*°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.**SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*_*SADAUKARWAR PAGE ƊIN NA KUNE, HAFSAT ISAH PZ & HAUWA MUSTAPHA JAJERE A (Gaskiya Fans H) KUYI YANDA KU KE SO DA SHI, INA JIN DAƊIN YANDA KU KE SON WANNAN NOVEL ƊIN, SABODA HAKA MA BESTY NAH (Miss Xerks) TA CE NA GAISHE KU BOHOT-BOT... Kuji daɗin karatu lafiya.*_
*SHAFI NA 12📑*
*__________📖* Daga Abbu har Ummi sun ji daɗin karrama su da na yi musu, bayan munga ma dinner ta re da su, Abbu ya maida hankalin shi kan kallon News da ake yi na ƙasan, ni da Ummi kuma kaman wanda mu ka shekara muna tare, sai hira muke yi na rayuwar Amal da irin wahalar da ta ke sha.
"Ummi to me zai hana Amal ta dawo wuri na mu zauna tare? Saboda yanayin ciwon ta ina ga bai dace ta zauna ita ɗaya ba, saboda wataran ina ga baza ta iya samun sararin yiwa Dr waya ba, ko me ki ke gani Ummi?".
Na faɗa ina matsawa jikin ta, tsabar samun wuri irin nawa, dama asali ni mai son naga ana nuna mun kulawa ne, domin duk ranan da kaka ta tazo gidan mu ko naje wurin ta, sai Daddy yayi ta mana shari'a, zata yi ta mitan ina tumurmusan ta, amma ina primary 6 Allah ya yi mata rasuwa, Allah ya jiƙan ta da rahma.
Abbu ne ya juyo ya ƙurawa Ummi ido don jin mai za ta ce, amma sai Ummi naga ta sunkuyar da kanta ƙasa kaman mai tunani, har tsawon wani lokaci sai ta ɗago tace,
"Humaira ba wai naƙi shawaran ki bane, iyayen ki ina ga ba lallai ne su yadda ba, and secondly kuma ciwon Amal ba ita kaɗai ba, duk wanda ya raɓe ta ma sai ya sha wahalar jinya, keda aka kawo ki karatu, ai bai kamata mubar ki da jinyan Amal ba".
Ummi ta faɗa tana share guntun hawayen da ya biyo idon ta."Ummi Daddy na ba shi da matsala bazai hana ba, shima kullum sai yace tausayi na ya keyi na zama na ni kaɗai, kawai babu yadda ya iya ne, ciwon Amal kuma kawai nawa idan ya tashi ne na ƙira Dr ya tafi da ita asibiti, tun da asibitin su ba zama akeyi a wurin ba, ba kai musu abinci akeyi ba, komai acan ake musu, kinga ai babu wani matsala, bana son ta zauna ita ɗaya ne".
Abbu ya yi gyaran murya yace, "Humaira bani number shi mahaifin kin, nima nayi tunani irin naki tun da muka shigo gidan nan, idan Allah yasa ya amince ni zan fi samun kwanciyar hankali ma".
ya faɗa yana miƙo mun wayar shi.Da sauri na amshi wayar tsabar murna jiki na har rawa ya ke tayi, number Daddy na juye mishi, na miƙo mishi ina ta murmushi.
Bai daɗe wayan yana ringing ba naji muryan Daddy yana sallama, alamar ya ɗauki wayan, Abbu ne ya fara gaishe shi, sannan ya mishi bayanin shi ne mahaifin Amal ƙawar Humairah, Allah sarki Daddy daga muryan shi za kaji yaji daɗin ƙiran da Abbu ya mishi, tambayar jikin Amal ɗin yayi, Abbu cikin farin ciki da jin daɗin an nuna kula akan ƴar ta shi ya amsa da sauƙi, sannan Abbu ya gayawa Daddy manufar ƙiran shi da ya yi.
Daddy ma ya nuna jin daɗin shi in da ya ke cewa Abbu ai daman kulum zama na ni kaɗai tausayi na ya ke ji, don ma ya bada amana na wurin Dr Hussain ne ya samu ɗan sauƙin tunanin abun, amma ai bakamar yadda zasu zauna su biyu ba, don kuwa zata daina jin kaɗaici, kuma za suyi karatu tare.
YOU ARE READING
ƘADDARA TA RIGA FATA.
Acciónlabari ne mai tattare da faɗakarwa da kuma ɗumbin darussa, soyayya dama nishaɗi.