☠️☠️☠️☠️
*DUNIYAR MATSAFA*
☠️☠️☠️☠️*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_we are here to educate motivated entartain our readers_©️
_Zainab Abdullah_
_real shaxee🍒__email_
rzainababdullah@gmail.com_facebook_
_zeenat deen shaxee__wattpad_
_real shaxeee__wannan book d'in nasiyarwane inkina bukata kona bukata zaka iya tuntubar wannan nomber 08085898952 kokuma katuro 300 kacal ta wannan account nomber d'in 0068933035 kokuma katin MTN saikiyi screen shot dinsa kituro ta waccan nomber👆🏻_
_FREE PAGE_
_PAGE 9-10_
_DUNIYAR MATSAFA_
"Tabbas hakane ya waziri, mutun biyune acikinmu zasu iya futa, dalili kuwa shine kunsan cewa babu wanda yake da ikon barin duniyar nan har sai ya mallaki zoben sihiri, kuma gidan sarautane kadai suke dashi sai matsafa da masu kudin cikinta, tunsanda zu'kairu ya kamaku yaje masarauta ya 'kwace dukkan zobunan na kowa da kowa, cikin ikon Allah nasamu na tsira da nawa da kuma na ummata wanda yake hannunta tun sanda ta mutu, kuma dan baku kula bane amma tun sanda ya kamaku yacire muku zobunan, shiyasa yanzu hankalinsa baiyi wani mugun tashiba saboda yasan cewa bazaku iya ta'ba barin duniyar ba". Dukansu suka duba hannunsu ilai kuwa babu ancireshi.Sarki Aziz ne ya kallesu yace, "Mafutarmu fa d'ayace fa kuma dole ita zamu bi, ni zan taresu daga nan kukuma kuje, sannan kuma Jalal ka rakasu har izuwa 'kofar da zasubar duniyar kaikuma Hamit saika saka zoben kabawa rusaika itama tasa kubar duniyar saboda dalilai masu yawa, kafimu 'karfin tsafi da jarumta domun duniyar matsafa ma tanaji da kai saboda jarimta zaka fimu iya kula da ita, maza kuhuce sunkusa 'karasowa". Yana kaiwa nan ya gyara takobinsa, yayiwa rusaika sumbata agoshi tare da shafa cikinta, yayi mata murmushi, hamit kuwa yayi saurin kama hannunta domun yafuskanci sotake ta karyar wa da sarki zuciya, saboda kukan datakeyi, nan take suka bar gun akan iska.
Sarki kuwa suna zuwa suka fara fafatawa da su, yana kashe na kashewa yana 'kona wasu daga cikin aljanun da ayar Allah, daya daga cikin wani bakin aljanine ya bayyana a bayansa ya daga hannunsa wani bakin hayaki ya fara futa ya d'ora hannun akan sarki hayakin yana shiga kansa take ya yar da takobinsa ya rike kansa, jikinsa yana karkarwa uwa mai jijjiga nan take ya fadi agun, wani aljani ya daukeshi ya bace dashi, kogon zu'kairu ya kaishi ya d'aureshi da wata sarka ta ba'kin tsafi tukun ya 'bace.
Bayan su Hamit aljanun sukabi, hamit yana bace musu wani lokutan saboda tsafin sa yafi nasu, amma zu'kairu dayake gida yana kallo tajikin wani mudubi shiyake nuna musu inda sukabi shima kuma wani zubin su 'bace masa, duk ransa ya 'baci burinsa kawai akamosu akawo masa su, yayi alkawari da cin alwashi irin kisan azabar da zaiyiwa Hamit dama naimansa yake.
_'KAUYAN MAGARYA_
Ganin wahalar da bakinta takeyi hakan yasa ranta ya baci ta kalli ginin da akeyi tayi fatali da bulo guda d'aya ya fad'i ya face tayi hucewarta.Gidan su Aisha kuwa sunata fafutukar siya mata abun bu'kata irin na gida, ummanta kuma tanata yimata fada da nasiya akan zaman aure, basu wani saka kansu yin taron bikiba saboda sunsan cewa gulmace kawai za azo aitayinta dan haka iya 'yan uwan tane na dangin uwa dana uba sukazo suke abunsu iya su isu.
Mustafa ne azaune a 'kofar d'akinsu yana gyara tsinkakken takalminsa, yana so ya futa, acan bakin murhu kuwa matarsace taketa fama da hayaki tana juya dafa dukan taliyar murji mai romo tana fyace majina da bakin zaninta.
"Wai ke Hansai haya 'kinnan baya damun kine? Inbanda shegen son kud'i wai bazaki siyi itaceba saidai ki had'o yayi kice zakiyi girkin sana'a dashi aikuwa kina cikin wahala". Goge majinar data futo mata tayi ta tashi tsaye, "Dallah can rufewa mutane baki, in ka damu kabani kud'in icen mana, jarinma naga nina d'orashi da kaina abincin gidan ma bamu kakeyi wadatacce badole in naimi sana'a ba, kaikuwa da bakada zuciya ai saikaitayi". "Kedai wallahi hansai bakida mutunci ni mijin naki kike gayawa haka to kije kiyitayi ni gidan ma zan bar miki masifaffiya". Yana kaiwa nan yayi fucewarsa yabarta da babatun banza dana hofi, "Wallaji baka isaba, kaibaka baniba kuma ina naima kace zaka mun ba'kin ciki dan wannan ba'kin cikine 'karara, wai ni ina Karime ne ma tazo taliyar ta sauka tatafi gun tallan nan kar rana tayi mutane suci abinci". Dakin su ta shiga inda ta iske Karime akwance duk tayi amai, la'ila ha illallah karime maiya sameki haka? Ganin ba amsa zata samuba yasata dagata tasa mata hijjabi, "Muje gidan mai magani ta dubamun ke". Itama hijjabi tasa tayiwa yan gidan bayani tafuce.
_AFTER 40MNT_
Hansai ce ta shigo cikin gidan tana kumfar baki, "Wallahi bazai yuhuba bazan taba yadda acikin gidannan ayi mun hakaba, ina bazai yuhuba". Nan da nan mutanan gidan suka futo suka tsatstsaya suna tambayar ta lafiya amma ina masifa da zage-zage kawai takeyi, malam Idi ne ya futo yace, "Ke ya isa haka koma mainene kibari anjima kowa ya dawo cin abincin rana sai atattauna". Jin haka yasa kowa yayi shiru Hansai kuwa ta figi hannun Karime suka shige 'bangaran su._4:00pm_
Kowa ya hallara a babban tsakar gida kowa ya zuba ido domun jin dalilin dayasa aka tarasu, malam Idi ya kalli Hansai yace, "Ke hansai mainene yasa dazu kiketa masifa kina kiran sunan Bashir kina aibatawa mai yayi miki?". Cike da masifa tace, "Dazu naje kiran karime tazo ta dau talla ta tafi na iske bata da lafiya hakan yasa nahuce da ita gidan mai magani, ta dubata ta tabbatar mun tanada ciki, kuma nasan halin tarbiyar danayiwa 'yata kuma duk gidannan kowa yasan shikadaine zai lalata mun 'yata dan haka wallahi sai anbimun hakkina". Mutuwar zaune Bashir yayi agun, Mustafa yayi tsalle yafara dukan Bashir Shafi'u ma yana tayashi harda Salisu Saminu duka suma rufar masa suna dukansa.
YOU ARE READING
DUNIYAR MATSAFA
Actionlabarine akan wata duniya ta matsafa wanda wani dalili yasa yayan sarkin duniyar sukashigo duniyar mutane ake fafatawa