Rayuwar Meenat

1 0 0
                                    

🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻
🧕🏻

*_RAYUWAR MEENAT_*
           
                        🧕🏻
                   🧕🏻🧕🏻
              🧕🏻🧕🏻🧕🏻
          🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
      🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

💞💞💞💞💞💞💞💞
*_(Labari mai taba zuciya♥_)*
💞💞💞💞💞💞💞💞

Story
     &
      Written
                by:

    *_Meenat Laweal tk_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
   *_PEN WRITERS  ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*Page 12-13*

........................Dandazo aka yi a bakin wajen domin mafi yawan mutane wajen suna sa ran za'a fito da 'yan uwansu , a gefe guda na juya inda na hango motar Fannerh ta sauke glass tana hangen bakin gate din.

Kimanin 1 hour ana abu daya, mutanen dake tsaye duk sun samu waje sun zazzauna.

         A can ciki kuma inda shugaban kasar yake ana fito masa files din mutanen yana ganin laifukansu, idan yaga wanda ya cancanta zai bada izinin a fito da shi.

A kuma wani dan sardado na hango wani ma'aikacin wajen yana waya kamar haka,

  "Toh ranka ya dade insha Allah, karka damu an gama komai ai baza'a gane ba," ya kashe wayar sakamakon wasu da ya ga sun taho wajen a wayance ya wuce ya koma ciki.

Mutane da aka tara ne shugaban kasa ya basu jari sannan ya bada umurnin da a fitar dasu kowa ya tafi.

Cikin murna kowa ya fito yana haduwa da danginsa, Fannerh ta fito da sauri ta karasa, sai dai har suka watse babu alamun Meenat wajen. Jingina ta yi da bango ta fashe da kuka don ta san hakan aikin mahaifiyarta ne, mota ta koma ta lalubo number din  Br Aminu bugu uku ya dauka,

Fannerh , ta ce" *Br can you help me please?*

Br Aminu, yace" me ke faruwa ne Fannerh?

Fannerh ta shaida masa komai,

Br Aminu, yace "Gaskiya Fannerh ba bangarena bane nan, amman zan yi kokari na gani bayan biki,

Fannerh,ta ce" shike nan na gode amma ka kokarta,

Br Aminu, yace"Insha Allah, me ye sunan yarinyar?

Fannerh ,ta ce" Aminatu,

Br Aminu, yace"Ok in kina da wani detail a kanta ki turo mini ,

Fannerh ,ta ce"Ok na gode" ta aje wayar.

Motar ta figa a guje ta bar wajen ta nufi gidansu.

   Karfe biyar daidai aka wuce da amarya gidanta, wanda ya ji kayan more rayuwa ta kowane fanni abin ba a magana domin barnar baki ne fadar yadda gidan yake da kayan da a kasa. Kun san harka dasu Momma akwai kashe dala"

Da yake suma a al'adarsu akwai kwana gidan amarya shiyasa ba ranar za'a raka ango ba ,

Tunda aka kaita ko leke bai leka ba gidan sabanin wasu angunan da suke zuwa , sai wajen 8pm Farouq yazo ya same sa a bangarensa.

Rayuwar MeenatWhere stories live. Discover now