Not edited!!!
Haka rayuwar Hafsah a gidan Alhaji takasance Hafsah abun tausayi,watarana tana dawo wa daga makaranta umma da aminiyarta suna babban falo suna hira shigar ta keda wuya taji aminiyar umma "wai Dan Allah aminiya ta ina muka kwana da zancen yar tsintuwar nan ne" hmm kedai bari kawai na rasa dalilin da yasa Alhaji ya dauka son duniyar nan akan yarinyar nefa banki ace yau ta mutu ba fa in huta kwananki har tunani yadda zan bata da ita nakeyi.Wata mahaukaciyar dariyar aminiyar umma tasa "kinji zancen manya toh wallahi dani babban fahad yayima wulakanin nan da tuni na shafe labarinta a duniya kae yanxu ya ka Kare da yaran ka balle yaran wasu"
Nifa kae kika yadda dan duk laifin ki nake gani,baban Faruk ba zama yake ba kinga kinsamu damar samata tsnar gidan nan ne gabaki daya,kinga idan kikayi haka watarana da kanta zata bar gidan nan ai wallahi karyar kallan dangi a gidan na balle har wata da ba dangin uba balle na uwa gara ki San nayi dan watarana kar kiyi dana sani toh kinji xance dai.
Hafsah da kanta ya kulle , maganar umma da aminiyarta keta mata yawo a ka tana mammakin irin sakacin iyayen ta duk da bata San laifin da ta aikata har iyayen nata suka sadaukar da ita alhalin basu San irin rayuwar da zata Shiga ba.
A haka dai tayi sallama kinga bakar munafukar nan kallan dangin mayu sai kayi magana ta zaro ma idon nan kaman na mayu chewar umma,hmm gara dai kifara tunanin abun yi kafun ayi Dana sani,dallah ki wuche mana daga gani shashasha kawai
Simsim Hafsah ta wuche tana kuka mai taba zuciya.
"Chigaban labari"
Muna nan zaune da Yayah har aunty Hauwa tadawo,a manya kuce kuna nan kuna hira Hafsah tashi Ki taimaka ma layla a kitchen dan Allah ya Zahra bata nan aikin zai mata yawa,tohm aunty mummy Ammar da Amal da girman kujerarki matar dadyn Ammar da Amal duk muka sa dariya.Ina Shiga kitchen na iske layla na tafsa doya ahh manya kice kin kusa gamawa hmm kedai bari Hafsa da saura, toh bari in taimaka miki nan na bude fridge na fito da kayan miya nayi blending na zo na hada egg sauce na hada mango juice da cucumber monk na zuba a flask dai dai layla tagama hada abincin a cular peach color mai touch of white nan da nan muka shirya abincin a dining ina komawa parlor su anty na nan ita da Faruk, hmm ana shan hira a nan kenan ne aka tura ne kitchen food is ready o.muka sa dariya toh muje Allah yasa abincin yayi dadi haba Yayah Faruk nasan sai kayi santi muje toh .
Yau kam ina chikin jndd Wanda ne kaina nasan da ina gida wajan umma da ko kwatan kwancin jnddn nan banyi bah Muna dining muna ci muna hira har muka gama cin abinci cikin walwala da farin ciki muka gama na kwashe kayan na mayar kitchen na koma daki na .
Anty Hauwa ce tashigo da jaka a hanun ta da wata babbar bakar leda ta zauna side din gado na yan mata har kin zaba daki kenan? Toh aunty ai baki nuna min daki na bah shiyasa na zaba da kaina ,ai dakin ki ne kika zaba Daman nan zaki zauna gashi ko,Daman ne da Faruk munyi magana tun last two weeks akan zaki zo nan Hutu dan ki samu ki huta so nayi miki dinki sai kuma kayan kwaliya gashi nan anjimah ki shirya zamuje shopping da yamma sai ki zaba kayan da baki da su ko bazaki ba? Aa na isa zanje ki shirya toh anty sai na fito.
