☠️☠️☠️☠️
*DUNIYAR MATSAFA*
☠️☠️☠️☠️*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_we are here to educate motivated entartain our readers_©️
_Zainab Abdullah_
_real shaxee🍒__email_
rzainababdullah@gmail.com_facebook_
_zeenat deen shaxee__wattpad_
_real shaxeee__whatsapp nomber_
08085898952_youtube channel_
_Real_shaxee tv__wannan book d'in nasiyarwane inkina bukata kona bukata zaka iya tuntubar wannan nomber 08085898952 kokuma katuro 300 kacal ta wannan account nomber d'in 0068933035 kokuma katin MTN saikiyi screen shot dinsa kituro ta waccan nomber👆🏻_
_FREE PAGE_
_dadifa yakusa karewa free page yana dab da karewa kudai kuyi hanzari kuzo ku mallakeshi domun jin yadda wannan cakwakiyar zata kaya_
_PAGE 13-14_
A zabure ya mi'ke yana kallonta, "Ina fatan baeasa kike mum ba?". Kallon cikin nata yayi tare da shafashi, "Bashakka kinada ciki, ke agunki wannan matsalace amma aguna abun farin cikine, duk duniya banida burin daya huce in mallaki d'a namiji aduniya amma kuma ban samuba sai 'yata d'aya tak mulaika dukda cewa duk duniya banida abunda nakeso kamar ita amma inason d'a namiji". Wani farin cikine ya lullu'be kasira har ya bayyana a fuskarta, "Amma fa karka manta indai na haifi yaro namiji to bazaita'ba mulkar duniyar matsafa ba domun bamuyi aureba k.... "Ya isheki haka wannan karan zan canza dokar kuma babu mahalu'kin daya isa ya hanashi mulki a duniyar matsafa"."Saini!". Sukaji an anbata daga bayansu, da sauri suka juya dan ganin wanene mai wannan zarar, mulaika ce cikin shiga ta alfarma ranta amugun 'bace tana ri'ke da wata sanda mai muhum kyau da ado, "Atunaninku akwai wanda ya isa ya mulki duniyar matsafa bayanni? To kuwa kunyi kuskure babba domun akan mulkin nan zan iya yin komai kuma in hallaka kowanene da zaikawo mun cikas acikar burina". Cikin 'bacin rai take wannan maganar.
Zu'kairu yayi saurin ri'ke hannunta ganin ta nufi inda kasira take, "Mulaika inaso kishiga hankalinki kisan abun da kike cewa kuma dawa kike magana". Cikin 'bacinrai ta kalleshi tace, "Da sarki mai ci ayanzu nake nikuma sarauniya mai jiran gado kuma da babana nake magana, abu d'aya nakeso kasani muddin aka haifi yaro namiji to nice ajalinsa, kuma kasan zan iya duk abunda nace da wanda ma banceba, kai! Bama zai yuhuba wallahi saina illata cikinnan ko macece ma ba a isa a haifeta ba, dan haka gwara kama zubar dashi da kanka". Huci kawai sukeyi suna kallon juna uwa zasu cinye juna.
"Ya 'yata mulaika inaso kiduba halin danake ciki naburin haihuwar yaro namiji kibari incika burina nayi miki al'kawarin bazai mulki duniyar matsafa ba kece sarauniyar dazaki maye gurbina". Wani kallo tayi masa tukun tace, "Hmmm ya baba na kenan nasanka nasan halinka nasan komai, bazaka ta'ba yaudara taba kuma bazan ta'ba sauka daga wannan 'kudirin nawaba na rantse da abun bauta gurgur". Tana kaiwa nan ta fizge hannunta tafuce daga d'akin fadar.
