3&4

1.2K 36 0
                                    

🔷 *_MATA KO BAIWA ???🔷_*

_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_

_*BY HAFSY BABY*_
( _*INDON KAUYE*_)

*_Masoyana

*3&4*

Nufar inda take tayi tare da hawa bisa ruwan cikinta "don kutumar ubanki wannan yayi miki kama da colour d'inki da har zaki ce kina buk'atar phone number d'inshi zata kai mata wani naushi taji an rik'eta

D'ago Fuska tayi ta ganshi fad'awa tayi jikin shi tare da fashewa tayi da kuka tak'ara shigewa jikin sa kama ta yayi kawai sukaje suka biya kud'in abinci da suka ci wadda ko 3 spoon ba suyi ba

Shiga mota sukayi batayi magana har suka isa ko kallon shi bata yi mai gadi yana bud'e musu ko gyara parking bai yi ba ta bud'a ta fita dasauri har mayafin ta ya fad'i Amma bata bi ta kanshi ba

Girgiza kai yayi sannan ya gyara parking ya fito ya d'auko mata mayafin ya nufi ciki d'akin ta ya nufa turus! Yayi ganin tasa ma k'ofar key!

"Feena!"
Amma shiru bata bud'e k'ofar ba
''Feena kinajin ina yi maki magana zaki shareni ko."

"Ka koma restaurant ka d'auki budurwarka zata saurereka."

"Feena yarinyar da ban tsaya saurere ba zaki ce natafi gunta."

"Eh ai da baka bata Fuska ba bazata zauna kusa dakai ba ko."

"Shikenan kiyi hak'uri yanzu ki bud'eman k'ofar kinji my honey Feena."
Rarrashin ta ya farayi tasowar ta yaji ta bud'e k'ofar turawa k'ofar yayi ya kalleta ta koma bisa gado tayi kwance.
Nufar inda take yayi

"Haba! My Feena meye na Fushi nifa kwatata banga zamanta ba kusadani sai naji maganar kuma nifa banyi mata magana ba wallahi Haba Honey ta ya kamata kiyardani mana.

Kallon shi tayi can kuma ta kauda Fuska
"Nasan ko ka canza ne daga yadda nasanka ne."
.
"Bazan tab'a canzawa ba My Feena ke kad'aice matata kuma wadda zan kula Har abada nayi miki Alk'awarin haka fa."

Murmushi tayi tare da matsowa kusa dashi.
"Naji dad'in haka daga gareka My Ammar Domin ina maka wani kishi wadda bazan iya misalta maka shi ba Ammar duk mace da tayi k'okarin shigowa gida nan da sunan matar ka wallahi zan iya halakata domin kai _*MIJIN MACE D'AYA*_ ne"

Ammar zaro ido yayi jin ta Ambaci kalmar kisa
"Feena Kisa fa kika ce?''

"Kwarai kuwa Ammar zan iya kashe ko wacece saboda bazan iya kallon ka da wata mace ba da sunan matar ka face ni domin kai mijin mace d'aya ne in ko har kace zaka k'okarin shigo da wata to tafo da likkafani ta..."

Ammar cike da mamaki yake bin Feena da kallo yadda wannna Furucin

"Ni naki ke d'aya My Feena.".....

*** **** ****

"Baffah sannu da dawowa."

"Yauwa Dije."
Karb'ar ledar dake Hannunshi tayi
"Baffah kawo na rike maka ledar."

Dariya yayi
"Dije wayo zakiyi dai kiji ledar kice to ban manta ledar tsarabar kice."

Dariya tayi tare da rufe Fuskar ta
"Baffah na nagode Allah yak'ara bud'i ya rufa asiri."
"Ameen Dijen Baffah."..

"Baffah bari nakai d'aki sai gama sallahr marigaba sai naci."..

"Shikenan Dije bari nima bani butar nayi sallah."......

"To Baffah".
Gun aje ruwa ta nufa ta d'ebo ta bashi yayi Alwallah ya fita itama itada Inna d'aura sallar magribar sukayi suka shiga d'aki...sukayi tasu

Bayan Baffah ya dawo ne Dije tana kusa da Baffah yana cin Abinci gyad'a kai yayi
"Wannan abinci dakajinsa Dije tayi sa domin naji d'and'an nasa yayi yawa fa.

"Haba! Malam kodai jagwalolo domin dai kasan wannan girkin nawa ne shine zaka ce na Dije ne"

Dije kallon Inna tayi tare zumb'oro baki
"Inna ninayi Miya fa Baffah Miyar tayi dadi sosai ko?"
."sosaima Dije taji maggi sosai kamar kunne na ya cire fa."
Dariya Dije tayi daga ita har inna Har Baffa ya kamallah cin Tuwon shi
"Baffa na mik'o ma furar kasha?"
"Aaa Dije kar cikina ya fashe sai zuwa anjima ko.."

"To Baffah."

Bayan Anjima kadan Baffah ya dawo daga sallar isha'i ne suna zaune sallamar wani yaro ta katse maganar da suke

"Ilu shigo mana meyafaru ne?''
Dama Habu ne kike kira Dije waje."
Dije Gaban ta yayi mumunar fad'uwa domin hakan bata tab'a Faruwa gare ta ba gakuma taga yanayi Fuskar sa ta canza
"Jeka cemashi gatanan."
Juyowa yayi wajen Dije.
"Dije dama bakya jin magana ta ne? Meke tsakaninki da Habu?"
"Baffah.. dama ..."
Kwatsa mata tsawa yayi wadda bata tab'a jin daga gareshi ba."
"Amma bazaga laifin ki ba har da mahaifiyar ki domin na fad'a mata hakan Amma kukayi hakan ban isa daku bane..."

"Malam karkace haka.."
Dakatar da ita yayi tare mik'ewa yafito Habu yana jingine yana jiran Fitowar Dije kawai yaga Baffa durkusawa yayi har k'asa ya gaida Baffah cikin Fara'a ya amsa sannan ya mik'e Baffah jan shi gefe d'aya yayi sukay magana gumi ya k'eto ma Habu Sharewa yayi Har suka gama magana da Baffa ya shiga ciki Dije tana rakub'e tana ganin shigowar Baffah ta mik'e
"Kije waje."
Cikin sanyi jiki ta mik'e ta fito Habu yana tsaye har ta iso
"Habu"
D'ago idon shi yayi ya kalleta cikin Fushi ya fara magana "Dije kin cuce ni kin yaudareni kinsan Kina da miji a hannu shine kika b'oye man Kinsan d'an birni zaki aura kika maidani wawa."..
"Habu bangane maganar ka har yanzu wayace maka inada miji kuma d'an binni zan aura?"
''Baffah ya sanar dani ya bada aurenki Ammar jikan mai gari.."..

Dije zaro ido tayi tafara tafiya da baya dasauri ta shige gida gaban baffah ta ganta sai hawaye shar!!!!!

MATA KO BAIWAWhere stories live. Discover now