chapter 18

246 34 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

18👯
Kowa ya girgiza da mutuwan khalifa farat daya babu wani cuta ko jinya, hakan ya jawo rashin walwala a Mailafiya family dan sunyi babban rashi Bayan watanni 2 Kuma Zainab ta aihu ta samu 'yan biyu Suma maza saidai sabanin iyayen su kaman su hakk kaman an tsaga Kara gasu kyawawa farare Tass don kamannin uwar su suka dauka,

Kwata_kwata Zainab bataso haihuwan twins ba dan a ganin ta Bazata iya dawainiyar su ba, itafa har yanzu ma Bata shirya aihuwa ba da marigayi khalifa ya matsa Mata ne yasa babu Yanda ta iya ta yarda, saidai tayi farin ciki da hakan ko babu komai yanzu tana da Wanda zata dinga kallo a matsayin jininshi Wanda ya fito daga tsatson ta,

Yara sunci suna Sa'ood da Sa'eed anyi hidima sosai ranar sunan su Kuma anyi jimamin rashin mahaifin su Wanda ya kasance babban 'da wurin baba alhaji, twins Basu wani samun kulawa daga wurin mahaifiyar su Banda sahayar dasu babu abinda take musu haka zata sake su ma nanny suyi ta fama a saboda haka suka fara rashin lafiya,

Hafsat ita ta zama Mai kula dasu gaba daya duk wani dawainiya nasu ita takeyi dan Samm Bata da qyuya, haka tayi ta fama da qananun yara 3 har saidaasuwan khalifa ya cika shekara guda sannan Aliyyu ya tada zancen komawar su Mexico dan shi sauran kadan ya gama nashi karatun fannin likitanci,

Hafsat taso tafiya dasu gaba dayan su Amman baba alhaji ya Hana yace ta ajiye 'daya wurin mahaifiyar shi sai ta tafi da daya Dan idan suka Mata yawa ba zata maida hankalin ta Kan karatun ta ba Daman yanzun ma lallabawa ne, da suka tashi tafiya sai ta dauki Sa'ood ta bar Sa'eed,

Bayan shekaru 2 suka Gama komai suka tattaro suka dawo gaba daya ya zama sauran Ishaq ne da sauran 'yan uwa a can, lokacin da suka dawo su Sa'ood suna yawon su ko Ina ga magana a bakin su kaman Wanda suka Sha ruwan baru hakan yasa shekarun su hudu a duniya aka saka su a makaranta,

Duk cikin su Sa'eed ne bayi qoqari a makaranta kullum haka yake zama yayi ta kallon mutane bayi gane komai, sai anzo text ko exams Nan ake ganin aikin dolanci dan saida ya maimaita primary 1 sau biyu a hakan ma da pass yake wuce wa,

Haka ya tashi abin bayi damun shi Kuma duk gidan babu Wanda ya taba Masa fada ko Kuma Jan kunne akan rashin maida hankali a kan karatun shi, sai Hafsat ne ta fara kasadan yin shishshigi, suna zaune a parlon ta suna wasa ta jawo shi gefe ta zauna sannan ta daura shi Kan cinyar tace

"Sa'eed Chéri baka zo ka biya min karatun ka ba fa? Kaga naji na brothers dinka Amman Kai ban taba Jin naka ba"

Sunkuyar da kanshi qasa yayi Yana making sad face yace
"Mamanmu ai bani ganewa ne sai aunty tayi ta turanci da sauri_sauri ni bani Jin abinda take fada Kuma idan aka ce nayi karatu nayi sai tace wai qwalabe nakeyi I'm a fool su Sa'ood suyi ta min dariya"

You can start calling me cariña(darling) kaji yarona, and inaso duk lokacin da baka gane wani Abu ba kazo ka tambaye ni I'm ur darling kowa a duniyar Nan Yana sharing problem dinshi da Wanda yafi kusa dashi Kuma ya damu dashi that's his darling, yanzu kana so in dinga koya maka karatu?

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now