These page is dedicated to sister like no other Maryam(maream) luv u lodi lodi
Shida da rabi daidai muka karaso unguwar, dai dai gate muka hadu da yaya faruk "Yayah mun wuni lafiya"lafiya lau yan islamiyya ya karatn yau? Nace lafiya lau Alhamduliah, toh zan zo a koyan Wanda aka koyo, nace mai toh sai ka zo duk magana da munkayi bai dago kai muka hada ido bah . dai dai parking lot mallam dreba yayi parking na fita ina chemai sai da safe.
Adu'ar shiga chikin gida nayi ina mai yin sallama...
na shiga nan na iske umma a karamin falo tare da aunty Hauwa da yaranta sun zo gayda gida, da gudu nage na rugume ta sanu da zuwa auntyna, nayi missing inki, saukan yaushe ina ta dariyar farin chiki. Hafsah kae dai bakya girma haka zamu kaiki gidan mijin, na turo baki na ina chemata aunty kae dai baki da magana sai miji ai ne ba yanxu xanyi aure bah.ta yita dariya tace wuche daki ki changa kaya, anjema mayi hira ko nace tohm auntyna, umma kam ko kallon arziki bata mun ba tun shigowa ta. umma ina wuni ko ansawa batayi bah na wuche dakin nawa, ina shiga na chire kayan islamiyya na na shiga bayi sai da na dau kusan minti talatin ina wanka ina tunani irin duniyar da muke chiki a yau, ina kuma adu'a Allah ya nuna mun iyaye na. Na gama wanka na dauro farin towel iya kneel ina na dauro alwala na fito na shafe jiki na da mayuwaka na masu dadin kamshi da turaruka, na sa nighty wando da riga,ina bude drower da kaya kae chiki na chiro hijabi nazo na tada sallar magriba ina idar wa nayi azkar da na saba kullum bayan kowace sallah na dade ina kaiwa Allah kuka na kafun in nade. sallaya na maida ta wurin zaman ta daidai shigowar aunty hauwa daki tana mai sakar mun murmushi ta zauna nan gefen gado na "aa anty har kin shigo Kenan?" ina dariya tohm ba dole ba kin barni ina jiran ki nan nazauna gefen ta.Hafsah! Na'am ina mai dago kai inda take wai har yanxu kae da umma? bansan sanda na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya ba, bata hana ne bah sai danayi mai isa ta kafun nace anty har yanxu,yanxu abun har yazama ko gaishe da umma nayi sai taga dama take ansa mun gaisuwa ta , na rasa mai na yima umma hakane Hafsa kicigaba da hakuri na san kina yi kuma ki kara kingi watarana sai labari duk da nasan akan abu daya umma keyi miki hakan amman ki kara hakuri dan Allah, toh Aunty insha Allah. toh share hawayen ki muje kasa muci abinci ki zo ki ban labari tana fita na shiga bayi na wanke fuskata ina sauka kasa na ge na zauna inda na saba zama a dining kowa na nan ne kadai ake jira inna ce tazo tayi serving .
Yauwa umma nace tunda su Hafsa sunyi hutun makaranta dan Allah ina son ta koma waje na da xama kafun su koma makarantar,ne dai ido dai na xuba ina mai jin mai umma zata ce "akan mai ? ina che tana zuwa islamiyya toh ban amince ba nan gidan da batason zama nan zata zauna idan gidan ya ishe ta ne to ta koma gidan ubanta ehee."bansan sanda na fara hawaye ba chan nagi muryar yaya faruk nacewa, umma ki barta ta tafi mana ai ko aiki ma sai tayi mata tunda ba lafiya ya ishe mammy Ammar ba haka wajen yayi shiru sai kara spoons ana gamawa na kwashe kwanukan zuwa kitchen in fitowa naji umma na chewa aunty Hauwa shikenan goben sai ku wuche, ina dawo wa na ce sai da safe na wuche daki na ina shiga na sa ma kofa key sai kukan da bansan rana dainawa bah har bacci ya kwashe ne bansani ba .Misalin karfe hudu na tashi na shiga toilet nayi wanka na daura alwala nayi sallah ina nan ina azkar har karfe shida naji ana buga kofan daki nah na ina tashi na bude ashe aunty ce na gaishe ta,ta ansa tace in shirya karfe tara zamu wuche daddy su Ammar zayi tafiya nace toh na koma chikin dakin ina hada kayana a karamin akwati na dan nasan iyakaci sati biyu zanyi hutun makarana ya kare haka na hada duk abunda na sann zan bukata na amfani nah na, na gyra daki na, na feshe dav tirarukan wuta da na daki dani ba baya nake wajen tsafta bah
Ina sauka na tada innna a kitchen na gaishe ta ta amsa da murmushin ta tache Hafsa kichigaba da hakuri duk mai hakuri mawadaci ne,da sakin fuska ta nace inna nagode bara na gaida umma nazo na samiki hanu. ina fita na wuche dakin umma ta na kan sallaya umma an tashi lafiya ina kwana hanu kawai ta daga na tashi na wuche.ina fitowa munkayi karo da ya faruk wani irin bugawa nagi zuciya ta tayi wanda shima nasan hakan ne tafarau a wajanshi ina kwana yaya yace dani lafiya an tashi lafiya nace mishi lafiya lau ya ce tohm ki shirya kayan ki karfe tara zan kaiku chan gidan mammy Ammar na ce to shikenan nagode na shiga daki aunty hauwa tana shirya Amal Ammar kuma na nan na bacci bai tashi bah na anshe ta ina mata wasa ta na ta dariya na aje ta nace ma aunty hauwa zanje kitchen in taimaka inna da girki tace sai mun fito