Tana fita na chire kayan jiki na na bude drawer na dauko wani sabon towel milk color da wani karami shima milk na shiga bathroom komai a tsare yake sai shining yake yi nafi minti goma shabiyar ina wanke jiki na da ruwan tirare masu kamshi gaske ina gamawa nayi alwalar dayke la'asar tayi na fito na bude drawer na dauko zani salla na da hijabi nayi sallah da azkar ina da na saba bayan sallah nayi tilawar Qur'ani na koma gaban dressing mirror na janyo stool na zauna na shafa lotion da tiraruka na jakar da anty takawo mun da ledar na bude kaya ne atampopi da materials sai jalabiyyas sai kayan kwalliya da takalmi.
Wani gown onion purple mai touch of milk color na dauko nasaka da milk head veil sai takalmi milk shima na dan shafa powder da lip balm sai eye liner,bawani kwalliya nayi bah amman am so Masha Allah na feshe jiki na da tiraruka masu sanyi na sa a jiki na
Ina saukowa daga stairs na hadu da layla hmm su Hafsah yan mata kin ganki kuwa Masha Allah dariyar nayi nagode Layla bari inje wajan ya Faruk ta haura ne kuma na sauko kasa na duba karamin falo banga kowa ba kawai sai na fita a chan compound naga anty da yayah su Ammar kuma na wasa kan keke
Da taku na mai daukar hankali na isa, anty ana hutawa wa kenan? ehh Faruk ne yace min wai zai wuche gida tun yanxu Yayah? Ehh wallahi zanje in taimaka ma umma da zaman gida kinsan ita kadai ce.yakamata kam ka gaishe ta insha Allah zataji Amman kinyi kyau Masha Allah na turo baki na ina rufe fuska ta da tafin hanu na,kinga bakinta kaman nawa ahh nawa yafi kyau ai kaima kasani ne bansan komai ba sai dai idan mummyn Ammar will judge anty Hauwa ce tace kanku ake ji.
Har wajan car lot na raka ya Faruk ina mai bye bye, sai da ya wuche na koma chikin gida,dakin Anty nage na buga kofar bugawa biyu nayi amman ba'a ansa ba so ina tunanin tana toilet,daga nan naje dakin Ammar suna wasa nema na Shiga chikin su muna ta wasar hide and seek.
Karfe 6:15pm aunty ta shigo,Anty ina kika shiga? Na yita buga kofar dakin ki baki ansa ba,sorry lil sis ina toilet ne jeki kira mun layla
Daga haka na wuche dakin layla tana nan zaune tana karanta novel kafar ta na buga kae ana ta sallama baki ansa bah kina nan kina karanta shirme.
Hmmm Hafsah wa yagaya miki shirme ne ina koyon zaman duniya ne da na nan gaba hada zaman aure ma gara ki fara karantawa wai Ku yan boko dariya muka sa duka mu.
Daman mumyn su Ammar ce tace in kira ki, wayo nasan abinci ne kuma yanxu nake shirin shiga kitchen nidai na isar da sako na kinga tafiya ta aa ki jira ni muje tare.
Layla, nace yau kar ayi sanwa tunda dadyn su Ammar baya nan anjima zamu fita sai muyi take away Hafsa aje ayi sallah sai ku shirya mu fita ko .
Daga haka duk muka wuche daki,ina Shiga daki na shiga toilet nayi wanka nayi brush na daura alwala na fito nayi sallah ina idar da sallah nayi azkhar ,gaban dressing mirror na koma naja stool na zauna.
Nayi as usual make up dina daga lip balm sai powder gaban drawer na koma ina tunanin mai zan sa,sai chan na tuno da kayan da Anty takawo mun chan na dauko wani skirt and blous red color sai touch of black,na sa da black veil sai wani low pam Slippers duk chikin kayan da Anty ta kawo mun.
Na feshe jiki na da wani body spray mai dadin kamshi nabi jiki na da shi,ina sauka Daga stairs na same su Ammar a parlor sun shirya Ammar ina mumy? Anty taya chichi mu jira ta ko bangama magana ba sai ga Anty tana sanye da wani peach jalabiyya dayake dukan mu farare fata ne sai yayi mata kyau,Anty kinyi kyau kema kinyi kyau Masha Allah duk muka sa dariya.
YOU ARE READING
QADDARAR RAYUWA
Romance"Qaddara" dai wani Abu ne da kae kan kowane bawa. Ku biyo ne domin jin yadda kaddar rayuwa Hafsat zai kasance...