BABI NA 4

11 2 0
                                    

Maimuuuu 🐾

*004*

Tafiya yakeyi a hankali kamar baya son taka kasa daga gani bazai wuce shekara 30 bah hand gloves inda ke sanye a Hannunsa ya cire ya jefasu a Dustbin duk inda yabiya gaidashi staff in keyi daga musu hannu kawaii yakeyi office insa ya shiga wanda aka rubuta *DR.AMIR AHMAD TURAKI* aka rubuta a sama   all black and white ne office in

Files in ya fara dubawa da sauri saboda Dad insa ya Kira shi

Bude kofa yaji anyi ba knocking wata budurwa da zata Kai 22 ta shigo cikin office din nasa fara ce suna Dan kama da shi amma ya fita kyau kaya matsatsu ne sanye a jikinta riga da skirt sai gyale data rike a daya hannun tah sai Kuma daurin dankwalin ta ture kaga tsiya da gashin atachment da ta sako ta baya

Mesmirizing eyes nashi ya dago Yana kallonta sai kuma ya dauke Kai ya cigaba da aikin sa

"Love" tafada cike da yanga
Ko kallonta baiyi bah ya cigaba da aikin shi"Haba boo bakayi missing ina bane ina sauka fah ko Gida banje bah na zo ganinka" tayi maganar cikin shagwaba "did I call you?, and why did you enter my office without knocking"  yafada batareda ya kalle ta bah

"Ohh sorry babe baazan sake bah" shiru yayi bai tanka ta bah ya cigaba da duba files inshi zama tayi saman kujerun da ke gaban desk in sa tana jiran ya gama shi kuma Yana sane dashi take jira Amma  yayi kamar ma Bata dakin bayan kamar minti 30 ya gama duba files in sannan ya Mike itama mikewa tayi tareda matsowa kusa da shi tamasa peck ga kumatu"babe zan wuce Mummy na jirana"  "bye" kawai yafada koshima saboda ummun sa tace yadaina kyaletah murmushin jindadi tayi ta Kara yi masa peck ga Kumatu ta fita

Tana fita tayi tsallen murna Bata ma so wucewa yanzu bah Amma mummy tace mata ta dinga jamasa aji "Yanzu aka fara , Amir na Lauratu ne ita kadai " tafada afili tana wani murmushi

Shi kuma bedroom inda ke makale da office insa yashiga tareda cire labcoat insa ya ajeta a gefe yaso yayi wanka anan Amma baida extra clothes tareda shi wayarshi ya dauka sannan ya fice daga office in gabadaya wata Mercedes Benz baka na ga yashiga tareda janta dagudu yabar asibitin

Wani  makeken Gida naga yashiga Kai  wannan Mansion ne katoton gate naga an bude mishi ya shiga wanda wurin yake kamar garden flowers ne ta ko ina sai wasu dakuna kamar na masu gadi sojoji ne cike a wurin, wani gate aka bude masa yashiga nan ma sojoji ne birjik amma wannan parts parts ne dayawa sai Kuma wani abu kamar waterfall a tsakiyar gurin fitowa yayi yashiga wani part Wanda aka kashe dukiya dayawa aciki , wani parlour ya shiga komai Golden nee Kuma royal

Gefen parlourn ya shiga ya bude wata kofa saiga wani parlour Kuma everything black har kujerun kamar dai wancan parlourn amma wancan yafi girma wata kofa Kuma ya Kara budewa  ya bayyana wani katon daki dakinma komai Black ne wayarsa ya aje saman royal gadonsa dazai iya daukar mutum Biyar ya cire agogon Hannunsa yashiga toilet ko toilet inma abun kallo ne kayansa yarage sannan ya had'a ruwan wanka yafada cikin jacuzzi in tvn ne lake a gaban jacuzzin Saida yakusa away daya snn ya fito da towel daure ga kugunasa muscles insa Kai daga gani Yana zuwa gym wannan

Gaban mirror yaje yajawo kujera ya zauna ya fara shafa ma jikinshi mayyuka sannan ya shafa ma gashin shi mai sulbi da kama da na yan India  bayan yagama shafawa wa yabude wadrobe insa ya dauko black jallabiya da vest yasa sannan ya fita daga part in gabadaya wani part naga yashiga parlourn komai grey nee harda tiles
Wata budurwa ce wadda ke kama dashi Amma idan bah kusa da ita ko shi kazo bah bazaka ga kamar bah "Hamma ina wuni" tafada da murmushi a fuskanta "Lafiya lil, ina ummu" "tana sama" gyada kansa yayi ya wuce "am Hamma " juyowa yayyi Yana kallonta "idan ka fito Hamma ga abinci can a dining please kaci ninayi" tafada cike da farinciki murmushi yayi me sanyaya zuciya ya Kara gyada kai

Saman stairs in yafara hawa parlour Dad yawuce directly don yasan ummunshi na can bude kofar yayi ya shiga da sallama wani mutumin dazai Kai  shekara 50 nagani  wata mata  zatakai 46 zaune gabansa tana zubamasa abinci murmushi ya kumayi ganin iyayen nasa "Dad ummu Barka da dare" ya fada yana dan kauda Kai ganin yarda suke kallon juna

Dariya sukayi gabadayansu ganin yadda ya wani kauda Kai "Yauwa babana ya aiki?" Dad ya tambayesa "Alhmdullilah" ya fada tareda da zama "Ya aikin" ummu ta tambaya tana mikewa Alhmdullilah ya Kara fada Yana sunkuyar da Kai " Toh kaci abinci?" Ummu ta Kara tambaya Girgiza kansa yayi "Toh taso muci Mana babana" dad ya fada, shagwabe fuska yayi tareda cewa kamar xaiyi kuka"ALLAH Abba bana jin Yunwa Hararsa ummu tayi " mekaci?" Shiru yayi baice komai bah dad yayi dariya tare da Girgiza Kai yacigaba dacin abincin shi bayan ya gama ummu ta kwashe tafita dashi dad Kuma ya goge bakinsa da napkin" Yauwa babana magana takaran Nan ne sunaso fa in fito president Kuma sai nake ganin kamar bazan iya bah" Amir yayi Dan murmushi " dad  nifa gani nake kana b'ata lokaci nee kawaii akan wannan maganar kuma banga abun tunani ba , kar ka manta ALLAH ba ya azama bawan sa abunda bazai iya bah Soo kawaii ka amshi offernsu" yafada kansa na kasa dad murmushi yakarayi Yana Kara jin son Dan nashi acikin zuciyarsa " Nagode d'ana ALLAH yayi Albarka, Amma ya maganar Offer inda aka baka na nan BUK Kuma kasan fah Autana tace Nan takeso"

HINDATUWhere stories live. Discover now