Amincin Allah su tabbata agareku Masoyana...!!!
Ina yi muku fatan Alkhairi da kuma fatan samun Albarkar wannan Wata Mai Alfarma ta RAMADAN. Waɗanda basu samu azumtar wannan Wata ba, cikin Marasa Lafiyanmu da kuma Mamatanmu waɗanda suka riga mu gidan gaskiya, Ya Allah ka kai haske kabarinsu kuma ka yafe musu kurakuransu!.
Mu da muke Azumtar watan Ya Allah ka mana Albarka cikin tarin Albarkar da ka yiwa watan!. Ka Amshi Sallolinmu da Addu'o'inmu!, Ka Azurta mu da Halal ka tsare mu daga Haram!, Kasa Mu kasance daga cikin Ƴantattun Bayin da zaka Azurta su da shiga Aljannahr ka Maɗaukakiya!