Page 30

175 24 2
                                    

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 30
Da sauri na mike ina kallon shi, sabida tambayar shi yazo min bazata, yadda yake min abu kamar wanda ya sha giya ya sani yin baya, biyo Ni yake fuskar shi tayi jajjur, dan bakin shi ruwan pink sai wani rawa yake, a hankali ya kai ni bango tare da dafe hannun shi daya da bangon, yana kallon fuskana wanda ya ke cike da mamaki.

"Ki gaya min waye Allah?" Cikin rawan murya yake maganar. Jan hancin shi yayi tare da cewa.
"Ba zaki gaya min bane?"
Ya kuma tambaya na, kasa nayi da kaina, tare da cewa.
"Allah shine wanda ya halicci samman da kassai, babu abin bautawa da gaskiya sai shi. Shine wanda ya halicci Annabi Adam ya samar da Nana Hauwa'u daga jikin shi. Ubangiji shi ya halarci kome a cikin kwana bakwai, wata rawaya suka ce a cikin kwana shida. Kuma shi yafi cancanta mu bauta mishi."

Kai hannun shi yayi saman kai rigar jikina, yaja igiyar gaban rigar, rike hannun shi nayi.
"Ubangiji ya halicci Annabawa, kusa dari da goma sha uku, sannan ya zare manzan guda ashirin da biyar, sannan ya basu addinin suyi da'awa shi."

Sake fauce hannun shi yayi sannnan ya zare rigar zai fadi kasa na rike hannun shi.
"Ubangiji ya aiko Manzon Allah, Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama,cikin kabilar larabawa sabida yawan damuwar da suke me yasa ba a aiko wani daga cikin su ba, domin Yahudawa sun fi yawa a cikin annabawan. Sai gashi ya aiko musu dan uwan su, bakuraishe! Bahshimi, Dattijon kwarai, kuma aminttacen ya zo mana da addinin musulunci. Kafin nan dole idan zaka yi imani da Allah sai ka isa sharudan musulinci. Ubangiji yayi mana gata da ni'ima."

Zare igiyar yayi, cikin tashin hankali, na shiga mishi bayani tare da gaya mishi girman musulinci da abinda ya haramta, idanun shi sunyi jajjur, jijjiyar goshin sa sun mik'e. Uwa uba na jikin shi. Wani irin zazzaɓi ne ya rufe shi, kifi kanshi yayi bayan ya sunkuya goshina.

Har ina jin zafin jikin shi, ga baki daya ya narke min, gashi ba kadan ba, duk sai na damu da kai na. Kasa mishi kome nayi. Shi a tunanin shi yana rayuwa ne cikin takura ashe akwai babban kalubale da yake ciki.

Me yasa Mahaifiyar shi ta kashe mishi rayuwa? Me yasa ta hana shi fahimtar Meye rayuwa? Musamman da yake kuma jin tasirin addinin Musulunci.

Kasa fadin kome yayi har na kai shi bakin gadon ya zauna, kasa rabuwa yayi dani, yana rike da hannuna.kanshi a jingine da cikin, wani irin ajiyar zuciya yake saukewa daga lokaci zuwa lokaci, ban san ya ban tausayi ba, sai da na shiga shafa kan shi ina yatsina gashin kanshi sannan na fahimci tausayin shi da yake raina.

. A hankali na kawo mishi sharudan musulinci, tare da dokokin su, d'ago kai yayi tare da kallona sannan ya kuma mai da kan shi, ya rungume ni, nasan yana cikin damuwa ne, amma haka kawai Mehran ba zai tab'a rungume ni ba, fahimtar lokacin sallah yayi ne ya sani, janyewa daga jikin shi. Kallon na yayi tare da dauke kan shi, a hankali ya mike yana dafa bango, tab'e baki nayi a raina nace.
"Miskilin banza kawai, ya wani kwaso jiki kamar wani abun Arziki akan azumi ranar kamar zai dake ni, yau kuma kaje sun kulla maka tsiya zaka sauke min. Mitseww!"

Naja yi tsaki abuna, ban kuma jin zuriyar shi ba, domin iya abincin da na girka na rana yana nan na daren ma bai ci ba, ashe yana can kwance babu lafiya, shirun da nayi yayi yawa ne na tashi dake ban tab'a shiga dakin shi na wannan shashin ba, sai yau.

Da sallama na shiga a hankali, kamshin turaren sandal ne ya daki hancina, wannan shashin Narmin ce take shigo da wasu bayi mata guda uku har da Mahlika suke gyara mishi, tunda na shiga na hango shi can tsakiyar gadon, ya dunkule cikin bargo, a hankali na isa ta gefen shi na haura gadon tare da jan bargon na dafa goshin sa. Tab'e baki nayi a raina nace.
*Mazaje ana jin jiki*
Taba goshin sa nayi tare da gyara mishi kwanciyar shi, a hankali na fita daga dakin na je na sirka ruwan zafi, nazo na taimaka mishi ya rage kayan jikin shi sannan na shiga goge mishi jikin shi tare da dafa goshin sa.

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ.. 𝘉𝘐𝘠𝘜!!!   dynasty'sWhere stories live. Discover now