CHAPTER ONE

10 2 0
                                    

Kina ina? dan ubanki kinji ina kiran ki amman kikayi banza dani,  da yake ba uwarki bace kae kiranki ko. Umma dan Allah kiyi hakuri banji ki bane,  toh idan banyi bah fah ehh nace idan banyi bah fah?  wuche kije ki gyaran daki, kuma idan kingama kishiga nan chikin toilet da kayan wanki ki kaima mai wanki kinji ne koko. Nagi umma insha Allah zanyi kar kima ji wuche mun daga gani, da gudu nashiga chikin daki sai kuka nake wanda ba mai rarashina nayi kuka har na koshi,  idona duk sun kumbara hakanan natashi nayo alwallah nazo nayi sallah Azahar nayi ta kuka ina gaya wa Allah damuwa ta saboda shi kadaine zai iya gyran lamurana da kuncin da nake chiki.
Ina idar da sallah natashi na shiga dakin umma nayi shara,  nayi mopping, na changa bedsheet.  sai na tirara dakin da tiraren wuta na sa freshener ina gamawa na shiga bandaki na kwashe Kayan wankin umma na kaiya mallam musa mai wanki ina shigowa chikin gida na same umma ta fito daga kitchen na tsuguna har kasa ina chewa umma na gama,  ko kallon arziki ban samu ba balle a chemun sanun da aiki haka na haura sama ina mai tsanar irin gidan da na same kaina a chiki  kullum adu'a ta bata wuche Allah yanuna mun karshen zaman gidan nan na shiga toilet nayi wanka.  nadawo nayi shirin islamiyya na dauki  jakata ina saukowa daga saman bene har nafito waje ban same umma a parlor ba na koma chikin gida na haura sama har dakin umma na shiga har kasa ina gaida umma nace mata zanje islamiyyy, har na tashi na kai kofar daki kamar a mafarkin ana chemun a dawo lafiya kuma ki kula sai da na Kala hanyar fita na waiga baya nah Banga kowa ba sanan ne na gane umma ce kae magana na waiga da mamaki ina umma wani farinciki naji tun daga tsakiyar kaina har zuwa kafa funa haka nace Allah ya yadda na fita na tada mallam Shehu driver nace mai na shirya yace to Hafsah muje ko na shiga gaban mota yana ta yimun hira haka dai ina ta murmushi har mu ka kai  islamiyya na fito ina mai jin wani irin dadin da ban san dalili bah ina shiga aji na tada maryam tana gani na ta taso da gudu muka rungume juna tana chemun yau mallam Haris zai shigo nan da nan mun ka kwashe da dariya  haka har yan aji suka shigo muna ta hira kamar bani bah.
Muna chikin hirar "Age is just a number"na chikin Zee word series haka har mallam Haris ya shigo mallami FIQHU dukkan mu muna son mallammi saboda yana koya mana ba kadan ba yadda zamu gane mun dai san fiqh baban Abu ne a Addini shiyasa yakama mata mu tashi mu nemi illmi saboda shine jigon rayuwar mu muna chikin karatun har karfe biyar daidai wani mallami ya shigo  aji angama karatu Karfe shida muka tashii muna ta hira da maryam har zuwan mallam driver nayimusu sai gobe muka wuche gida...

"Asalamu alaikum "wattys hope we are all fine these my first novel on wattpad, vote and comment pls and also share to your loved ones. And follow me in "KADDAR RAYUWA"to know how Hafsat faced her own destiny of life. Lubb yhuu loads..
Yours Nanerh Ayshatu

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now