Zu'kairu ya dafe kansa cikin damuwa da 'bacin rai, "Bashakka akwai matsala mulaika nita gado gun tsaurin hali da rashin imani, dole daga yau kasira kikasance a 'kar'kashin tsarewata". Hannu yasa yanuna bango nan take ya tsage saiga wani 'kayataccan d'aki ya bayyana, "Daga yau anan zaki kasance har ki haihu babu mahalu'kin daya isa yayi miki komai gobe za'a d'aura mana aure dake". Kasira tayi murmushi ta rungumeshi, "Nasan muddun kananan to babu mahalu'kin daya isa ya yimun komai ina alfahari da kai." 'Dakin ta shige nan take gun ya had'e uwa baitaba tsagewaba.
Zu'kairu cikin 'bacin rai ya 'bace daga fadar.
_MASARAUTAR KAM_
Masarauta ce maicike da iko mulki da isa, masarautace da garin kam suke jida ita sarki Abdullahi shine yake mulki a wannan masarautar yanada mata biyu Samira sai amaryar sa Maryam baita'ba haihuwa ba.
Samirace zaune a falonta wanda ya 'kayatu da kayan alatu na more rayuwa sanye take cikin shiga ta sarauta, a kashingid'e take akan tuntun nasarakai gefanta kuma hadimanta ne guda biyu, suna yimata fifita tare da bata 'ya'yan itatuwa tanaci tana yatsina fuska.
Jakadiya ce tashigo falon cikin sauri da hanzari tazube agabanta, hannu ta d'aga tayiwa hadimanta alama da sufuce subasu gu.
"Ya gimbiya Samira akwai mummunan labari dana ke tafe dashi". Tashi zaune tayi tare da kallinta, "Wane labarine haka Jakadiya wanda ya faru yau amasarautar nan mara dadin ji?". "Allah ya huci zuciyar uwar gidan sarki yanzu nakeji ance fulani tanada juna biyu". Wani malalacin murmushi Samira tayi sannan ta kalli jakadiya tace, "Nadade da sanin wannan labari kuma alissafi watan haihuwar tama ya kama, sun'boye batun cikinne su awayonsu cewa zasuyi maganin matsalarsu nan kuwa basusan cewa matsalar tana nan a inda suke ba, shima wannan yaron ko yarinyar abunda yafaru da wad'ancan shine zai faru dashi kedai kizuba mun ido, muddin ban haihu a masarautar nanba to babu wacce ta isa tahaifi sarki mai jiran gado". Murmushi jakadiya tayi tare da jinjinawa uwar d'akinta, "Ya shugabata harna shiga damuwa wallahi". "Hhhh nicefa Samira kedai kije duk sanda kikaji tafara na'kuda kizo ki gayamun".Fulani ce zaune akan kafet acikin lanbu wanda yake can bayan 'bangaranta gefanta kuma zagaye yake da kayan itatuwa ita kad'aice tana zaune tana karatun kur'ani dama duk yamma haka take kasan cewa, ko hadimanta basa zuwa inda take harsai ta kirasu tunda watan haihuwar ta ya kama take cikin fargabar abunda zai faru da wannan d'an kamar yadda sarki shima yake cikin damuwa.
Hamit ne zaune a gaban rusaika yana kallonta, "Dolane yau mufuta daga duniyar matsafa saboda kwanakin haihuwarki sun gabato nan kusa zaki haihu". "Yanzu d'ana hamit ina zamu nufa kuma ni abunda yafi damuna shine halinda su sarki suke ciki". "Karki damu komai zai dai-dai ta tashi muje". Hannunta ya kama yasa mata zoben tukun suka futo daga kogon dakarun Zu'kairu suka ci karo dasu nandanan yafara fafatawa dasu ganin zasu 'bata masa lokaci hakan yasashi buga hannunsa a 'kasa ya ri'ke rusaika wata wal'kiya ta bayyana sukayi sama suka face, nan take duniyar matsafa ta girgiza alamun wani daga cikinta yafuce kenan, basu sauka a ko inaba sai _MASARAUTAT KAM_
YOU ARE READING
DUNIYAR MATSAFA
Aksiyonlabarine akan wata duniya ta matsafa wanda wani dalili yasa yayan sarkin duniyar sukashigo duniyar mutane ake fafatawa