"Dan Allah mamana kiyi sauri ki tsince waken nan, abinda ba dati ne da shi ba, ni fa dadi na dake kenan nawa, har ruwan ya tafasa ya kone kina nan kina kal-kale wake". Matar da ke tsaye bakin kofar wani matsakai cin daki dake can gefen tsakar gidan ta fada, tana ci gaba da tafiya hanyar zaure rike da tsintsiya da abun kwashe shara , da gani dai kaga mahaifiyar matashiyar buduwar dake zaune kan kujerar tsakar gida ta karfe daga can daya gefen dauke da tray a kan cinyar ta tana tsince waken a nutse.
"A'a Aminatu, ki bita a hankali kinsan ta bata da garaje, a nutse take abubuwanta". Wata bafulatanar dattijiwa dake fitowa daga dakin da mahaifiyar budurwar ta fito ta fada tana tsaya wa a kofar dakin hade da gyara zanin ta.
"Inna tafi minti goma tana tsince wakenan kuma kanenta sun kusa tasowa daga makaranta, bana so su dawo da yunwa ba a gama dafa abincin nan ba inna". Ta fada cikin ladabi.
"Eh toh,da wannan -dan wannan, amma ba dan ba a sabo da yunwa ba sai ince waye bai saba zama da yunwa a gidan nan ba Aminatu?, kin sani sarai sai Ali ya fita ya nemo ake ci a gidan nan, to amma yanzu Allhamdullilah, tunda ba a fasa ci ba kuma ba a gaza wajen nemowa da kawowa ba".
"Eh, Allhamdullilah Inna".
"To kinga, dan haka abi min takwara a hankali, in sha Allah ba me zama da yunwa a cikin gidan nan". Inna ta fada tana komawa dakin da ta fito, wanda da gani mallakinta ne .
Mikewa ta yi daga zaunen ta nufi drum din ruwan dake tsakar gidan duk kalarsa ta kode saboda rana, da kyar ta samu wanda zata wanke waken saboda rashin ruwan, dawowa tayi ta nufi kitchen din dake tsakar gidan wanda aka kewaye da langa langa, sai da ta zuba waken kafin ta fifita charcoal din don kara saurin wutar .
"Ummah an tsince shinkafar?". Ta tambaya cikin sanyin murya wadda da gani haka halittar ta take.
"Ah, tun yaushe, ni mamana in nace zan daka ta taki ai baza mu dinga cin abincin rana a gidan nan ba sai bayan la'asar".
"Kai Ummah" ta fada tana murmishin jin kunya.
Haka Allah yayi ta bata da sauri a aiki, komai a nutse take yinsa, shi yasa indan ana bukatar aiki da gagawa ba'a saka ta saboda sai an gwanmace ba a bata aikin ba."Ummah, ba dunkule fah".
"Oh, kin ga kuwa na manta, gashi dashi za a daka yajin, bari yan makaranta su dawo, sai Uthman ya siyo a kanti(canteen/kiosk)".
"Tohm, Allah ya dawo dasu lafiya".
"Ameen".
~~~
"Assalamualaikum""Waalaikumusalam, yan makaranta an taso kenan". Ummah ta fada tana murmushin ganin autanta ya dawo daga makaranta.
"Eh Ummana, sannu da aiki, ina yini?"
"Yauwa sannu yaron kir-ki, ya karatu?"
"Allhamdullilah Ummah, ina Aunty?"
"Tana dakin Inna". Kafin ta karasa ya nufi dakin da gudu yana kwala musu kira.
"Aa akarambana an dawo, sannun ka, kazo damun Aunty da surutun ka ko?". Inna ta fada tana kafe shi da ido .
"Kai Inna, nifa bani da magana, kawai dai ina tambayar abinda ban sani bane, kuma malamin mu yace duk abin da mutum bai sani kar yayi shiru, ya tambayi elders din sa".
"To radio, me wani edas ko me ne ka ce a karshe?" Inna ta tambaya tana gyara zama.
Sai da yayi dariya son ransa kana ya bata amsa da
"Haba Inna, kar ki bada mu mana"."Kai ni ban iya yaren yahudun nan ba da ma dai Arabiyya ce, sai in ce ina da sani anan fanin".
"Ayyah Innar mu , to Aunty ta dinga koya miki mana , amma sai kin fara iya Alphabets tukkuna, kafin ki iya kalmomi".
YOU ARE READING
Baya wuya...
SpiritualDama a zamanin nan na yanzu akawai abinda zai hana matashi mai jini a jika da ji da ilimi,arziki, isa da Iko uwa uba kyawun Hali da hallita rashin macen aure? To haka take ga Muhammad Muhamoud Maitama, kyayawan matashi wanda ya tara komai na duniya...