ƳAR FARA

55 1 1
                                    

FARKO

A iya tunani na da duniya ga Musulmi na kwarai, ita waje ce da ake bautawa Allah, da kuma ƙin duk wani abu na aikin sabo. Wannan tunanin nawa tuni yayi hanun riga da na Amina Ƴar Fara, wadda ta kasance ƙaramar Bazawara mai tashen cin kasuwa da jikin ta.

Kafin na shiga cikin wannan labari, yana da kyau na zayyana maku kyawon fuska da jiki da Allah yaba ta, wanda take alfahari dashi a duk gurin da ta shiga.

Ita ɗin doguwa ce, amma ba irin wanda ya wuce kima ba, sannan gata da farar fata kamar Larabawan gabas ta tsakkiya, fuskarta madaidaiciya ce wadda masu hasashe suka tabbatar da tana cin fiye da nera dubu biyar a kullun domin kwalliya, baban abinda ke ƙara rikita Maza masu sha'awar yin zina da ita, da kuma matan dake sha'awar maɗigo da ita shine, yadda Allah ya halicci jikin ta da suffar kwalbar lemun koka kola.

Sai dai duk wannan iya shegen da ta ke yi, Amina ba 'ƴar kowan kowa bace a garin cikin garin Katsina, Mahaifin ta Ado Bahago tsohon Ɗan Dambe ne, wanda tun tana ƴar shekara biyar ya aka dokar masa zuciya a wajen dambe ya mutu, a halin yanzu Amina tana Zaune da Mahaifiyar ta. Kai a takaice ma dai Ita ɗin Ɗan wake ce, wanda ya fi uban sa kan-kan ba.

A wata Litinin mai zafi a zuciya da aljihu, wadda ta saka matasa masu zaman kashe wando zama a bakin wani dogon dandamali dake kusa da wani shagon sayar da kayan Masarufi suna fira, Kwatsam! Babu zato babu tsammani, a dai dai wannan lokaci wata mota mai numfashi ta cinno hancin ta a cikin lungun da wadannan matasa ke zaune.

Alokacin Majalisar waɗannan samamari masu zaman kashe wando ta cika maƙil, babu abinda suke yi sai faman gardamar Messi yafi Ronaldo, lokacin da suka ji sautin ƙarar Injin motar mai kama da sautin kyakyawan kiɗin turawan gabas ta tsakkiya, duk sai suka kai idanun su domin ganin wace kalar Mota ce wannan. Lokaci ɗaya idanun suka kafe akan motar, nan da nan numfashin su ya ɗauke na wucin gadi, jikin su ya koma babu inda yake motsi.

A hankali Motar mai kalar Ja ta wuce waɗannan matasa, kai tsaye bata tsaya ko ina ba sai kofar gidan su Amina. Ba wasu bane a cikin motar sai wani matashin saurayi da Baban sa yayi ƙaurin suna a ciki da wajen jihar Katsina.

Sunan sa Mustafa Amma ana ce masa Dady saboda sunan Mahaifin sane aka saka mashi, a gefen daman sa kuwa Amina ce zaune tayi tatul da kayan maye, saboda tsabar shayuwa ma da tayi bata iya ɓuɗe idanun ta sosai.
Da tsayawar Motar sai Dady ya dubi gurin da dake zaune, sai yaga har a lokacin idanun ta a rufe suke, watau da alamu ma bata san da tsayuwar sa ba a ƙofar gidan su ba. Ganin haka yasa yayi murmushi, sannan ya ɗaga hannun sa ya ɗan mangari gefen kafaɗarta.

Jin wannan duka yasa Amina ta buɗe idanun ta da kyal ta dubi Dady tace da shi a cikin yanayin maye.

"Haba Uban Shagali, kada ka karya mun kafaɗa mana"!
Dady na jin haka sai yayi Dariya, sannan yace da ita.

"Kiyi haƙuri Ƴar Fara, idan badda abin ki ma, idan na karya maki kafaɗa gobe wa zai kashe mani Gobara idan ta tashi"?

Duk da a cikin Maye Ƴar Fara take, sai da taji daɗin wannan kirari da aka yi mata, cikin karfin hali irin na ƴan maye ta buɗi baki tace dashi.

"To ai ni ma shi na gani, na ɗauka ka fara ga jiya da jikin nawa ne".

Dady ya dafe kai kamar wanda yayi a sarar miliyoyi Nerori, sannan yace da ita.
"Ko kusa kada kwalwarki ta ba zuciyar ki damar faɗar haka, wannan jikin naki yafi mun abinci da ruwan sha amfani sau dubu, sannan kuma kallon sa kaɗai yafi mun kallon tarin buhunnan kuɗi".
Kan Ƴar fara ya Ƙara girma da jin haka, cikin jan aji irin na ƴan matan bariki da suke yi ma masu harka da su ta Buɗe marfin motar daniyar ta fita, Cikin Sauri Dady ya maido ƙofar ta rufe, sannan yace da ita.

ƳAR FARA(Labarin Amina)Where stories live. Discover now