EPISODE TWO

57 4 1
                                    

BABAN DOCTOR

SADAUKARWA GA LATE RUKAIYAH ABDULLAHI CONTINUE REST IN PERFECT PEACE.

ɗagowa nayi na zuba mata ido ina faɗin "haba sweat dan girman allah ki dena min maganar baban doctor wlh bana so,"

Cike da wulaƙanci ta kallan sannan tace "wlh ki guji duniya ki so mai sonki idan rana ta fito baki san lokacin faɗuwarta ba karki bi ruɗin duniya ina ƙara tunashsheki",

dafa kafaɗunta nayi da dukka hannayena ya zama kamar ina fuskantar ta, ɗan murza kafaɗunta nayi da hannayensa saboda haka nike duk lokacin da raina ya ɓaci sai nayi hakan nike jin daɗi, "haba sweat kinsan komi kinsan yadda na tsani ganin baban doctor sweat har sai yaushe zan fara ganin dai dai arayuwata kin fina sanin komi, ana son laƙamin auren da natsana na gwammaci mutuwa akansa,"

Na idashe maganar ina kuka kamar wata aramar yarinya,

Jan hannuna sweat tayi takaini dakalin gidan hajiya abu ta zaunar dani sannan ta ɗago ta zuba min ido,

Cikin sanyinta da sanyi hali irin nata tace "wlh swaet kiyi ma iyayenki biyayya karki bijire musu sweat ki duba ki gani, gobenki ce abin ji ba yau ba, kinga yau kuma ta wuce miki", ta idashe maganar tana bubbaga kafaɗuna.

Bance mata komi ba na miƙe saboda ta fara hasalani cikin faɗa faɗa nace mata "in zaki taho mu tafi tau in kuma zama zakiyi ki bari har sarkin zama ya sameki",  na faɗa cikin sauri ina tafiya.

Biyo bayana tayi da saurinta muka ci gaba da tafiya ba tare dana ƙara kulata ba saboda ina kallon mata duk bakinsu ɗaya da ƴan gidan mu,


Muna shanyo kwanar gidan mu na hangi baban doctor shida yaya Abbas sun zauna zaman jirana, gabana ne yay mummunar faɗi jikina ya hau kyarma saboda tsakani ga allaah na tsani ganinsa, duk lokacin dana gansa nikan ji babu daɗi harna rasa mai kemin daɗi, ahankali na zunguri sweat nace "kinga matsiyacin can ya zauna zaman hasara marar imani kawai,"  na faɗa ina goge hawayen idona,

Fincike hijabinta tayi tana faɗin "sai allaah ya kaimu da rana ni tacan zanbi" ta faɗa tana nuna wani lungu, azahirin gaskiya ba bin lungun takeyi ba kawai dan ta ƙonamin raine.

Yaya Abbas kallona yay daga nesa yana ɗaga min hannu alamar inzo, jikina na rawa na fara tafiya, ina ƙin zuwa kuma na jama kaina doka, bemun da wasa koh kaɗan inya fara dukana kamar ya samu jaka haka yake min, kuma ba kowwa bane ya sashi illa mamana,

Haka na tafi jikina asanyaye, tsayawa nayi daga ɗan nesa kaɗan dashi cikin rawar murya nace "ya... yanmu gani",
seda ya gama abinda ya keyi dan nakai 10mins atsaye ga idanun baban doctor dake yawo asassan jikina,

Kallona yay sannan yace "baki iya gaisuwa bane"?

cike da ɓacin rai nace "ina kwana yayanmu",
Kallona yay yace "dan ubanki ni kaɗai kika gani?"

dakewa nayi nai kamar banji abinda yace ba,

Cikin sanyayyar muryarshi ya ɗago ya zuba min dara daran idonshi, kyakyawar fuskarshi na kalla wanda nike ganinta kamar baƙin gawayi saboda tsanar da na mishi amman a zahirin gaskiya baban doctor kyakyawane naƙin ƙarawa saboda koh kusa bazan iya haɗa kyauna dashi ba,
Kasancewarshi fulanin usul ni kuma kanur.

"Haba yayan mu kasan lokacin da muka gaisa da ita nidae ka kyaleta dan allaah", ya faɗa yana miƙewa tsaye ga dukkan akamu tafiya zeyi,

Harara yaya Abbas ya zabga min sannan yace "baza ki gaishe shi ba?"

dake idon yaya abbas akan waya yake shiyasa na fakaice shi na zabga aguje na shige cikin gida..,

*Wannan labarin kai tsaye zaku same shi awattpad*

*kuyi follow ɗina roukylollypop dan samun cikakken labarin*

*yanzu mun koma school baza kuna samun update kullum ba se in ina da time*

*Comments and vote share pls*

BABAN DOCTORWhere stories live. Discover now