Page 35

194 27 0
                                    

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
     
*Wannan shafin naku ne Aunty Mamieh Mom Imam, da MOM Sayyid and Noor 😒😏 Me za ayi da basamuden kun nan*
Page 35

     Tarin da nake hade da aman ruwa ya sashi fita daga dakin ma, Baba ne ya shigo yana mamakin halin shi kamar bai damu ba, sai da ya gama bani kulawa sannan yace min.
"Kina jina?"
"Eh!"
"Yawwa sannun taso muje!"
Haka na taso jikina a sanyayye ga ɗan karen sanyin da nake ji, bayan ya nuna min yadda zanyi amfani da ruwan wanka da yadda zan sha, ya fita.

    Cire kayana nayi, sannan nayi wanka tare da wanke kayan tass, ina gamawa na nufi dakin na shafa mai sannan na same su, suna cin abincin ranar zama nayi na fara ƙoƙarin ci. Ruwan zafi aka mika min, na sha sannan na fara cin abincin.

        ---- wato Mehran tsakanin shi da Allah ya hana Ikram da Fudail haduwa, wai gudun kar su keb'e zai ce taje gidan shi, tayi mishi aiki kuma babu aikin, karshe zuwa yake ya sakata a gaba tana mishi karatun Alkur'ani. Har yayi barci tana ganin haka zata mike ta rufe shi da abu sannan ta juya zata fita zai ce mata.
"Banyi barci ba tukuna!"
Haka zata cigaba da zama har itama barcin ya dauke ta,yana ganin ta fara barcin zai zuba mata ido. Har sai yaga ta fara kokarin faruwa zai rufe nashi.

   Idan kuwa sallah take, yana kallon duk yadda take, har ta idar, sai ka lura zaka Fahimci haka, idan baka lura ba, sai ka zata barci yaƙe.

    A hankali suka cika wata daya cif, wanda ya kai watanin shi goma da zama sarki,. Zaman wata daya nan. Wani irin amayar da SO Mehran yayi a aikace amma a zahiran ce ya kasa furta kalmomin yabo ko burgewa, amma duk me hankali da tunani ya ga yadda yake ririta alamarin ta, sai ya fahimci yadda yake kaunarta.

      Ana gobe zasu bar garin, mutanen garin suka shirya musu biki da dare, anata shagali da raye raye, haka yan mata suka jata bata so, amma haka ta shiga. Kura mata ido yayi tana rawa. Tare da dariya.
             A karon farko da yaji tana tafiya a tsakanin zuciyar shi, kura mata ido yayi yana fadin a ranshi.
*Sirrintacciya na! Kinga yadda dariya yake kara Kawata fuskarki! Kin san girma da darajar farin cikin ki kuwa? Sirrintacciya na! Kin fahimci yadda kike haska dukkan Ni manta gurin? Idan da kin san da haka da murmushin ki sai tafi hasken farin wata kawa! Dariyar ki sai tafi iska kad'awa! Farin cikin ki sai tafi sanyin damina!  Sirrintacciya na! Tayu wasu sun gaya miki sirrin kyanki! Amma Ni da nake tare dake zan iya gaya miki shi yasa.*

"Sultan ko zaka shiga cikin rawan ne?" Girgiza kai yayi tare da nuna alamun a'a, hango Fudail yana ƙoƙarin shiga filin. Ya sashi b'ata rai, ya mike babu shiri, haka ya shiga cikin rawan. Kamar wani mashiya ko sikago, yana tsaye yana kallon yadda take dariya da juyi, hannun shi ya kai zai riko ta, ta zille mishi.  Sake kaiwa yayi ta kuma zillewa.

             Saka mata kafa yayi ta tafi luuuuuu zata zube ya tare ta, suka d'an rankwafa, yana kallon cikin idanun ta, itama tana kallon na shi.
*Kai kan ban san wani irin mayye bane?*
Murmushi me sauti ya sake mata, tunda take bata tab'a ganin murmushin da tayi mata kyau, har kumatun shi yana lubewa ba sai yau, hannun ta takai gurin, tare da kallon shi, tsintar kanta tayi da sake mishi murmushin tare da lumshe idanun shi.

          *Sirrintacciya na!!!*
    *Heydar!!!*
Ta faɗa a ranta, can kuwa kasan ranta wani tunani ne yazo mata, lokaci guda ta kwace kanta zata fadi ya d'agata cak,  ya dire ta da kafarta, dai dai lokacin da aka gama kid'ar haka sai ya bawa mutanen gurin damar tafa musu.

   Wannan yanayin ya haifar mishi da farin cikin da ba zai tab'a Mantawa ba, a hankali na zare hannun daga gare shi na fita daga filin da gudu, bai damu ba, shi dai ya fito abin shi yana me zama a gurin shi. Baya son ya cika zakewa akan al'amarin Yarinyar nan, duk da zuciyar shi ta zab'e mata suna da sirrintacciyar shi.

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ.. 𝘉𝘐𝘠𝘜!!!   dynasty'sOnde histórias criam vida. Descubra agora