Tun daga wannan lokacin zainab take amfani da shawarwarin da auntyns dinta Mrs JH da mss XOXO, suka bata tai watsi da kawayan banxa dan ta fahimci ba hanyar gaskiya bace, ynxu shiri suke sosai da abban abrar tasakar masa jikinta yana gurxa San ransa tunda shi mutum ne mabukaci, ta kanainaye shi da kissa da kalamai masu dadi komai xai yi game da auran sai ya nemi shawararta' idan Fad'ima tayi masa waya kuma ta dan kwashe harshe tace yabata wayar su gaisa da kanwar tata' hakan data ke ynxu ya kwantar masa da hnkali har yanajin Santa nakara shiga bargon jikinsa, Addu'an sa Allah yasa hakan yadore yanda zasu had'a kai da Fad'ima da yayi farinciki Mara misultuwa,
GAREKU MATA!!! shawara inji Mmn shukhrah, idan Allah ya kaddarowa mijinki Karin aure, to ki karbi wannan kaddarar hannu 2 matakin farko dazaki fara dauka shine!! Ki kara mi xanin tsaftar ki yafi Nada, ki dinga tarairayar mijjnki sosai koda ada bakya tarairayar sa kixama mai hkri da kawaici ga duk rawar kan dazai yi akan auran, kikara maggi a miyar ki idan da bakya yin girki mai dadano, ki dinga gyaran hq fiye da nada, ki dinga kula da 'ya'yansa fiye da yadda kike yi da, kirage fita unguwa, ki kame kanki agida, kidinga yawan Tatar da sha'awar mai gidanki yana yawan kusantarki, in bakya jin kunyar sa to ki kokari kidinga yawan jin kunyar sa irin dai yadda muke yi na kissa, ki kuma gyara harshenki domin mgna mai dadi tana bada matsayi sosai gurin mai gida. Allah yasa mu dace ameen👏
3days later!!!
yau takama biki yarage saura kanaki takwas masu zuwa,
ayaune yan'uwan Zayyan keta kokarin harhad'a kayan lefe' na uwar gida dana amarya, Dan sunaso washagari sukaima amarya abinta, gidan Zainab yacika da jama'a Dayake anan suka taru dan raba kayayyakin, kasancewar komai yana a hannun Zainab gaba daya siyayyan da Zayyan yyi na lefe tare sukeyinshi da Zainab komai biyu yake siya kuma iri daya Dan dai yafaranta ran Zainab, kuma ya nuna mata halacci,
Zayyan ne yashigo rike da kaya Niki Niki a hannunsa yan'uwansa dake barbaje a falon duk suka bishi da kallon mamaki, da azama k'anwansa Aneelurv tamike tana cewa, "kaii yaya yanzu wasu kayan kasake jibgowa muda muke shawaran rage wasu ya xasuyi da wannan kaya fisabidillah?"
Rai abace Zayyan yadaga mata hannun yace, "kinsan bana san haka kar in kumajin wannan maganar abakinki nagaya maki, ina Zainab din take?
Aneesa ta yamutsa fuska tace suna ciki mana anacan ana kulle kullen da aka saba itada.. Mugun kallon da Zayyan kemata yasata yin shiru, "yace wuce ki kira min ita!" Aneesa tatabe baki azuciyarta tace wahalalle ai sekaitayi duk kabi ka kashe zuciya ka lalace akan mace sewani lallabata kake kaman wani shanyanye kodayake wannan dagani ba banza ba, ina tausayin Fad'ima Dan sai wani ikon Allah tasamu kolawan yaya yanda ko kad'an bayaso afadi laifin Zainab..
Hmmm saisu Aneesa dangin miji ba'a iya maku da an ce d'an'uwan naku nashirin karin aure anan zakaji ana tado tsofaffun laifukan uwar gida.. Tayi abu kaza, bata yi masa kaza hmm Dan Adam kenan😊
Cikin ladabi Zayyan ya gaisa da kanwar Hajiyansa wacce suke kira da aunty sis,, sannan suka shiga gaisawa da yan'uwa anata mishi murna masu tsokana nayi..
Cike falon Zainab yake da kasaitattun kawayanta irinsu Ilham Mohd,, Ayshet Mohd,, Hajara Mohd,,Fulalu,, Shafa'at Umar,, Kausar M Hasan,, Belly Badaru,, Halima A ilma'il,, Maman shaheed,, Faxy passion,, Jidda Aliyu,, Umma Yahya,, Zahra Ibrahim,, Rahma Rufa'i,, hira suke sosai ko wacce na irin nata *DANAN KINJIN* tahanyar kwantar ma Zainab da hankali da kalamai masu dadi, sa'annan suna sanyata akan hanyar dazatabi ta tsira da mutumcinta bawai takama bambamin banza ba, Zainab kam ba baka se kunni sedai idan anyi abun dariya tadan murmusa amma.. sallaman Aneesa yadakatar dasu Aneesa tashiga binsu da kallo da tashiga da niyyar kallon raini amma tana ganin irin suturar dake jikinsu sai tai lakwas, tajuya ga Zainab tace "kwari me kwara miya in anjima ki kwara ashar " sai kizo Ga yayana can yashigo kin wani kunshe a daki koma me ake kitsawa oho aure dai babu fashi sai munyi ehe.. Kafin tarufe baki Zainab xatai magana Ilham tarigata dacewa idan Baku auro yan mata ukku a rana daya ba Baku cika Zazzagawan asaliba, nagaba yai gaba dan kiji mu bama shakkanta Dan uwarta ko yar gidan uban waccece, Jidda Aliyu takara dacewa , maganarki hakkun ita din banza tadade batazo ba ai da tsohon Zuma ake magani,, yayinda zazzakar murya Aneelurv ketashi zakwakwai tana mayai masu da martani Dan kafin sufadi daya ta fadi ukku, Mrs Umar tace da Zainab tashi kije mana kinga irinta ai kin tsaya jin wannan soki burutsun.. Aneesa taisaurin cewa shiyasa zamu dauko mai kuladamu ehe😏 Munayshat tadaka mata tsawa Aneesa kike kowa, ki iya bakink.. Sanin halin Aneesa yasa Ummu Adnan toshe bakin munayshat sannan taja hannun Anee tana dariya tace fita kikama gabanki kaddai daga wasa ku fara mana tashin bama bamai, ana zaune kalau...
YOU ARE READING
DANNAR 'KIRJI...💞(COMPLETED✅)
Short StoryDannar kirji... Gajeren labari mai dauke da darussa kala kala na wata uwargidah da akaiwa abokiyar zama(amarya)😻💕..NA MRS JH AND MSS XOXO