Mrs jh tai murmushi yanxu kika dawo hanya yar'uwa, miye mafuta kuwa banda ki mayar da al'amuranki ga Allah haba zainab yanxu me abban abrar yagaza miki acikin gidannan dahar zaki saka kanki a halaka ke da bakinki kinsha kawomin kukanki akan yawan bukata irin nashi damuwa kike sosai coz takuran dayake miki dukda haka kince da hakuri yake karawa yanxu dan Allah miye laifinsa Dan yace zaikara aure? Shin ko kinfiso yajefa kansa cikin halaka yanabin Matan banza mutincinsa yaxube shi kuma ba wai yasara abinda zai rike mace koda hudu ba wanan babban kuskurene muce wai saidai mazanmu su zauna da mace daya shin sauran mata suyi yaya??? yanxu a binda nakeso dake kina jina kibud'e kunnuwa kiji abinda xamu fad'a maki sannan kuma kiyi amfani dashi nasan babansu Abrar na tsananin sanki halittarsa ce bazata iya hakuri da mace daya ba, ga dayar kuma Allah ya hadashi da raguwa mara juriya! amma kinji zancan kishiya dan munafunci har... auty walh ina iya kokarina indai ba kasheni kukeso yayi ba ko haihuwa nayi andade asamu sati biyu amma duk da haka mugun mutumin nan sakaiyan dazaimin kenan d'an kutumar uba kawai maci amana😭
Atare xoxo an mr JH suka bushe da dariya cikin dariyar xoxo tace da'alama zainab kinkusa haukacewa shifa kishi haka yake yawanci duk wacce za'a yima saikinga tayi wannan haukan, "Mr JH tahadiye dariyarta sannan tad'ora da cewa hakane aikoda kace kishiya bawani Abu bane kadai faha babu wacce za'aimata bataji zafiba sedai hakuri, kishin da yakamata zainab tayi shine tadage da gyara jikinta walh indai miji zai jiki zamzam kinfi gaban wulakanci amma bakijin shawara koda mun kawo maki abunda zai amfaneki sekice ba xakisha ba miji zai takuraki amma dagajin batun kishiya kin kwashi jiki kin biyewa zigar kawaye sun jaki xakije kijefa kanki ga halaka ko ma nace kun halaka, dan yanxu kyakyawar sallar ki ta kwana 40 baki da ita sai ki ta istiqfari kituba kuma yiki alkawarin baza ki sake aikata shirka ba dan duk wanda ya hada Allah da wani to yayi shirka Allah ya tserar damu ga aikata sabo, Ameen cewar zainab dan jikinta ya gama yin sanyi tana Dana Sanin biyewa shawatar jamila, XOXO tad'an murmusa gsk yarki sis dasake yar Uwa Sam wannan tsarin naki beyiba kicanxa taku sekace wata jahilar kauye haba Zainab bakisan duniya ba haryanxu gaskia ..
ga abunda yadace kiyi kin kama wutsiyan watari zancan boka haryanxu idan natuno daxu yadda bunayya taketa kuka wani tukukun makoko ne ke tsayamin awuya Wlhy kmr na kifeta da mari.
..UMMU abrar tai
murmushin dole to naji nayi kuskure ayi hakuri baxan sake ba dan ni kaina natsorata da wannan boka, ku kunga k'ungurmin dajin damukaje Wlhy munsha wahala wani abin bakin cikinma har dasu cemani wai kishiya baxa'a fasa taba sede in tashigo afidda ita,Yana fad'in haka nai tsaki azuciyata to tinda xata shigo Dan Allah meye amfanin xuwanma ai seda mukayita da maman Bobo shiyasa ko gidan nan taki shigowa tun a titi muka rabu da juna kuma Sarai nasan fushi tai!
Mr jh taja tsaki wannan kuma ke kikaba kanki wahala wallahi da boka ko Malam babu Wanda ya Isa yahana abinda Allah yace sai anyi faruwa kuma kisani shi Karin aure kaddara CE in Allah ya kaddara ma ko baka da ra'ayin yinsa lokaci daya Allah xai sakama sha'awar sa a xuciya kuma dama tun farko kekika siya da kudinki wallahy munsha Gaya maki yadda xaki shawo kan mijinki amma kememe kinki waike baxaki jureba,to ai gashi nan wadda tafiki taku xata shigo gidan naki taxo tasamu fada kina xaune da yan' ya'yanki biyu xata shigo tsakani!!!!
