Kamar yanda aka saba, kudin da muka samu bayan ansiyarda littafin suna zuwa kai tsayene ga ga gidauniyar dake tallafawa abokananmu mata wanda mazajensu suka rasu, da "ya"yayensu, dakuma wanda aurensu ya mutu, kuma basuda halin dawainiya da kansu.
Godiya ta musamman ga yar'uwa kuma abokiya, Zainab Adamu, dakuma Fatima Rabi'u wanda suka bada gudunmawa marar adadi.
ABUBUWAN DAKE CIKI:
i. GABATARWA:
- JINJINA
- Tunatarwa akan muhimmancin mata
- Gudunmawar mata ga cigaban al'umma, ilimi, da sauransu
- Matsayin mata a addinance
- Halinda Mata suke ciki a yanzu
- Abunda bazai taba yafuwabaii. KASHI NA DAYA. Matsalolin da mata ke fuskanta kafin Aure:
- Matsalar ilimi
- Matsalar Tarbiyya
- Matsalar Talauci
- Matsalar son abin Duniya
- Matsalar karancin mazajen aure
- Matakan magance matsaloli atakaice.iii. KASHI NA BIYU_ Matsalolin da mata ke fuskanta bayan sunyi Aure:
- Matsalar Muhalli
- Matsalar Ci da sha
- Matsalar Dangin miji
- Matsalar Cikin Gida
- Matsalar Kwanciya
- Matakan Magance Matsalolin atakaice.Marubuciya: Muhibbat Adam. 07040915535 | Text or WhatsApp only.
- JINJINA: Wannan jinjina ce ga iyayenmu, kakanninmu, yan'uwana mata dama duk wata mace datayi rayuwa ta shude abisa wannan doran kasa. Wannan jinjinace wa duk wata mace datake fadin duniyarnan. Kodaga ina kike kuma kowane irin matsayi kike akai, mata sune suka bada mafi tsokar adadi na rayuwarsu, domin cigaban wannan al'umma. Sune wanda suke aiki tukuru, badare ba rana. Duk zafi duk sanyi, basu hutawa saisun tabbatada munkaiga nasara. Wasunsu sunacin gajiyar dawainiyar dasukayi damu, wasunsu kuma ko kadan. Sune iwaye sune "yaya, aune mata kuma sune innoni. Sabida haka nake kira gareku damufara mika jinjinarmu izuwa wannan kinshikai masu daraja. Ina rokon Allah daya albarkaci rayuwar dukkan wata mace da abinda tasaka agaba. Allah ya jikan iyayenmu, kuma yabamu ikon kyautata masu.
- TUNATARWA AKAN MUHIMMANCIN MATA: Mata sune abokan rayuwar kowane namiji, Allah ya albarkacesu da ni'ima mai tarin yawa. Mata gundarin kinshikine ga mafi yawan mazaje. Kuma su rahamane ga kowace al'umma.
- GUDUNMAWAR MATA GA AL'UMMA: Tun tali talin tarihi, gudunmawar mata ta kasance abinda ke tafiyarda cigaban kowace al'umma. Iyayenmu mata sun kasance madogara wajen tarbiyyantar damu tareda "ya"yayenmu, haka zalika wajen bayarda kulawa ga lafiyarmu, cinmu da shanmu.
Mata suna taka rawa matuka wajen kulada yara da tsofi aduk fadin duniya. Bincike yanuna cewa, idan tattalin arzukin kasa ya razana, matane suke habbasa wajen ganin anci gabada kulawa da gida yanda yakamata, batareda wani daga waje ya fahimci bambanciba. Matan karkara sun kasance sahun gaba wajen taimakawa da abinda za'a tafiyarda gida. Tundaga hidimar yauda kullun, har izuwa hidimomin bazata.
- GUDUNMAWAR MATA FANNIN ILIMI DA ILMANTARWA: Gunmawar da mata ke badawa bangaren ilimi tundaga karamin mataki har izuwa babba bazaya ta6a misaltuwaba. Ilimin yau da kullum yana daga cikin ginshikan tafjyarda kowace kasa, haka zalika ci gabanta. Bincike yanuna cewa, ilimi yanada karfin canza matsalolin yau da kullum, tundaga matsalar noma har izuwa ta matsayin su kansu matan acikin al'umma. Iyaye mata sune suke tsayawa tsayin daka don ganin yara sunje kuma, sun zauna a makaranta.
- MATSAYIN MATA A ADDINANCE:
- MATSAYIN MATA AHALIN YANZU: A wannan zamani, mata sune marasa gata, sune abin ciwa zarafi, sune marasa galihu, su ake dannewa hakki. An maidasu bayi, an maidasu kashi da tusa. An maidasu abin yaudara, abin ban tausayi. Matsalolinsu ba'a dubawa, kukansu ba'a sauraro, al'amarinsu ba'a dubawa. Kuma kullum cikin nemansu ake, kullum cikin cin gajiyarsu ake, kullum cikin cin albarkacinsu ake. Amman kuma kullum cikin wulakantasu ake, kullum cikin banzatar dasu ake, kullum cikin raina masu hankali ake. Mun manta da ni'imar da Allah yamasu, mun manta da raunin dasuke taredashi, mun mamnta da umarnin Allah akan basu kulawa. Mun manta da hadissan manzon Allah akan janyosu jiki, da kyautata masu, da faranta zukatansu, da tsaya masu akwane hali, da kulada al'amuransu, da taimakonsu sanda suke neman taimako. Da agaza masu domin Allah.
YOU ARE READING
Muhimmanci Mata Da Bukatunsu Na Aure
RomanceMace kinshiki ce, haka zalika mabukaciya ce. Tun daga sutura har makwanci. Na kara maku da shawarwari akan yanda namiji zai bawa matarshi kulawar da take bukata akan gado.