UBAYD MALEEK 1

2K 77 8
                                    

_*UBAYD MALEEK*_
(_Royalty versus love_)
_Mamuhgee_

_Bismillahir-rahmanirraheem_

*1*
Qoqarin sauke kayan dake kan jakinsa yakeyi fuskarsa cikeda annuri da farin cikin jikinsa ma na nuna hakan sbd yanda yake sauke kayan da kuzarinsa da dukkanin himmarsa.,
Fitowa bayi matarsa Kuma uwar yayansa tayi tana kallonsa cikin tsananin mamakin ganinsa adaidai wannan lokacin,
Kallon sama tayi tana son kwatanta lokaci idan ta kwatanta daidai zata Kira lokacin da guraren uku zuwa hudu na yamma,
Duban uban kayan daya shigo dasu da jakin tayi tana sake bayyanarda mamakinta a fili na ganinsa Rana tsaka batareda lokacin zuwansa ganinsu yayi sbd a qaidancen aikinsa sai bayan sati bibbiyu yake zuwa ganinsu yayi kwana daya ya juya sai Kuma bayan satin biyu,
Yau kwanansa shida da komawa Amma gashi tana ganinsa harda kaya haka,
inda yake ta fito tsakar gidan tana ajiye butar hannunta tana Dan sake fuska kadan ta qarado tana karban qaton akwatin qarfensa dayake qoqarin saukewa daga kan jakin tana Dan nishin nauyin akwatin tace"

Abal Kaine yanxu?

Kallon kayan data sauke tayi tana maido kallonta kansa tace"

wannan dukannin kayan fa??
Fatan dai lafiya?

Yana qarasa aje daurin karshe dake kan jakin ya jasa zuwa wata rumfar dake can nesa da dakunansu wadda sukai daure dabbobinsu lokacinda suka taba kiwo yakaisa ya dauresa yadawo Yana zama kan saqin data shimfida Masa Yana cewa"

Alhmdlh ya ubangiji.

Ruwa taje tadebo Masa a qaton kofi me nauyi takawo gabansa ta ajiye tana zama gefensa cikin sauke ajiyar zuciya tana sake gaishesa wannan karon cikin yarensu na amheric tace"

_Dehina metahi_
(Barka da dawowa)

Shan ruwan yayi sosai Yana jinjina mata Kai Yana cewa"

Yawwa barkanku da gida,
Nasameku lafiya?

Alhmdlh"tace tana sake Masa kallon tambaya sbd gabaki daya hankalinta baa kwance yakeba da ganinsa gida yanxu sbd tafi kowa sanin tsanin qarfi da ikon masarautar delah take dashi akan ma'aikatansu Dan shekarunta ashirin harda yan Kai batareda mijinta ba saidai yazo yaganta duk bayan sati biyu yakoma saidai idan tace takai Masa ziyara wadda kafin tagansa ma aikine saiyanzu da shekaru sukaje saidai yayansu suje sugansa duk bayan kwana biyu saigashi yanzu tana ganinsa kwatsam haka ba tsammani.

Sauke numfashi tayi ahankali zatai mgn ya rigata da kallonta cikin tattara Yar nutsuwa a fuskarsa ta dattijantaka yace"

Jamila nasan hankalinki ba'akwance yakeba da ganina adaidai wannan lokacin,
Ki kwantar da hankalinki lafiyace tasanyani dawowa,
Babu wani abu daya faru kamar yanda kike tunani,
Nadawone gida wannan karon gabaki daya da yardar Allah shikenan zansamu yancina zanyi rayuwa taredaku cikin iyalina,cikin nutsuwa.

Wani guntun numfashi ta sauke wannan karon dukkanin jikinta nayin sanyi dajin abinda yake fada Wanda tasan ba iyakacin maganar kenanba akwai babbar maganar dake gaban wannan daya fara ta dago murya a sanyaye tana kallonsa tace"

*_NEGES?_*

'Dan dauke kai yayi ahankali cikin 'Dan jin nauyinta ya jinjina Kai ahankali yace"

Eh negestati.

Sama numfashinta yayi cikin wani irin yanayi na tsoro da muguwar bugawar da zuciyarta tayi ta sunkuyar dakai idanuwanta suka fara qoqarin cikowa da hawaye
Ya kalleta Kai tsaye yace"

Mahaifina yayi bauta a delah tun yanada kuruciya har tsufa ya kamasa Saida yakai baya iya wata bautar Ni yabayar ya yanci kansa a bautar dela,
Nayi bauta a delah tun Ina qaramin saurayina harna zama cikakken saurayi harna aureki muka Tara yaran dake gabanmu,
Nayi shekaru sama da talatin Ina bauta a delah,
Kinyi shekaru kusan ashirin ko fiye kina zaman kadaici batareda mijikinba,
Yarana sun taso Basu zauna da mahaifinsuba suka samu dukkanin kulawarsa,
Shin kina ganin bai kamata ba Nima nasamu yanci nadawo gidaba na huta 'daya daga cikin yayana ta fanshi 'yancina?
Jamila kinfi kowa sanin daganan har lokacinda Rai zaiyi halinsa ba barin delah zanyiba matuqar ba Wanda zan bayar maimakon yancina
Da inada 'da namiji bautar da mahaifina yayi haryabar duniya Nima nayi Shima ita zaiyi da haka zuriarmu zataita tafiya fa Amma yanzu daga kaina inshallah wannan gadon bautar yaqare sbd nine me 'yaya mata su ba bauta zasuje yiba *_NEGESTATI_* zasu zama.

UBAYD MALEEKWhere stories live. Discover now