Ummu abrar ta zabga tagumi to yanxu niya xanyi fisabilillahi?! Yakukesan insa Raina kalla dinning Table kigani breakfast din danai masa ko tabashi beyiba yana nan yadda yake Wlhy..,miss xoxo tajuyar da fuska Tana kallon kofa, 👉kee dae Ummu abrar Wlhy kina ban mamaki kinfasan Sarai me mijinki keso amma kememe kin badawa Idonki kasa akan hakan wallahy yamun Dede da beciba tunda ba abinda yake nema ba kenan. Ace tinda yafara Neman aure shikenan kita axabtar dashi har fadi kike kin hanashi kanki sekace wadda tayi abun kirki baki ko tsuran Allah walh idan baki canxa ba kinagani mai bayarwa xatazo ke watama akan idonki zataja ra'ayinsa dan kiji haushi. nashiga ukku Dan Allah karkusa xuciyata tabuga suka dau dariya JH tace yanxu dai abinyi gobe ko jibi xamuxo da k'awar mu Mrs adamss Dan tashiryaki yanda ko amaryan albarka Dan tasan surruka dadama na kayan harka
"xoxo tace wannan haka yake saura kuma ki kisha mude baxamu juya maki baya ba kuma xamu baki shawarwari irin namu na mata, dukda kince kina ganin yarinyar batada kirki Hanya daya xakibi ki tsereta wannan hanyar itace KISSA kuma ki gwada ki gani ga kissarnan kala kala Wanda basukai shekarunki bama sun iya akwai kissar magana, kissar abinci, kissar shagwaba, kissar kwanciya ..gasunan kala kala sewanda kikayi amma kya kama shirme.
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Ummu abrar tace naji wallhy kuma nagode da shawarwarin ku insha Allah xanyi amfani da KISSA naga ko hakan xe xamto mafita?!kuma kuncika yan halas DANNAN K'IRJI dakukai min yanzu tabbas yakwantar min da hankali dan daxu wani biyi biyu nake gani...
To Allah yasauwake cewar Mr j
Miss xoxo ta kalli abrar da tintini yai baccin wahala tace dan Allah ji yanda yaran nan ya fada ya rame wallahy Ummu abrar baki kyautawa dubi abrar yaro bulbul dashi jibi yadda yarame to shima da yake yaranki ya koma hk ina kuma ga Baban shi watakila shi baxai ganu ba dan rama, zainab tace insha Allah Komi xedawo normal yanxu! Allah yasa cewar Mrs JH ynxu abinda nakeso kiyi shine xamu tayaki gyaran gidan gaba daya mu tsaftace shi yadda in baban abrar ya dawo ofis tun da ga hk xai san canji yaxo kuma ki shiga kitchen ki markada fruit ki sha inaso ki tsima kanki kafin dare ki bashi hakkin sa da kika dau tsawon lokaci baki bashi ba cos dan xai kara aure inaso ki bashi kulawar da bai taba samu ba agurinki kuma inkin san da gashi a jikinki kije ki sheaving ki gyara djk sako da lungu na jikinki ki koma zee dinki kamar yadda kike da inaso kinuna masa komai ya huce kice ya yafe miki Sharrin shedan ne ki hada harda kukan kissa, oya jeki ki gyara jikinki mu xamu gyara miki gidan musa turaren wuta !!! inkin yi wankakixo xoxo ta kitse maki kanki ga hennah cikin jakata kixo amaki, xamu shiga kitchen miyi aroma medadi Sannan xamu tafi idan abbansu abrar yadawo Dan Allah kidaure kitareshi cikin shagwaba kissarki tafarko kenan Komi kinuna ke yarinyace karama agabansa kisa kaya Wanda xasu dauke hankalinsa kitabbatar su abrar basu bata maki show ba..sauran bayani xamuji awaya...😜
Dahaka suka mike alokaci daya suka fara gyaran gidan.
YOU ARE READING
DANNAR 'KIRJI...💞(COMPLETED✅)
Short StoryDannar kirji... Gajeren labari mai dauke da darussa kala kala na wata uwargidah da akaiwa abokiyar zama(amarya)😻💕..NA MRS JH AND MSS XOXO