EPISODE ONE

75 5 3
                                    

*BABAN DOCTOR*

*WANNAN LITTAFIN GABA DAYAN SHI SADAUKARWA NE GARE KI LATE RUKAIYAH ABDULLAHI,INA MATUKAR KEWARKI KAWATA ALLAAH YA JIKAN KI DA RAHAMA*

*GAJERAN LABARI MAI DAUKE DA ABIN AL'AJABI*

*DAGA ALƙALAMIN ANTYN BEAUTY*

*SHAFIN FARKO*

                 *MAFARIN LAMARIN SHA TAKWAS GA WATAN TARA SHEKARAR DUBU BIYU DA SHAUKU*
*unguwar mu'azu giwa road*

ahankali nike tafiya kasancewar ina tafiya cikin nutsuwa babu wanda zai ce cikin sauri nike, shanyo kwanar gidan mu keda wuya na haɗu da ƙawata maryam smolly, kasancewar duk tafi mu ƙanƙanta cikin ɗabiban da muka zo (teaching practice) yasa muke kiranta da maryam smolly.

Miƙa mata hannu nayi mukayi sallama sannan muka ci gaba da tafiya babu  koh hira atsakanin mu har muka iso makarantar da muke koyarwa ma'ahad Aisha wa Umar Ash shammar, gaishe da shugaban makarantar mu kayi sannan mu kayi signing tukunna kowwa ya kama kansa,

Shiga na aji keda wuya sai ga ƙawata mai suna Rukaiyah, ahankali na ɗaga mata hannu sama alamun ta ƙaleni lokacin karatunne gashi yara har sun fara muraja'a, bata cemin komi ba ta wuce nata ajin itama,

Nayi nisa cikin karatu sai ga ɗaya daga cikin abokan koyarwa na kuma wanda nike ma laƙabi da abokina wato El-bashir,

Miƙomin parket ɗin lolly pop yay da sweat sannan nai masa godiya ina haɗashi da allaah kar ya ara siyomin saboda hidimar tayi yawa.

Kallona yay cike da kulawa ranshi aɓace ya ɗago yace.

"bana son godiyarki ki riƙe kuma wlh da rana saina kawo miki wani matsa ki bani waje in shige",
matsa mishi nayi kasancewar naga kamar yay fishi shiyasa ban ƙara masa magana ba na ci gaba da karatuna cikin siririyar muryata da mutane krɗemin laƙabi da iyayi ne da tsabar girman kai.

Seda na gama ƙara musu alku'ani mai girma sannan muka ɗauko sauran durussan mu kayi,

Duk da ina da ƙanƙanta ajiki amman ina da cika ido shiyasa cikin yaran babu wanda ya raina ni duk abinda na umarcesu suyi shi su keyi, sannan in mutum yay min taurin kai in haɗasa da el-bashir awuce wajen.

*Karfe sha ɗaya*

sha ɗaya da rabi dai dai muke, signin book na ɗauka nayi sannan na ba Rukaiyah tayi tukum mu kayi sallama da abokan aikin mu,

Tafiya mu keyi mun ɗanyi nisa sannan Ta dubeni tace "wai Rukaiyah ya maganar baban doctor ne?"

cike da tsananin tsanar da nike masa na ɗago na zuba mata ido wanda suka fara kawo ruwa nace.....,

*Comments and vote plss*

BABAN DOCTORWhere stories live. Discover now