❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*BABAN DOCTOR*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*DAGA ALKALAMIN*
_REAL ANTYN BEAUTY_
*(ROUKY LOLLYPOP)*
*DEDICATED TO ROUKAIYYERH ABDULLERHEE MAY YOUR GENTLE SOUL CONTINUE REST IN PERFECT PEACE,MAY JERNNERTUL FIRDERUS CONTINUE TO BE UR FINAL ABODE(AMIIN)*
*PAGE4*
_Not edited_
_Bayan kwana biyu_
Yau ma kamar kullum na bumbulu hijabina zani makaranta, ahanya na hadu da el_bashi kallona yay sannan yace "gimbiya har kin fito? "
Cikin iyayi na kalleshi sannan nace "eh na fito mine, Antashi lafiya ya gida ya mama yasu fa'iza",
Dariya sosae yay sannan yace "my lollypop duk wannan tambayar ni zan amsata? Gaskiya tai min yawa amman dai bari na amsa ataikace, duk suna lafiya ya gajiyar mu", harararshi nayi sannan nace "gajiya ta bi jiki," haka muka ci gaba da tafiya har muka iso kofar makarantar sannan na mika masa biro hadi da fadin "mine dan Allaah kayi mun signing", da yake el_bashir irin mutanen nan masu hand writting, in yay rubutu koh yay signing kamar computer ce tayi shiyasa nikeson ya dingai min rubutu,
Hararar ya watsa min sannan yace "wlh bazan ba, koh kina son wancen dan rainin sense din ya samin idone, kar ki manta ranar da ya kamani nai miki signing harda kiran Al_mugamgam yay ya fada masa," ya idashe maganar yana murmushi keta,
Fisge biron nayi daga hannunshi sannan nace "naji din kar kayi, kuma karda ka kara min magana, ka wuce ka bani waje inyi signing", na idashe maganar da bacin rai saboda ina da saurin hasala ba laifi,Juyawa yay har ya fara tafiya sannan ya dawo da baya hadi da karban biron ahannuna tukum yay min sannan ya kama kasan hijabina da yake malala akasa muka tafi,
Muna shiga cikin makaranta abokan koyar warmu suka fara tafi wasu daga cikinsu na fadin "A'a kaga love bird mijin hajiya Rouky, "
Wani daga cikin yan ajinmu da mike wasa da dariya ne ya taho da camerarshi a rataye awuya ya fara kashe mana pics mu kuma muna bada style masu kyau,
Seda ya gama sannan na mika ma el_bashir jakata nace "ka koyar min dan Allaah ni yau ina tare da sweat dan ajinta zani akwai muhinmin abinda zamu tattauna da ita",Karban jakar tawa yay, sannan ya miko packet din lollypop da sweat da chocolate tukum ya daura hannunshi abakin shi alamar inyi shiru kawai besan godiya,
Idona ne suka ciko da hawaye sosai kamar zasu zubda ruwa na dago na kalleshi sannan nace "haba mine duk wadan nan abubuwan ya kake son nayi dasu, dan Allaah karka kawo min next week ka barshi wannan zai kai min karshen wata ma", na kare maganar ina dunkule hannayena,
Daga kanshi yay alamar naji bawai dan ya aminta da zancena ba, sai dan kawai beson ja in ja dani,_TUNA BAYA_
watanni ukku da suka wuce, duk sanda zani makaranta na kan tsaya kan hanya in saya lollypop da sweat da cincin din ledar da ceesy kasan cewata mai mugun son kayan zaki, kasan cewar ina ciwon mara mai tsananin gaske shiyasa aka hana ni shan duk wani abu mai zaki ko zansha sesa² nike sha saboda na kasance mai son tsaki, koh sugar na shiga dakin granny na gani haka nike hadata da madara da bornvita inta zuba ma cikina ba tare da na ci wani abuba sabida bansan cin abinci da yawa kullum sai anyi fama dani kafin naci, amman in wajen sha zakine da kayan fruits har sayo min Abbana yake ya ajiye inna ci abinci koh yayane sai ya bani inta fama inaci, ina da mugun kwadayin madara dan bani manta ranar da hakorina ya fita guda daya saboda na ciko bakina da madara, madarar ma sabota nayi dakin granny ba tada labari, wannan dalilin ne yasa da yawa daga cikin yan ajin mu suke kiran mu sweat da lollypop,
Wata rana muna labari da el_bashir cikin wasa nace dan Allaah yau in zaka zo makaranta ka siyo min lollypop, maganar gaskiya ni awasa na masa amman da yamma sai gashi da packet din lollypop ya kawo min, miko min yay naqi karba ina tambayarshi lafiya dukka wannan na waye.
