🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻
🧕🏻*_RAYUWAR MEENAT_*
🧕🏻
🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻💞💞💞💞💞💞💞💞
*_(Labari mai taba zuciya♥_)*
💞💞💞💞💞💞💞💞Story
&
Written
by:*_Meenat Laweal tk_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*_PEN WRITERS ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/بسم الله الرحمن الرحيم
Page 14___15
.................. Da addu'a bakinsa ya farka barcin tare da 'yar mika, ya duba agogo yaga 4:50 na asuba mikewa yayi ya shiga toilet ya dan watsa ruwa a gaggauce ya dauro alwallah yasanya jallabiyar sa ,ya matsa wajen gadon yafara tashin ta , ta bude ido tana haba "Haba momy yau fa banda lectures kuma kike tashi na a wannan daren ki bari 11 ta ida please,
Murmushi yayi ,ya shafi gefen fuskarta ,
Yace" baby tashi asubah tayi ni na tafi masjid."
Ya fice daga dakin , bai dawo ba sai kusan 7 :30 am ,a tunanin sa yaga amarya ce ta samu ta kimtsa in yana nan ba zata sake ba, a tunaninsa.
Sai da yafara shiga part dinsa yayi wanka ya dan janyo system din sa ya yi 'yan ayyukan da zai yi ya mike ya shirya cikin kana nan kaya sun matukar amsar jikinsa , sannan ya dau wayarsa ya fito , kusan 10 lokacin ya nufi sashen ta .
Turus yayi yana kallon gadon yadda ya barta haka take, wani mugun haushi ya turnike sa domin ya tsani wasa da sallah, karasawa yayi yaja duvet din data rufa dashi , a firgice ta mike ,
Sky,yace"kin kau yi sallah Sarah?"
Sarah,ta ce" Ya Aminu duk karfe nawa yanzu lokaci fa bai yi ba "
Sky,yace "da yake shi lokacin mai aikin ki ke kula da shi da zai tsaya sai kin bata izini sannan ta murda second."
Sarah,ta ce"to ai na gaji shiyasa."
Sky, yace" tashi malama ki bada taki."
Mikewa tayi tana turo baki ita an takura mata , fitowa tayi ta daura Zane tasa hijab ta mika sallar ta cikin abunda bai kai 5 minutes ba ta mike tana niyyar komawa gado,
Sky,yace"Sarah zo nan ."
Karasawa tayi in da yake ta zauna ,
Sky, yace" ki daina wasa da sallah don tabbas zamu samu sabani dake kullum. "
Sarah, tace"toh dear, daman don nagaji kaga ansha hidima."
Sky,yace"duk da haka dai ."
Sarah, ta ce"jiya shine kayi barcin ka ko ka kyaleni?"
Sky,yace" me zan miki ne?"
Sarah,ta ce"amman dai kasan yadda nake missing din, jikinka ko?"
Sky,yace" To yanzu ba kina ganin sa ba."