29&30

852 27 0
                                    

29&30_


"My Ammar har kashirya ne fita ne?''
Kallon ta yayi cikin wata zazzafar k'aunar da yakeji rungume ta jikinsa yayi
"Eh zan tafi muna da wasu bak'i ne kuma dole sai sun ganni sannan."
Kuma Mommy kasan jirgin da zata tafi Around 8:30 zasu tashi fa kuma yau na tashi jikina ba dad'i bazan iya tuki ba ya za'ayi ne?"

"My Fee duk yadda kikeso hakan zanyi indai ranki zai farantu da hakan kinsan bana son b'acin ranki."

"So nake muje kaje mommy airport sai ka maido ni gida sannan sai ka wuce office d'in."

Ammar kallon Feenah yayi "My Fee bakiji yadda nace ba bak'i gareni fa Around 8 kiyi hak'uri please zan turo driver mu na office ya kaiku pls my Fee."

Dak'atar dashi tayi da hannu cikin b'acin rai
"Kaga kayi tafiyar ka basai ka kawo man wata magana Mommyn tawa ce bazaka iya kaiwa kawuce kayi tafiyar ka office banason jin komai."
dasauri Ammar ya tari Feenah dake shirin barin waje "haba My fee pls kiyi hak'uri kinji bari na kai Mommy d'in sannan na tafi."
Feena kallon Ammar tayi batayi magana ba.
"My Fee ki saki ranki mana ko hankalin Ammar ya kwanta."
dariya tayi "shikenan Amma kason ban cika son nayi magana ba kayi man gardama."

"shikenan Angama My ♕ queen."
"Fee ko ruwan tea ban samu ba? Kafin na fita office.?"
''Babu nima mommy ta had'a min nasha.".
"Ok ina Fita office nasamu."

"Ok bari naje naga Mommy ta idar da shiryawa."
D'akin da Mommy ta sauka ta nufa iske Mommy tayi tana saka sark'a a wuyan ta.

"My Mommy zanyi kewar ki sosai."
''My daughter karki damu bazan dinga call d'inki zan tafi ne dadynki ya kirani gobe zasu dawo shida wannan makirar matar tashi.

(Alhaji taheer yak'ara aure inda d'iyar k'anwar innace ya aura ansha daru kafin anyi auren inda inna ta dage da Add'ua akayi auren inda yanzu suna yayan uku tare maza biyu mace d'aya rabi'atu matar da ya aura mace ce mai kirki da son Addini tana dage yi ma mijinta addu'a dare da rana)

"Mommy ni banga Abinda Aunty rab'iatu ke maki kika tsane ta tana girmamaki fa."

"Daughter kenan bazaki tab'a ganewa ba ko duk wannan duk munafurci da kissa irin nata."

"Mommy ga Ammar can fa zai kaiki airport."
"Ok"
d'aukar hand bag d'inta tayi tare cewa "ina kika baro Ammar d'in?"
Yana palour."
''Ok abinda zan fad'a miki kinga komai ya canza ne?"
"Mommy nagani sosai bakiga gani ba yanzu yadda yake man da raina ya b'aci."
"Shikenan baby sai munyi waya."
Haka suka fito jere sai kace wasu k'awaye doguwar riga ce jikinta bak'a gyala gyalen tayi suka fito Ammar yana jingine da k'ujera yana ganin su ya mik'e."

"Mommy har kin fito."
"Eh Ammar zanj tafi gobe Dadyn Baby zai dawo ne."
"Ok Muje."
Feena kallon Ammar tayi bangane ba Ammar wazai rik'e wad'ad'anan kayane na hannu mommy ni zan rik'e ko ita kasan dai ba lafiya gareni ba babynka yana tak'ura man."

Ammar cikin kyarma ya amshi Hand bag d'in
Yafito.
Mommy kallon y'ar ta tayi yadda ta fara zuba mulki tun yanzu.
"Daughter kirage ma yi mashi hakan. Mana."
"Mommy ni kad'ai nasan wahalar da Ya bani inason Ammar har cikin raina kema kinsani Mommy ina tuno abinda yayi man ne nake mishi."

"Daughter kenan."
Haka suka fito Feenah ta kwantar da kanta bisa kafad'ar Mommy.
Ammar dama ya bud'e musu bayan mota mommy ta shiga sannan Feenah ta shiga Ammar kallon ta yayi
"My fee ki dawo gaba mana."

"Anan nake son zama ka rufe murfin mota muje time yana tafiya."
Ammar yaji ciwo cikin ranshi yau shi aka maida driver Amma ya rasa Abinda ke damunsa bazai iya yima Feena gardama ba.

Haka ya rufe murfin mota suka nufi airport.

