🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻
🧕🏻*_RAYUWAR MEENAT_*
🧕🏻
🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻💞💞💞💞💞💞💞💞
*_(Labari mai taba zuciya♥_)*
💞💞💞💞💞💞💞💞Story
&
Written
by:*_Meenat Laweal tk_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*_PEN WRITERS ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/*بسم الله الرحمن الرحيم*
*Page 16-17*
Indo ce tsaye a cikin daya daga cikin azuzuwan dake a cikin primary din dake garin, koyawa take cikin nutsuwa,inda nakai duba na ga allon dake like ga bangon naga an rubuta IRS watau (Islamic Religious Studies). Koda ta fito daga class din kasancewar bata san kowa ba tasamu waje ita daya ta zauna, domin ma da yawan malaman suna mata kallon 'yar kauye tunda yawanci daga cikin gari suke ,sai masu sayar da abinci ne suka zama abokanan firar ta. Karfe 1:20 suke tashi ko da suka tashi takama hanyar gida tana isa tayi Sallah ta fara ayyukanta har malam Sada ya shigo, yaga tana ta surfenta.
Malam Sada ,yace"ni kuwa Indo yakamata ki daina surfen nan tunda yanzu Allah ya rufa mana asiri "
Indo,ta ce"malam kenan to shikenan ai yadda kace haka za'a bi."
Malam Sada, ya ce"yawwa kuma kinga gona ta da aka kwaceman za'a maido man ita ,kinga mu shikenan."
Indo, ta ce"hakane kam Allah ya taimaka mana ."
Malam Sada, ya ce"Ameeeen Indo."
Ya zauna yana yaran nan basu dawo bane, ta ce"eh kasan su sai biyu suke dawowa."
Malam Sada,yace"hakane na manta ne."
A kauyen sossai ake mamakin yadda Indo tasamu aiki ,wasu kuma na hassada da hakan masu zuwa yi mata murna na zuwa. Indo ta jinjina ma mahaifiyar ta domin ita ta tsaya mata ka'in da na'in ta tafi birni tayi karatu inda lokacin ake zagin yaddiko ana cewa ta tura diya karuwan ci .*Rashin ilimi babban ciwo ne sannan wadanda suka jahilce sa suna ganin ai in mace ta tafi jami'a sai ace ta tafi yawo ko makamantan su sannan ana mata kallon ba nutsattsiya ba , wannan zancen sam ba haka yake ba ilimin diya mace yafi komai dadi domin duniya ce zata ilimantu dashi, itama kuma zata ba yaranta ilimin,sannan suma zasu ba nasu yaran a haka har akai inda ba'a tunani, Allah yasa a gane a daina yi ma mata wannan kallon*
Ko da wata yayi cif aka turo mata albashinta ,tunda dama tana da asusun ajiya tunda tai makaranta, malam Sada ne yaje ya amso mata, sannan ya umurce ta da takai ma iyayenta su,
Yaddiko ,ta ce"Ni Indo ai kun fimu bukatar kudin nan, kuje ku siyi abunda zaku saya, kinga mahaifin ki ma yaku karba."
Indo,ta ce"haba Yaddiko , kefa kika tsayaman sannan yanzu kice bazaki karba ba kinsan bazan ji dadi ba.''
Malam Sada ,yace"gaskiya kam Yaddiko ki karba."
Ba yadda basuyi ba amman taki karba hakan yasa suka siyo masu kayan amfani, irinsu man shafawa,sabulai harda atamfa ta sai mata, sauran suka siyi kayan abinci suka aje .