BABI NA DAYA

70 7 15
                                    




Assalamualaikum,




Ina mika dumbin godiya ga dukkan wanda ya bawa wannan littafi nawa lokacinsa❤️

Wannan shine karo na farko da zan rubuta littafi da harshen Hausa, wanda nake fata zai amfani duk wanda ya karanta kuma ina fata na isar da sakon da nake son isarwa.

Ina fata zaku bani goyon baya.


Bazan fara ba ba tare da mika godiya ta ga dukkan kawayena wanda muke tamkar yanuwa, nagode sosai da kwarin guiwar da kuke bani ❤️, Allah ya bar zumunci.

Sabrispen Thank you for the endless support Habibty ❤️

Maymunatu_Bukar  Ina mika godiya ta mussaman da taimakon ki wannan littafi yake existing yau, Thank you ❤️


















   ~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA, MAI JIN KAI~






Motocine manya manya na alfarma guda uku, ta farko kirar Range Rover ta biyu Mercedes Benz sai ta karshe kirar Hilux tare suka tafiya a jere convoy, driver na farko ne yayi honk a kofar wani makeken gidan Alhaji Muhammad Maitama mai dauke da katon gate mai kalar gold, daya bayan daya suka fara shiga cikin gidan bayan mai gadi ya bude gate din, a parking lot suka yi parking motocin kafin mata guda takwas suka fito daga motocin guda biyu dukansu da shiga ta alfarma, wata fara a cikinsu ce tayi magana "Saminu a sauko da kayan a biyo mu dasu ciki". Ta fada fasakarta ba yabo ba fallasa Lamar ta sauran matan.  Sun danyi tafiya kadan kafin suka karasa kofar baban parlour gidan.
"Assalamualaikum". Suka fada a tare suna shiga cikin haddeden parlour dake dauke da manyan kujeru kirar Royal chairs, parlour ya hadu iya haduwa , yasha kayan gayu na aji ba hayaniya daganin parkour naira ta yi kuka, wanan gida shi ake Kira da Mansion.  Farar mata ce wadda bazata wuce shekara arba'in da biyar zuwa da takwas ba, kana ganin ta kasan gayu ya ratsa ta, tayi kwalliya ta alfarma da aji.
"Aa Fati, sanunku da zuwa".Ta fada fuskarta dauke da murmushi wanda ke bayyana hakwaranta farere tas sai guda daya na makka dake kaylli kamar lokacin aka sa . Murmushin ta ne ya dauke kamar an dauke ruwan sama lokacin da taga ana shigo da anwatunan lefen da aka fita dasu awani biyu da suka wuce.

"Fati me ya faru naga ana shigo da kaya ?" Ta tambaya fuskarta cike da mamaki .

Ba wanda ya amsa mata tambayarta har se da suka zauna sanan, wadda aka kira da Fati tace " Yaya ki zauna zan miki bayani anjima.

"Wani irin anjima, ki fada mun mesa kuka dawo da kayan".

Ajiyar zuciya ta yi bayan su Saminu da Maigadi sun gama shigo da anwatunan guda ashirin da hudu sun koma bakin aikinsu sannan tace.

"Aunty sunce bazasu bawa yarsu Saheer ba dadin dadawa kuma basu ji dadin boye musu matsalar Saheer da kukayi ba, to dan haka sun gano kuma yar su bazata hada jini da gidannan ba.

"Inallilahi wa ina illaihirraji'un , Allahuma Ajirni fil musibati wa akliqni khairan min ha, yanzu Fati da wani idon zan kali yaron nan da mahaifinsa in fara musu bayani? Na yarda da Hajiya Rufaidah da amintar da ke tsakinina da ita dadin dadawa yarta da na yaba da hankalita da kuma imani da cewar zata iya zame wa Saheer matar rufun asiri."Hajiya Maraqissiya kenan ta inda take shiga bata nan take fita ba tsanin rikicewa da tashin hankali.

"Aunty Mara hakuri za muyi, haka Allah ya tsarawa rayuwar Yarona , tashi kaddarar kenan, in ba haka ba Saheer me yarasa a duniya ?, mu cigaba da addu'a mu fawalawa Allah InshaAllah watarana sai labari."

"Ai dama sai dai a yi hakurin, Aure dai ayi ma gani" Hajiya Hadiza ta fada hade da tashi daga kujerar da take kai ta nufi kofar palour tana cewa "Sai anjima sai wani jikon".

Baya wuya...Where stories live. Discover now