Ina shiga na tada inna na faman soya kosai n taimaka mata da kunnun gyada na hada fruit salad na taimaka mata muka shirya a dining dai dai da fitowar umma da aunty Hauwa sai na wuche kiran ya faruk muka fito tare ina gaba yana baya na har mu ka iso dining nayi serving muna gamawa ns tatara kwanukan na kai kitchen na wuche daki na ina duba agogon da ke jikin bango na naga karfe takwas da minti ashirin,na wuche toilet nayi wanka na zauna gaban dressing mirrow na taje tsuma ta na shafa lotion da turaruka a ko wani sashe na jikina nayi light makeup na doko wani atampa skirt da riga blue mai touch of pink na sa na yi daurin tura kaga tsiya na sa pink slippers da pink veil na dauko black hand bag da sa dan kunne na na dawo gaban madubi ina mai kara kallon kaina Masha Allah nayi kyau ba lefi ina duba agogo na ga tara saura minti goma naja akwati na ina saukowa daga saman bene na hadu da anty yanxu nake chewa in kira ki ko kin mance da tafiya mu ne? aa anty gani na sauko.Masha Allah kinyi kyau na kalle shi muka hada ido na kauda kaina kasa ina wasa da fingers ina, aunty ce tace faruk, kar ka chinye mana kanwa,anty yabawa kawai nai ko ache an gode ne kam ina ta murmushi anty Hauwa ce tace umma zamu wuche bata kalle mu ba tace Allah ya kiyaye hanya dukka muka ce amin daga haka muka wuche yayah faruk na ma su ammar wasa
Karfe goma da minti shida muka isa gidan Aunty Hauwa dake nan chikin Maitama estate na chikin garin Abuja Masha Allah gidan ba lefi yayi kyau sosai gidan sama ne daki hudu a sama da parlour daya sai uku akasa ko wane da toilet a jikin dakin sai parlour biyu da dining dake mane da kitchen sai pangaren masu aiki da kae gefe gidan da boyz qrts a bayan gida.
Mijin aunty uncle Abdallah yana aiki ne a companin NNPC da kae nan Abuja, sun hadu ne a lokacin da aunty taje school a Cyprus har ta kai ga auren su
Ya faruq na horning biyu mai gadin gidan ya fito yana bude gate yana gaishe shi muka shiga chiki, Ammar da Amal kam ana bude gate suka fara qiran daddyn su, suna shiga chikin gida, ko da muka shiga har yagama shirin shi chikin farin yadi su Ammar kam da gudu su ka rungume shi Daddy we miss you, miss you to sweetie pies yana musu peg , how are you? and daddy is travelling to lagos for an urgent meeting am gonna miss u we miss u to daddy take care of yourself for mummy duk suka sa dariya ne kam yaran sun birge ne sosai ina mai adu'a Allah ya nuna mun rana da zan kasance da nawa iyayen, nan da nan ido na suka sauya na haura sama duk da ban san daki na ba dan tun auren ta da muka rabu sai yau ma nake zuwa gidan nata nan dai na bude wata kofa naga komai a gyare na shiga chiki na fara bude drawer dan in tabatar ba kowa haka ko akayi ba komai chikin drawer na bude na sa akwati na na shiga bandaki na wanke fuska taTun daga kan bene jiki na ya bani ana kallo na amman bansan waye ba dan haka ina dago ido na mukayi ido hudu da shi ya sake mun murmushi mai yasa ki haurawa sama ko sallama baki yima Abdallah ba kika wuche? Daman naje aje akwatina ne, ashe har ya wuche ina anty take? chan naji muryar shi yana tambaya ta wai yaushe zaki bar tunanani nan ne Hafsah? Kina son sama kanki hawa jini ne ko mai? Na san kae mai hakuri ce amman ki kara da wanda kike yi komai lokaci ne wata rana sai labari nan da nan na fara kuka ya faruq mai nayi a duniyan na da iyaye na zasu yadda ne ehh yayah? Kuma kace mun in daina kuka haba yayah ai gara inyi kuka ko zan samu sauki, zuciya ta ciwo take duk sanda na tuna banda gata a duniyar nan sai Allah ya kake son inyi?
Wani murmushin da yafi kuka da nake ciwo nayi yayah kar ka damu amman na san watarana sai labari, bari in kawo ma ruwa kasha, ban jira mai zai ce ba na wuche na tada mai aikin aunty tace mun sanu nema nace mata sanu dan ban santa bah nace mata ruwa zaki bani ta bude fridge ta bani da cup sai da nakai baki kofar fita nace mata suna na Hafsa, tace suna na layla dan naga yarinyar da kadan zata girme ne ina zuwa parlour na tada yayah na waya na aje mai ruwa na koma gefen kujera chan kasa sai da yagama waya yace Hafsa yan matana nan da nan na fara dariya yace mun da mufeeda nake waya tace in gaishe ki daddy ma yace in gaishe ku next week zai dawo,
Yayah da gaske,ehh man wayo har nagi dadi umm masu daddy manya na turo baki na gaba nace jelousy yace mun you are not serious mufeedah to is coming back next week nace Allah ya kaimu lafiya muna ta hira kaman bani na gama kuka bah nace yayah daman magana sauka na ne ahh islamiyya idan ka koms gida ka gayawa umma nan da three weeks an sa date ya kalle ne yace toh mallama Hafsa as you wish na fara dariya.kinga idan daddy yadwo next week sai ki gayamasa ko nema am going to suprise my yan mata duk muka sa dariya.
ESTÁS LEYENDO
QADDARAR RAYUWA
Romance"Qaddara" dai wani Abu ne da kae kan kowane bawa. Ku biyo ne domin jin yadda kaddar rayuwa Hafsat zai kasance...