chapter 43

239 40 13
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
  🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
                          BATA WANE👩🏻‍🦱
   💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *Na*
        *UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Special gift to *Muhammad Karim*
       *And Fenarh matar Soja*

42👯
Da sallama Sa'eed ya shiga dakin ya same ta zaune tana jiran zuwan shi, amsa sallamar tayi hade da gwada mishi wurin zama ya zauna yana facing dinta hade da fadin "gani momy al'amin yace kina nema na"

Gyada kai tayi tace "eh akwai maganar da nake so muyi da kai ne akan matan ka"

Zuba kunnuwa yayi Yana sauraron ta tace " kasan dai kaman Yanda Saleeha take jinin mu haka ma Zarah itama jinin mu ce gaba dayan su Kuma matan ka ne kasan da Haka ko?"

"Haka ne momy"

Taci gaba da cewa "to bani so ka tashi da shanyayyen barin jiki ranar qiyama saboda kana rashin adalci a tsakanin su Kuma hakan ya bayyana a fili kafi son Sarwa, Zarah uwar 'ya'yan ka ne, ta zauna da Kai cikin wuya cikin Dadi kada kayi Mata butulci kowa shaida ne Akan irin son da takeyi maka, ko Kuma don girma ya fara Kama ta ne kake so kayi mata butulci?"

Girgiza Kai yayi da sauri yace "Aa momy, kiyi haquri insha Allah Zan gyara"

"Ba Mani zaka bada haquri ba, Zarah zaka bawa haquri, tunda Kuka dawo gidan Nan ta canza gaba Daya kaman ba ita ba tayi sanyi Bata walwala, ka dubi Yanda take son zuwa orphanage kodan ta baza yawon ta son ranta amman Jiya tunda muka je tana zaune wuri daya Kuma laifin ka ne, Kai kake sata taji kaman Bata da sauran amfani tunda ta Riga ta aifa maka 'ya'ya ta tashi a aiki"

Sa'eed yasha mamaki Sosai da momy ta tunkare shi da wannan Maganar lallai da gaske ne kowa a cikin su ya koyi darasi na rayuwa domin da ada ne saidai mamanmu ne Mai Shiga al'amuran su Amman momy nata Ido,

Yana fita daga part din momy ya koma nashi, Babu kowa a parlor kasancewar yau asabar Yara sun tafi islamiyya cikin orphanage haurawa sama yayi ya fara duba dakin Salee ya hango ta kwance tana barci ya fita ya duba dakin Zarah itama bata ciki ya sauqo ya Shiga kitchen,

Tana tsaye tana frying Kazan da zata saka cikin abinci ya shigo, maids din dake Taya ta aiki suna ganin shi kowa ya fita ita Bata ma sani ba, ta baya ya rungume ta hade da daura kanshi saman kafadan ta Yana cusa hancin shi gefen wuyan ta Amman zafin da yaji jikinta yayi yasa yayi saurin juyo da ita Yana Mata kallon tuhuma,

Kawar da kanta tayi avoiding his looks ya saka hannun shi ya dago da kanta making sure tana kallon cikin idon shi yace "me take damun ki?"

Hannun shi da ya riqe Mata fuska ta cire tana juya Masa baya tace "Babu komai" taci gaba da motsa kazar ta, sake juyo da ita yayi cikin 'dan fada yace "me yasa Baki da lafiya Baki fada min ba?"

"it's just a slight fever miel, nasha magani zuwa zai sauqa shiyasa Banga fa'idan fadan nashi ba"

" Tun yaushe Kika zamo likita? Kuma Bayan haka ma ai ko Dan Baki fada min saboda na Baki magani ba Zaki fadamin a matsayina na mijinki this is not fair yanzu idan wani yasan Baki da lafiya Kuma bani da masaniya a Kai fa? Wani irin miji za'a dauke ni?"

KAMA DA WANE....(Completed)Where stories live. Discover now