Da misalin karfe biyar na asuba, Abida ta tashi. Bayi ta nufa don dauro alwala. Daman bayin a ciki yake, saboda haka ba saita fita tsakar gida ba. Hannu ta saka a handle din kofar taji a kulle. Sake murdawa tayi still. Tunani ne yazo mata shin ko an kulle bayin ne. Bude kofar da akayi ne ya yanke tunaninta. Aunty taga ta fito bayin fuskarta a jike. Da mamaki ta kalleta. Tun zuwanta gdan bazata iya cewa ga ranar da taga Aunty ko daya daga cikin 'ya 'yanta sunyi sallah complete ba. Asalima duk abin addini basu damu dashi ba. Illa neman duniya. Kuma itama mahaifiyar tana goya musu baya sai abinda sukayi. Tunda kuma mahaifin nasu matafiyi ne bai San halayen dasuke ciki ba. Illa idan ya dawo kowannen su ya dawo kamar salihai. Nana ne ma kedan kokari tanayi chan ma ba kullum ba.
"Ke kuma me kikeyi a tsaye kin wani kafe mutane da ido" Ladi ta fada, wanda ya katse Abida daga duniyar tunaninta ta. Girgiza kanta tayi alamar ba komi.
"Ina kwana Aunty" ta fada a hankali. Wani kallo Aunty ta watsa mata.
"Sai da kika gama kare min kallo zaki gaidani. Kuma da ban kwana ba zaki ganni" sada kanta tayi kasa. Don inda sabo ta saba. Babu yadda zatayi. Komin wulakanci suna bata ci da sha.
"Kiyi hakuri ba haka nake nufi ba" ta amsa mata.
"Koma dai me kike nufi. Kiyi ki gama ki fara min aikin gida" kafin tace wani abu, Ladi ta raba ta gefenta tayi wucewarta. Shigewa Abida tayi ta yi abinda ya kawota.
Bayan ta idar da sallar, ta dauki Azkar ta karanta kafin ta soma aikin ta na gyare gyare da sauran su. Duka duka baifi awa daya da rabi ba ta kammala duk wani aikinta wanda ya kunshi gyara, shara, wanke wanke da goge goge. Sai kuma abincin kari da take hada musu wanda duk aikinta su Ramlat, Sa'adatu da Nana suna baccin su. Kuma idan tayi yinkurin tashinsu ranar zata raina kanta don ko Ashar zasu dinga kaimata shiyasa take barinsu insun tashi saita gyara harda na mahaifiyar tasu.
Lipton ta jefa a cikin ruwan zafin da ya kusa tausa dai dai nan taji an kira sunanta wanda bana kowa ba illa na Nana. Ita ce wanda tasan zata shigo kitchen din.
"Abida ya baki jirani nazo na tayaki ba. Kinsan nace you will be my teacher ko." Ta fadi cikin shagwaba. Hannu Abida ta kalmashe ta juyo don bata amsa.
"Nagani cewan idan na tsaya jiranki za’a Kai goma ba’a karya ba. Kuma sannin kanki ne idan Aunty ta ganki babu ruwana" sama Nana ta kalla alamar tunanin kamin ta saki wani murmushi.
"Karki damu zan dinga tayaki a boye nasan Aunty bazata sani ba kuma su sister Sa'a da sister ramlat basu nan balle su ganmu."
"Hanya kuwa Nana. Nifa babu ruwana. Kuma ai munyi magana ne akan weekends tunda kina zuwa school"
A iya saninta, Sa'adatu wacce take babbarsu ta kammala diploma daga Nuhu bamalli polytechnic, ita kuma Ramlat tana final year dinta a kaduna state university, sai Nana da take ss2. Ita kuma Abida ta kammala secondary, university ne ya rage ta shiga kuma Uncle Salisu kamar yadda take kiransa ya mata alkawarin nema mata university amma kasancewar an rufe jamb sai wata shekara zata dauka tareda Nana.
"Kedai Abida kinada fargaba babu abinda zai faru. Nasan abinda aunty takeyi baya maki dadi kawai kinayin shiru ne" Abida dai batace mata komi ba illa juyawa da tayi don sauke ruwan zafi dake tausa.
**
Abuja, Nigeria
Babban gida ce wacce ta amsa sunarta "babba" horn kakeji na tashi daga motar dake gaban gidan. Cikin minti kadan, aka bude makeken gate din. Motar ce ta shiga ciki.
"Kai kullum sai na dinga horn sosai shine zaka bude gate din. Bayan ka gama shanya mutum" cewan wanda ke cikin motan.
"Ayi hakuri baba karami" cewan dan matshin tareda dan duka Kai. Wanda aka kirada baba karami bai kuma cewa komi ba, illa karasawa daya ciki ya paka motar. Matashi ne dogo. Yanada haske amma ba sosai ba. Sajensa ya kwanta baki luf a fuskarsa. Hannunsa daya kunshe cikin aljihunsa, dayar kuma dauke da yar jaka. Cikin takun kasaita ya karasa daga ciki. Parlour ce babba wacca ta sha ado da kwalliya. Komai a cikinta milk and light brown. Kujerun ma royal couch light brown daka ganta kasan yaci kudinsa. Karasawa yayi wajen wata mata zaune a two sitter. Fara ce , kamanninta sak irin na matashin. Daka ganta kasan tana cikin hutu.
"I'm back mom" abinda ya fara fitowa daga bakinsa kenan. Murya karama kamar na yara. Ijeye newspaper dake hannunta tayi ta maita attention dinta kan dan matashin.
"Welcome back my son how was your trip?" Ta fadi. Muryar nata Ya fi nashi ma fitowa.
"Alhamdulila Mom. I missed you so much" ya fadi hade da side hugging dinta. Wani nurmushi ta saki wanda ya kara mata kyau.
"I missed you too son. Your dad too" Zai bude baki yayi magana ta katseshi.
"Go and freshen up first and then eat your dinner" cikin ladabi ya amsa mata. Pecking dinta yayi a chin sannan ya tashi yayi hanyar stairs.
***
Assalamu Alaikum,
Dafatan kuna lafia. First of all, I would like to apologize for not updating for so long. Password dinane na manta kuma danayi resetting sai email dinda nayi linking to it shima ya sami matsala.
Ya chapter? A shafi na gaba ne zaku ji cikakken tarihin Abida. Sannan kuma kusan waye matashin da aka kirada baba karami.
Ku biyoni don ji yadda zata kaya.

YOU ARE READING
Rayuwar Abida
RomansaAbida yarinya yar shekara 18 ta tsinci kanta a matsanancin wahalar rayuwa. Rashin Mahaifiya ya sakata cikin wani yanayin rayuwa na daban. Kishiyar mahaifiyarta da 'Yan uwanta basu raga mata ba wajen ganin su kawar da ita daga Rayuwar su. Me Zai faru...