🍂🍂🍂🍂🍂
HAEEDARR
(love story)
🍂🍂🍂🍂🍂Writing by
ALIYU ISHAQ
(fast class)________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com🅿 30↔35
Daga marubucin
UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
SANDAR GIRMA
And now
↙
HAEEDARRR
(live story)Dedicated to hassan A T K
special gift to anti Hauwa (Maman Usman
Taka dabance daddy na Hussein 80k ALLAH ya bar mu tare
MAKARANTA
......ina kwance acikin dakin mu bansan SANDA bacci yayi awo gaba dani ba na jima ina baccin nan dan banji shigowar Abdul ba sai ji nayi yana tashi na dan nayi sallah azahar
Ban yi masa mgn ba na shige bandakin mu danyin alwala ina fitowa na shimfida sallaya na tada sallah
Ina cikin sallar nehh naji shigowar mutum cikin dakin namu bayan na idar da sallar nehh na juya dan ganin wanene haka iya yanxun muda bama Wanda MUKA sani a makarantar ina juyawa nayi ido hudu da ita ta kura min idanu batamasan na idar ba
Ba kowa bace face babbar kawar mu xuly dan guntun murmushi nayi kana nace"ah Ashe manyan baki mukayi kece haka yanxun nan
Eh nice wlh na kawo muku abinchi nehh naga lokaci yayi
Kular gabanta na kalla sannan nayi murmushi nace"to gdy mukeyi amma bamu takura ki ba kinga anan ma akwai komai karmu shiga
Ban karasa ba tace "ai ba komai nifah nasa kaina karka damu heedarr
Nace " to mungode
Hakan yayi dai dai da zuwan Abdul daya dauko plat dan juye abinchin da Zuly ta kawo tunda ya shigo ban kuma mgn ba na maida hankalina akan dannen danakeyi a wayana duk dagowar da xanyi sai naga xuly na satar kallona amma saina basar dan ni ban kawo komai a kaina ba
Abdul na bude abinchin wani kamshi ya daki hancina bansan SANDA na kulle idanuna ba Ashe tana lura dani a fili tayi murmushi sannan tayi kasa da kanta
Ina jin Abdul na "fadin kai Ashe dai kawar tamu ta iya girki to ALLAH yasa dai ba Iya a filin bane ba kare muci miji ba dai dai koh ya kace haeedarr
Kai kawai na gyada masa
Suka ci gaba da yan surutan su ina jinsu
Ji nayi zuly tace " kai bari dai na baku guri dan naga idan b fecewa nayi ba bacin abinchin nan zakuyi ba harma yayi sanyi
Nidai bance komai ba dan har a zuciya ta nasan hakan nehh wlh Indai tana gurin nan sai dai nakai dare amma bazan ci abinchi a gabanta ba
Kulan ta ta dauka ta tafi na fadin to sai kun fito koh Abdul yace "ok gamunan ba tace" ok
Tana fita Abdul ya taso da abinchin a hannunsa ya dire a gabanta tare da warce wayana yasa a bayan sa yace"abinchi
Ban yi mgn ba na dauki cokali na dan tsakuri abinchin wani testing danaji nehh yasani lunshe idanu bansan SANDA nace"masha ALLAH a fili ba
Abdul ya gane abinda nake nufi dan haka baiyi mgn ba shima ya haucin abin chin bayan mugama nehh kowannen mu yayi wanka MUKA fito
A gaban bishiyar jiyan nan MUKA taradda ita kamar yarda ta fada sai dai ba ita kadai bace ba tana tare da wata kawarta nehh wadda da gani itama sabuwar Zuwa ce a zuciya ta nace"kila abikiyar zaman ta ce
