Episode 16

31 1 0
                                    

*°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°* 
                 *1441H/2020M.*
             
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*



*SHAFI NA 16📑* 

*__________📖*  Ganin bazan dawo ba ya saka shi wucewa cikin na shi gidan, amma ko kaɗan baijin kwanciyar hankali a tare da shi.

Wanka nayi na fito parlor inda Amal ke zaune, ta kunna laptop ɗinta rana ta aiki a ciki, take-away ɗin na ɗauko mana, zama mukayi a ƙasa ba tare da mun hau dinning ba muka fara ci, muna gamawa Amal ta dube ni tana murmushi tace, "Hummyn Dr Hussain", ta faɗa tana duba na da murmushi.

Hararanta nayi nima nace, "Amal ɗin Dr Hussain".

"wai laifin meye bawan Allahn nan yayi miki ne Hummy? gaba ɗaya kin jan mishi gaba ɗaya, gashi ga dukkan alamu hankalin shi ya tashi, don Allah ki gyara, don ni nafi son drammer ko na baya", ta faɗa tana mikewa zuwa ɗaki.

Harara na ke binta da shi, "ke ba sai ku cigaba da drammer ba, ae kema ɗalibar shi ce"

" ni ae ban iya yadda kike yi ba, kuma ke da shi kun fi bada colour, ni idan nayi ma bazai burge mutane ba", ta faɗa tana dariya, sannan ta wuce cikin bedroom ɗin mu.

ya mutsa fuska na nayi ina kwanciya a saman kujeran, a fili ina faɗin. "wato ya cigaba da wahalar da ni ko? Toh naƙi wayon, gara na share shi shima yaji yadda na ke ji".


5:00pm muka fito gefen da muke zama dasu peter don yin karatu, zama mukayi muna ɗan duba abinda akayi lokacin da Amal ke hospital, ina ɗan mata bayanin abun da akayi bata nan.


Bamu fi 30mnts ba saiga Dr yazo inda muke karatun, ɗago kaina nayi na dube shi, kallon dana mishi sai da gaba na ya faɗi, a zuciyata nace, "wani irin kyau ne Dr yake da shi kam?"  Three quater ne a jikin shi sai wata riga armless,idon shi ɗauke da glass ɗinshi na koda yaushe, sai wani sauƙe ƙamshin mai daɗin gaske ya keyi, hannun shi ɗauke da juice a cup yana ɗan sha yana duban fuskana, wanda ni kuma kaman naga mala'ikan ɗaukan rai, na wani haɗa fuska na gam.


Murmushi yayi ya nemawa kanshi wurin zama a kusa dani, ɗagowa nayi ina kallon shi, amma da sauri na sauƙe idona ƙasa ina zunɓura baki, domin muna haɗa ido ya wani ɗaga mun giran shi, sannan ya jawo books ɗin da ke baje a gaban mu, ya daɗe yana duba su, sannan ya dubi Amal yace, "wai me yake damun ƙawar kine kam, ko na mata wani laifi ne"?


Dariyan da Amal ta ke ƙunshewa ne ya ɗan suɓuce mata, amma sai ta wayance da, "Hmmm Dr laifin me zaka mata? Ita har ta isa ma kama ta laifi? Nima tun jiya na ke fama da ita, amma ina tunanin saurayinta ne ya ke mata yajin aiki, don naga kwana biyu baya ƙiranta, halan shiyasa ta ke son hucewa a kan mu, amma Dr ka hukunta mana ita tun da bata isa ta ja da kai ba",  ta faɗa  tana taka ƙafa na yadda bazai gan mu ba.

Baki na bari buɗe ina jin mamakin irin sharrin da Amal ta ke yanka mun rana tsaka, kowa yace mata ni ina da saurayi oho? Kallon shi nayi amma sai naji hanta cikina suna wani juyawa kaman xanyi gudawa, wani irin fitinannen kallo ya ke watsa mun na har kin isa yiɓ samari?

ƘADDARA TA RIGA FATA.Where stories live. Discover now