1

2.8K 119 6
                                    

*DEDICATED TO UMMU ABRAR*

1⃣_5⃣

BISMILLAHIR RAHMANIRRAHEEM,WANNAN SHORT STORY DIN FICTION NE BA TRUE LIFE STORY BANE AKIYAYE KADA A JUYA SALON WANNAN LITTAFI YIN HAKAN BABBAN LEFI NE GADUK WANDA YAYI!

🌷🌷🌷🌷🌷

Kofar dawanau A cikin unguwar d'an dishe, daidai kofar wani katafaran gida motar Mrs JH tai parking Baban gida ne Wanda yyi matukar tsaruwa, "sannu ahankali aminiyar ta miss xoxo tafara fitowa hannayan ta rirrike da manyan ledoji daidai lokacin gateman din gidan ya isa gabanta yana kwasar gaisuwa tare da karban kayan cikin ladabi, "saida Mrs JH ta fito suka shiga firfito da kayayyaki da suka siyo kayan kitchen ne na zamani ga dukkan alamu dai sund'an shiga kasuwa ne babu bata lokaci maigadi ya shigar da kaya cikin gidan me gadi ya karaso yace hjy na mika kayan duka Miss xoxo ta xuge jakarta ta bashi 1k ya tafi yana ta zabga gdy sa'annan suka nufi cikin gidan kowacce na fad'in wash alamar gajiya.

"a parlour sukaci karo da abrar sai faman jijjigar k'anwarsa bunayya yake tana tsaga ihu da azama Mrs JH takarasa ta amsheta tana tambayar INA uwar tata tabarta tana wannan kuka haka??

Abrar yai rau rau da ido kaman mai shirin barkewa da kuka yace aunty Wlhy umma batanan tinda safe abban mu na fita itama suka fita har yanxu basu dawo ba ga bunayya sai kuka take min na bata madaranta taki tasha! gama maganar yai dai2 da xubuwar hawayansa Dan ba karamin wahala bunayya tabashi ba, Ikon Allah Mrs JH tafada to INA tace maka zata?? Abrar yashare hawaye ni basu gayamin ba naji dai maman bobo tana cewa suyi sauri sutafi wai mutumin ya iya aiki indai tasaki kud'i tasa aranta an fasa bikin nan an gama.. 😳😳😳atare suka dafe girji suka furta Yau Munshiga ukku yayinda mrs JH ke sallallami tana xafga masifa gamida rafka uban tagumi ohh ni, hudda yanxu zainab bata d'auki duk hud'uban da nake aikin yi mata ba dare ba rana har saida tajefa kanta cikin halaka!

"Gaskiya bata kyauta wa kanta ba miss xoxo tafad'a kinsan kuma akwai xugar kawaye su zasu firgitata sukaita subaro, waima wacece maman bobo?? Duk suka xubawa abrar ido yace aunty jamila sunan ta. Kinji ko ai idan tabiye kawaye saisun tsiya tata zanin dazata daura ma sai ya gagareta wlhi, kinji wai harda fad'in anfasa auran angama, Abu nufin Allah akwai Wanda ya isa yahana abunda Allah ya rubuta faruwa ne Banda shirman zainab..

Mrs JH ta katse xoxo dacewa hmmm taso ne walhi kawayan banza fad'arsu har yafi fadar mu ko santa suka fimu banda hauka irin na zainab wani katon banxa ya isa yayi mata yanda takeso ne ina gaya mata idan Abu yadameta takai kukanta ga Allah shizai share mata hawaye amma bata ganewa.

Kukan yarinyar yasa xoxo cewa abrar kawo madaran mugani ko zata karba wannan ai haukane tatafi tabar maka yarinyar dake shan nono memakon ma taje da ita tinda tasa kanta a wahala dogon tsaki Mrs JH taja tareda janyo phone dinta cikin jaka rai a bace ta danna ma k'anwar tata kira, dalla malama kina ina kin tafi kinbar mana yara a gida sbd zabar hauka da rashin yadda da kaddara. hmm aunty hudda kiyi hakuri kinji!!! tasanar da ita gatanan tana daf da isowa gida!

🌷

Awahalce zainab takaraso gida Dan bakaramin surk'uk'in daji suka shiga ba gashi ko d'an achaba baka gani awajan bare karage tafiya tashi daya tai wani irin rama sai daqwa daqwan idonu wanda tashin hankali da fargaba suka kara hankad'osu waje,

Sosai Mrs JH ta balbaleta da fad'a inda take shiga batanan take fita ba miss xoxo ma ba'a barta abaya ba fad'i take ai naso inga ita jamilar datake saki ahanyar banza muci uwarta wlhi munafuka muna sak'a tanai mana warwara ke kuma da kika fita hauka sai kika kwashi jiki kunje gun boka sbd shi xai hana ai miki kishiya sai kace kanki farau. Ki duba dai kigani ga kawarmu maman shukra da tabi shawar warin mu batabi rudin Shed'an ba yanxu ita take juya gidan yadda taso mijinta yana ganinta da kima har cewa yai duk wacce ta taka uwar ya'yanshi sedai tabar gidan coz bata tada hankali ba tanuna ita ko ajikinta keko kinbi kin fitini kanki kinki kwantar da hankali kinsa mijinki gaba da bala'i yanxu datashigo Abu kad'an zaifaro yace halinki ne dama kin tsane ta walh kima kanki fada. hmmm fad'a mata dai XoXo, da dai Zainab taji basuda niyar kyaleta ga gajiyar data kwaso had'i da yunwa da tashin hankalin abunda boka yafad'a kawai sai tasa masu kuka.......

Haba aunty Ya kuke so nayi da rayuwata! kunsan abunda iyayen yarinyar nan keyi akaina kuwa?? Kunji muguntar da suke aikata min Ashe sunyi wunkurin data shigo bazan kara koda sati guda agidan nan ba.. Dalla rabani da zancan banza shi bokan yace miki haka?? To ta Allah batashi ba mu mun dogara ga Allah duk maiyi yaje Allah yafishi.

bare nasan walhi duk karyan matsubbata ne yanxu ma da zakije wajan wani shima wata karyan xai yanka miki tadaban, XOXO ta amsa da kwarai kuwa haka suke wata yar'uwata dataje mararta kawai ke ciwo tana zuwa gurin wani mai magani sai cewa yayi kishiya CE taimata ajiya aciki, taxo min da kuka aifa tajata sai hospital Ashe infection yaimata karfi yanxu haka tayi sumul harta haihu amma da han iskan yace idan bemata aiki ya cire ba bazata bata haihuwa ba aikinsu kenan macutan, Zainab tasharce gumi gami da cewa duk abban abrar ne yajamin mugu kawai maci amana walhi saida na gaya mishi ina da tsananin kishi banaso in budi ido inga wata akusa dashi xuciyata zata iya iya tar watsewa ta ida maganar cikin kuka,dogon tsaki sukaja ba wanda yace mata kala taci kukanta ta koshi da ta gaji tai shiru yaranta suka matso jikinta ta sanko da ga kan kujera ta xube akasa, ganin bacin rai karara a fuskar yar'uwan tata yasa ta kamo hannayan su ta dora akan kirjinta tace kuji yadda xuciyata ke bugawa ta kara fashewa da kuka kuyi hkri sisters nasan baxakuji dadin abinda nai ba duk iya kokarin da kuke akaina, pls sisters 4 give me yanxu meye mafuta?!

WRITTEN BY MRS JH AND MISS XOXO💐

DANNAR 'KIRJI...💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now