CHAPTER THREE

14 2 0
                                    

Alhaji Hassan Dambam haifaffen dan garin Dambam ne da ke chikin garin Bauchi dake gabacin Nigeria.Babban dan kasuwa ne dake siyen kaya daga kasashen waje.yana zama da iyalen sa ne a garin Abuja nan chikin Asokoro. matar sa daya Hajiya Hajara yaransa hudu Hauwa,Faruk,Mufeedah da Salma.
Faruq shi kadai ne namiji yayi karatunsa a university of Dubai, inda yanxu yake aiki a babban bakin Tarayya dake chikin garin Abuja CBN,  shekarunsa ashirin da takwas.
Hauwa itace babbar yarsu tayi karatu a kasar Cyprus a nan ne ta hadu da wani saurayin ta a lokacin tana year three,shikuma yana masters.da tagama karatu tadawo Nigerian shima yadawo a lokacin ne iyayayen sa dake zama a garin kano suka nema mai auren Hauwa yaran su biyu Amal mai shekara biyar sai Ammar mai shekarau  hudu.
sai mufeeda dake karatu a Oxford university,Salma itace autar tun haihuwar ta Alhaji Hassan yayima kanwar shi alkwarin bata ita duniya da lahira saboda bata haihuwa suna zama ne a garin kano

Watarana Alhaji da iyalensa sunyi tafiya zuwa garin dambam ziyarar yan uwansa,sunyi kwana takwas a garin a ranar litinin sunyi shirin dawowa daga Bauchi
chikin wani daji motar su ta tsaya a dai dai lokacin da Alhaji yafito dan duba lafiyar motar yaji wani irin kuka chikin daji da mamakin sa yace ma  matar sa ta fito tana fitowa da mamaki fal a fuskar ta takecewa Alhaji  kayi sauri mu wuche dan Allah  kagani fa wallahi kila ba mutum bace, Alhaji yace haba Hajara mu tafi mu bar rai idan wani abun ya same dan nan fah tsoro fal a zuciyar sa yaje ya duba chikin kwalin yana budewa da salatin sa yace Hajara mace ce fah.
"Hajiya da tsoro a jikin ta tace Alhaji nefa gaskiya ban yarda da wannan diyar ba kasan mai hakan ke nufi kuwa"Alhaji na zuwa ya bude kwalin ya dauki yar yarinyar nan da ko iyakacin ta shekara daya   da yar jakar ta da kae chikin kwalin, baya n motar ya bude ya ba Hauwa ita nan da nan Hajiya ta hada rai Alhaji wai tafiya zamuyi da ita Hajara barin ta zamuyi? Daga nan bata kara magana bah har ya duba mota suka wuche.
A chikin mota ba mai magana sai chan Hauwa kae che ma daddy yarinyar ta tashi , toh kiyi mata wasa har mu isa gida.
Karfe 6:00 suka isa gida,  suna shiga chikin gida ne kowa yaje dakin shi Hauwa ta wuche da baby dakin ta tana shiga chikin dakin ta yi wanka tayi mah baby wanka tana kan yimata wankan ne ta ga wani bracelet a hanu ta da suna Hafsa a jikin,  a zuciyar ta ta maimaita Hafsa nice name tana gama mata wanka sai bacci. Umma kam ta rasa a kan wani dalilin Alhaji zai dokin yarinyar da bai sani bah, bai san asalin ta ba chan chikin zuciyar ta take duk maganganun nan a haka har baccin barawo ya sachet.
Tun da asuba Hafsa ta tashi tana kukan neman abinci Hauwa na tashi ta wuche kitchen nan ta hada mata maddara ta dawo daki ta bata tana gama sha ta koma bacci.

Bayan breakfast ne Alhaji ya nema zama da kowa a Babban falon, Hauwa na nan rike da Hafsa tana mata wasa Alhaji ne ya fara dacewa na kira ku nan ne ba dan komai ba sai dan maganan wannan karuwa da Allah ya bamu, chan yace ma Hauwa ta kawo mai jakar da aka ganta dashi tashin Hauwa kae da wuya umma kecewa Alhaji  ne fah Alhaji bangane mai kake nufi da tara mu a nan akan wannan yarinyar ne ko mai?  toh ne ban amince bah dan ba'a gidan nan za'kawo mun abunda bai da asali da sunan inyi raino bah dan wallahi sai dai ka neman mata wata uwar ba dai ne bah, baka jin komai sai Hafsa dake hanun faruk tana ta wasan ta. 
Hauwa na dawo wa ta bawa Alhaji jakar yana budewa ko ya fito da wani envelop  mai rubutun twenthy third july it's a day a princess was born happy birthday Hafsah bayan ya gama karantawa ne ya bude envelop din wata yar sarkar gold ne da zube na yara sai birthday notes da kae chiki
Da wani farin baby towel da bottle water da murmushi fal a fuskar sa ya mikowa wa matarsa tana ansa ts duba tace mai zanyi dashi nan take ran Alhaji ya bace yafara yimata nasiha
"Shin Hajara idan yar kice a halin nan zaki ji dadi kuma kema ki duba duk abubuwan da muka samu a chikin jakar baby zaki san chewa yar baban gida che ki duba dan Allah ki gani shin ko da ache ba sintar ta mukayi bah baza ki tausayawa wanan yar jinjirar ki rike ta bah haba mana Hajara ki duba girman Allah ki taimakawa yarinyar nan ki rike ta kamar yar da kika haifa da chikin ki dan Allah Hajara ki duba girman Allah ki taimaka mata"duk da maganar Alhaji ya shiga jikin ta amman tace masa nefa bazan rike yarinyar nan ba na gaya maka daga kai har yaran ka dan haka kayi shirin nemar mata wata uwar rikoyarinyar nan  badai ne bah kayi iko da gidan ka da yaran ka.
Abun yaba Alhaji mamaki amman ba yadda ya iya nan ya aike faruq ya kira masa Inna ladi mai aikin gidan nan da nan ta biyo faruq.
Alhaji ka aika kirana? Ehh toh daman amana ce nake son in baki nan da nan Alhaji ya shiga bawa Inna ladi labarin yadda suka tsince Hafsah ta tausaya mata matuka nan da nan ko tacewa Alhaji Allah ya taya mu riko gabadaya duk suka ansa da ameen.

Karfe 1:30 Alhaji ya shirya da shi da yaransa suka fita a wani baban mall suka tsaya tare da yaransa suka shiga chikin mall din sunyiwa hafsah siyayen kaya ba kadan ba da abincin yara dan bata kai fara chin abinci ba daga nan suka wuche bangaren kayan wasa Alhaji ya siya ma yaransa kaya ba kadan bah daga nan kuma suka wuche park sai karfe shida suka dawo gida.
Hauwa na goye da Hafsah suna shiga chikin gida suka same umma zaune a falo ta hada rai da sallama suka shiga gidan faruk da mufeeda rike da ledoji a hanun su sai daddy da mallam musa dake biye da su da sauran ledojin da murmushi su faruk suka rugume umma suna mata sanu da gida ko kallon inda su Hauwa da Alhaji suke batayi ba.
A haka rayuwa ta chigaba idan su Hauwa na makaranta toh Hafsah na wajan inna ladi idan kuma sun dawo tana wajen su umma kam ko kallo Hafsa bata ishe ta ba ita ma kanta ta rasa mai yasa ta tsane ganin yarinyar da bata san komai bah haka kawai ita dai bata son yarinyar.


Hy wattys hw's the chappy pls vote and comment love u loads...........

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now