AL-HUDDA(SHIRIYA) A Hausa Novel
Sultan ya shigo cikin gidan yana duba versace wristwatch din shi. A hankali yayi sallama ya shiga main entrance wanda ke leading dinshi to parlour din da hajiya zaynab ke zaune. Ta amsa tana kallon shi da murmushi Sai yanzu ka iso? Kamar wanda ya taho daga sokoto.