Haka MUKA ci gaba da matsawa gurin da suke tun daga nesa na karewa wannan budurwa Dana gani kallo duk da a xaune take amma naga tsantsar kyau a tare da ita budurwa na da karamin jiki sannan fuskar ta ma ba mai fadi bace ba tana da manyan idanuwa wadanda suke dauke dogon hancin ta da dan karamin bakinta idan tana mgn kamar batason yin mgnr a hankali bakinta ke motsawa
A hakan dai muna matsawa gurin su na fahimci zuly bata ma ganmu ba gani nayi wannan budurwa ta mike da hanzari Ashe kadan gare nehh ya nufo gurin ai tana mikewa nakara rudewa nan take na nemi nutsuwata na rasa sakamakon ganin irin kirar da ALLAH ya bata
Tana kasance Ita ba doguwa ba ita ba gajeriya ba sannan tana da faffadan kugu cikin ta ya kasance a shafe tamkar bata taba cin wani abinci ba a duniya kirjinta a cike yake da na shanu ina kaiwa nan na kauda fuskar ta tare da daure ta tamau sabida naga mun iso inda suke
Abdul nehh naji yana fadin"haba NINA wai tsoron kadangare kikeji yana kaiwa nan ya tuntsure da dariya
Daure fuska wadda aka kira da nina cikin voice dinta mai dadin sauraro tace"eh din ba komai idan naji tsoron sa saime kaima ai akwai abinda kake jin tsoro
Abdul yace"hb yarinya nidin nehh nakejin tsoro wuce nan yarinya
Nina tace "wace yarinya
Abdul yace " watace wai ita Nina
Tace"ai na zata dani kake da kaga yarda akeyin ta anan
Kin kula ta yayi Dan yasan ta akwai saurin hawa dan kwana dayan nan da sukayi tare ya gano hakan dan Abdul akwai shi da gano yanayin mutum sosae
Nikam tunda Nazo mika gaisa da xuly ban kuma mgn ba inajinsu sai chaftar su sukeyi nayi dagalo ina sauraran voice dinta dake kara rikita ni
Dago war dazan yi MUKA hada idanu da ita naji zuciya ta wani buga da karfi da sauri na kawar da idanuna tare da dare kirjina ta lura da abinda nayi sarai amma ta basar ta nuna kamar bata gani ba
Abdul da zuly nehh da suka lura da abinda nayi sukayi saurin matsowa kusa dani Abdul ya riko hannuna tare da fadin"yadai bros haeedarr da damuwa nehh
Kai na daga a hankali na kali Abdul nace "no ba wata matsala bros
Nan na kalli zuly nace" ya meye lbr nehh ni duk asona na kauda tunanin su nako yi nasara nan dai muka dan taba hira kadan kowa yayi nasa bangaren sakamakon kiran sallar da akayi
WASHE GARI
.......da misalin karfe Tara da rabi muna cikin hall ana mana lecture naji wayana na ruri dayake nasata a silent neh
Daga wa nayi na sa a kunnena a hankali ina fadin baba dan Gida muna lecture nehh zan kiraka
Daga chan naji muryansa na fadin ka fadama shugaban makarantar ALLAH yayi wa Maman ka rasuwa k taho yanxun nan yana kaiwa nan ya kashe wayan
A fili nace"innalillahi wa'innah ilayhirraju'un kawai na yanke jiki na fadi kasa sumamamme..........
TOHH KA KA KARA KAKA ALLAH DAI YA KARBE ABINSA SHIN KOYA RAYUWAR WALIDA XATA KASANCE ACIKIN GIDAN NAN BAYAN BA MAMANTA BA HAEEDARR DINTA BA BABA DAN GIDA KUDAI MUJE ZUWA
TO WAI SHIN KASHETA AKAYI KO MUTUWA TAYI NEHH MA NIMA DAI INA DA WANNAN TAMBAYAR
vote
Comments and sharedWhatsApp number 08143314152
By fast class
YOU ARE READING
HAEEDARR BY FAST CLASS
Romansalive story wannan labarin ya faru a gaske duk abin da kuka karanta a ciki gsk nehh y faru