Episode 8

42 2 0
                                    

*°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*

*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 8📑*

*__________📖* Muna fita waje ya sa ke hannu na ya na bina da harara, tsayawa na yi baki na a zunɓure ina ta ƙunƙuni ban ko kalli inda yake ba, ba mu daɗe da tsayuwa ba, ya tsayar mana da taxi mu ka wuce gidan mu.

Muna fitowa a taxi ɗin ya bini da harara, ni dai bance komai ba sai murguɗa baki na da na ke ta yi, kuma ban kalle shi ba, amma nasan yana kallo na, kuma yana sane da abinda na keyi.

Har na saka key ina buɗe gida na ya matso inda nake, cikin nuna iko da gadara yace,

"kada na sake ganin kin shiga motan Dr nan, idan ba haka ba kuma zan mugun saɓa miki, idan kin tashi tafiya ki mun magana".
yana gama faɗin hakan ya juya yayi na shi hanyar gidan.

Tsayawa na yi ina bin shi da kallon mamaki, baki na a buɗe saboda mamakin shi, yana ƙarasawa gidan shi ni kuma na ɗaga murya da ƙarfi nace,

"To kai ɗan'uwa na ne da za ka takura mun? Kuma sai na ƙira shi ya kaini asibiti, ai kaima na ga matar ka kake ɗauka a motan ka, ko na hanaka ne?".

Tsayawa ya yi kaman ba zai juyo ba, amma ganin ya juyo yana kallo na bakin shi ɗauke da murmushi, na yi sauri na shige gida na na rufe ƙofan, don na san murmushin naugunta ne, don banga alaman na tsakani da Allah ba ne.

Ganin na gudu sai ya wuce parlon shi yana ta murmushin shi.

Kowan mu yana shiga yayi hanzarin ɗalewa gado, ranan da ƙyar na tashi nayi sallan asuba, sannan na sake komawa baccin, bani na tashi ba sai after 10, a razane na buɗe ido na ina kallon time, ganin da gaske haka lokacin ya yi ya sakani tashi da sauri na shiga toilet na yi brush na yi wanka, ina fitowa na ɗauki waya na na ƙira number'n Amal.

Yana fara ringing bai daɗe ba aka ɗauka, naji muryan Amal a hankali ta ke mun magana, haƙuri na fara bata ina gaya mata wani irin bacci ne ya tafi dani, don sai yanzu ma na tashi daga bacci, amma tayi haƙuri me zan kawo mata tayi breakfast?

Sautin dariyan ta naji sannan ta ce,
"Ki kwantar da hankalinki sister, komai da ka ke buƙata asibitin suna maka, kuma already ma Dr Hussain tun 7:30am ya kawo mun break, amma yasamu ma har suna bani, so kar ki damu kan ki, kawai kizo na ganki kafin su Abbu na su iso".
ta faɗa tana mun dariya a hankali.

Ina ajiye wayan na wuce kitchen na haɗa tea cikin sauri-sauri, ina gama sha na fito nayi ɗaki na, shima da sauri na shirya na fito domin tafiya duba Amal, ina fitowa na harari gidan Dr Hussain sannan na murguɗa baki na, dai-dai lokacin Peter ya fito daga nashi gidan, sauƙa nayi na ƙarasa inda yake muka gaisa, yana duba na da tausayi yace,

"jiya a can ki ka kwana Preety?".

Dariya na ɗanyi kaɗan na ce,
"gida muka dawo ni da Dr Hussain saboda hospital ɗin basu bari a kwana da patient".

sai naga ya yi sauri ya duba gidan Dr Hussain sannan ya juyo in da na ke yana murmushi yace,

"Dr yana kishi akan ki Preety, halan yana so ya ɗauke sister shi ba zai bari ma kowa ba".

ƘADDARA TA RIGA FATA.Where stories live. Discover now