*Assalamu alaikum warahmatullah!*
The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR
MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi rayuwar wasu masoya guda biyu wanda dukkan iyaye da yan uwa sun san wannan soyayyar, sai dai me? MARYAM ta yi rashin HAIDAR a daidai lokacin da zuciyarta ke tsananin kaunarshi, a daidai lokacin da tafi kaunar sa, a dai dai lokacin da take zaton ba abinda zai raba su, a lokacin da take tunanin burin ta ya gama cika a rayuwar ta gaba daya. Daga nan rayuwar ta ta fada kunci da tashin hankali, wanda ta dalili haka ta rasa maganar ta bama wannan ba wata daya da rashin HAIDAR aka gano MARYAM dauke da cikin a dalilin cikin mahaifin ta ya kore ta daga gida wanda barin ta gida ke da wuya ta manta wacece ita, ta manta kowa nata.
#To wai wannan cikin wanene? #Me ya faru da HAIDAR (Mutuwa yayi ko kuwa)? #Me zai faru da rayuwar MARYAM?
Ku daure damararku masu karatu domin labari ne da yake tattare da abubuwa masu yawa, akwai tsantsar soyayyar, sadaukarwa, hallaci, tausayi, da illar rashin sanar da iyaye abinda ya kamata su sani, illar rashin bawa iyaye hakkin su da sauransu, kudai kada ku bari a baku labari
Ban yi alkawarin dole abin da kuke so shi za ku samu a cikin labarin ba, sai dai zan yi bakin kokarina don ganin labarin ya yi armashi fiye da tunaninku. Sannan banyi alkawarin yi muku typing a ko da yaushe ba amman insha Allahu duk sati zaku samu typing daga Monday zuwa Friday.
Ku bibiyi alkalamin Maryam S Indabawa dan jin wanne irin sako ke kushe a cikin wannan labarin.
Zai fara zuwar muku nsha Allahu
Thanks
Antty