Ajiye mun yay akasa ya wuce ba yadda zanyi dole na dauka na shiga dashi cikin gida zuciyata babu dadi saboda ina tunanin zai ce koh na rukesa,********************************************
*waye baban doctor*Baban doctor dan asalin jihar gombe ne, karatune ya kawosa kaduna nan zuka hadu da yaya Abbas kasancewar makaranta daya su keyi dashi anan makarfi, tsakani ga Allaah tun haduwa ta da baban doctor na tsaneshi lokacin munje tayasu murnar gama karatunsu, bayan wani lokaci kuma an dauki shekaru lokacin har yay aure da yaranshi daya mai suna bashir amman suna kiranshi da doctor sukazo kaduna, tunda matarshi mai suna zainab ta kyalla ido akaina ta saka min karan tsana, wannan dalilin ne yasa na kara tsanarshi cikin zuciya, duk haduwar da zamuyi dashi ban taba gaishe shi ba, sai ma shi wata rana in ya ganni ya kance min ina yini in amsa da lafiya kawai in wuce, ranar da baban doctor ya furta ma yaya Abbas yana sona kuma shi da gaske yake zai turo iyayensa kwana nayi ina jefa masa yasin da addu'ar Allaah ya tsine masa, kamar wasa magana tafara nisa cikin gidan mu sai gashi cikin kankanin lokaci kowwa ya sanda baban doctor wanda ni ban daukesa wani abu ba, duk satin duniyar nan sai yazo week end gidan mu, dana fahimci hakan sai na tartara kayana na koma rigasa na ci gaba da zuwa makaranta na, da farko ummana ba ta yarda ba, amman dana kafe dole aka samu mai kaini school ya dauko ni,
Da baban doctor ya fahimci guje masa nike kawai sai ya samu Abbana su kayi magana akace ya turo iyayensa, cikin satin iyayensa suka iso kaduna tare da kudin aurena, innalilahi wa inna ilaihirrajiun tashin hankalin da ba'a sa masa rana sai dai ya sama kansa, va karamin rudu na shiga ba shikenan za'a kaini abaro karatuna ya koma baya kenan, duk iya yina dan inga na hana auren amman hakan ya faskara shiyasa nayi hakuri na fawwala ma Allaah komi amman ina nan araina na kullacesa kuma nayi alkawarin bazai taba samun kwanciyar hankali daga gareni ba, wannan shine,*********************************************
Ajin sweat na wuce can muka kafa dan dalin hira kowa na kawo nasa labarin, nikam shiru nayi tunanin duniya ya isheni, yau aurena da baban doctor ya rage saura wata biyu cif, ranar da zanyi murnar kammala tp na ranar za'a daura min aure, duk abinda sauran kawayenmu ke fadi ni ban saka baki ba, sai ma dokar da kaina nayi kasa ji nike yana sara min kamar zai tsage gida biyu,
Ina nan zaune na shafa'a ashe lokaci ya wuce har an tashi sai abokaina dake jirana mu tmjera tare, sweat ce ta sa hannu da zungurenu hadi da fadin "haba Rouky lafiyanki da wannan tunanin? "
"Uhm sweat babu komi muje koh", nace da ita dan kawai ta gyaleni, ita ma bata cemin komi ba muka kama hanyar fita cikin makaranta,Tafiya muke babu hira tsakanin mu har muka zo wajen da muke rabowa muka rabe ta hanyar mika ma junanmu hannuwa mu kayi sallama, ta tafi nima na tafi,
Tun daga nesa na hango cincirundun mutane sun hallara inda suke zama cikinsu harda baban doctor..................
_dont forget to follow me on wattpad roukylollypop pls_
*REALANTYNBEAUTY*📝
![](https://img.wattpad.com/cover/257821035-288-k614846.jpg)