiyanyan muryan. Hankalinsa ne ya maida kan wayar ji maganar da aka fadi ta dayan bangaren.

"Doctor Hameed baya nan ne?"

"Okay will be on my way. Attend to the patient before I arrive" bai jira amsarda zaa bashi ba ya katse wayar. Laptop dinsa ya wayarsa ya kwashe yayi hanyar part dinsa wanda tafiya kadan zakayi dana mom dinsu. Kafin ya fita ya jiyo muryan Mom din nasa. "Sai ina kuma wannan sauri Haidar?"

Takalmansa ya saka hade da bata amsa. "Wallahi Mom patient ne aka kawo kuma doctor dake on standby bayanan. Insha Allah zan dawo kafin isha'I"

"Toh Allah ya dawo dakai lafiya kuma ya ba patient din lafiaya"

"Ameen" ya amsa mata sannan ya fice. Mom ce ta bi bayansa da kallo. Dan nata na kokari sosai. Addu'ar ta Allah ya kara kare mata shi daga dukkan sharri. Guntu hawayen da ya soma fita daga idonta ta share. Batason tunoda abin baya amma akai akai sai abin ya zo mata rai. Batason ko kadan ta shiga rayuwan da sukayi a baya musamman dan nata.


You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 27, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Rayuwar AbidaWhere stories live. Discover now