Wajen parking d'in motoci Ammar ya nufa yayi Feenah hana Mommy ta bud'e murfin motar tayi

"Waka aje ne dasai bud'e mana murfin ne?''

Ammar murfin ya bud'e suka fito maidawa yayi ya rufe cikin sigar Alamun rarrashi ya kalli Feena
"Please my Feena kinga na fara samun kiran daga Office kiyi hak'uri naje sai nasa driver office ya mai daki gida."

Wani mugun kallon ta watsa mishi.
"Wallahi babu inda zaga sai jirgin su Momy ya tashi kamaidani gida sannan in kuma office d'in ya fini Muhimmaci kawuce katafi."

Juyawa tayi ta koma kusa da Momyn ta
Ammar komawa yayi ya jingina da mota yana jin wani b'acin rai, Amms babu damar yayi magana domin shakkar Feenah yake sosai.

A haka aka fara kiran sunan har akazo wajen Mommy, Momyn Feena k'ara bata wasu shawarwari tayi tare da fad'in sai sunyi waya a hakan suka rabu tana d'aga mata hannu

Jikin Ammar ta kwanta ta shagwab'a "my Ammar nayi kewar Momyna kamar na bita mutafi tare nakeji."

"Kiyi hak'uri zamuje kinji My Feena."
Haka suka shiga mota
"My Ammar inajin yunwa mu biya restaurant inason pizza 🍕 ne "

Ammar kallon ta yayi babu yadda zaiyi domin yana matuk'ar gudun b'acin ran Feenah.

Saida aka shafe 10 minutes sannan aka basu sannan ya nufo da ita gida nan ma sai da b'ata mishi lokaci bai isa office ba sai a round 9 har bak'in sun fara shirin tafiya don ma ya rarrashesu sosai sannan suka hak'ura sannan suka fara meeting d'in.

★ ☆

A hankali ta bud'e idon ta daga baccin gajiyar da tayi domin basu iso kano ba sai cikin dare mik'a tayi tare da addu'ar tashi daga bacci kallon Laure tayi dake ta sharar baccin ta bisa gadon da suke kallon d'akin tayi tsaftace yake sai tashin k'amshi yake komai tsaf gado ne sai mirror ciki sai wadrope

tashin Laure ta farayi
"Laure! Laure!! "
Bud'a idon ta tafarayi a can kuma ta mik'e tana mintsinar ido
"Dije har safiya tayi ne?"

"Eh mana bakiga har rana ma tafito fa.''

"Wallahi Dije naji dad'in bacci shiyasa kai binni akwai dadi sosai."
Dije kallon ta tayi tare tab'e baki
"Har dad'in binni kikeji nikam nafijin dad'in k'auye mu Allah sarki habu ko yanzu wane hali yake."
Dasauri Laure ta rufe mata baki.

"Dije ki manta da auren wani bisa kanki kuma kinsa babu kyau ki Ambato wani namiji da sunan soyaya haramu ne."

"Astagafurallah! Allah na tuba."
Goge hawayen da suka fara zubo mata tayi
Tasowa tayi daga bisa gado
"To laure ina band'aki ne?''
''Dije nima bansani shi ba gashi dama fitsari nakeji saura kad'an nayi na kwance."
Dije dariya tayi kai Laure Allah kin cika shishirita fitsarin kwance fa sai kace wata y'ar k'aramar yariyanya."

"Allah kuwa.."
Suna cikin wannan maganar turo k'ofar akayi aka shigo dasauri suka maida idanuwansu ga mai shigowa..

Cikin far'aa tayi sallama
Amsa mata sukayi.

"Har kun farka ne?"
Laure kallon ta tayi
"Eh Aunty fateema."
"Ai nashigo naga kuna ta sharar bacci Mamy tace a kyaleku."

Duk maganar kan dije yana k'asa bata d'ago ba hannun Fateema taji.
"Auntyn mu Amaryamu An tashi lafiya."
Dije rufe Fuskar ta tayi cikin kunya.

"Shikenan tunda kunya kukeji ku shirya ku fito."
Aunty Fateema bansan ina kewayen ba."

"Kai Laure Kodayeke bazanyi mamaki tunda baki tab'a zuwa wannan sabon gidan ba tunda muka dawo."

Kama hannu laure tayi ta nuna mata band'aki dake cikin d'akin

"Aunty fateema ai bamu san yadda zamuyi Amfani dashi ba."

Dariya tayi tare da nuna mata duk wannan Abun da ake Dije na gefe d'aya babu abinda tace
Bayan laure ta gwada ma laure tafito gun dije ta nufa dije hannu taji bisa kafad'ar ta....

📚✍🏻

MATA KO BAIWAWhere stories live. Discover now