5

579 35 3
                                    

*_UBAYD MALEEK_*
_(Royalty versus love)_

*_Mamuhgee_*

*5*
Zubewa AFIA tayi kan kujera tana sake wani irin kuka tana cusa kanta cikin tafukan hannayenta dasuke rawa.
Kamar zai wuce saikuma yaji afian na buqatarsa ayanxun sbd yasan tana cikin radadi.
Cikin takunsa na zallar nutsuwa ta asalin jinin sarauta yatako ya iso gabanta tareda miqa mata hannu batareda yayi mgna ba ta dago jajayen idanuwanta dake tsiyayar hawaye ba kakkautawa ta damqe hannunsa tana Kiran sunansa ahankali cikin kuka mara sauti.

Janta yayi farhat na jikinsa ya haye sama dasu zuwa ainihin babban bangarensa dake daukeda qaton palon farko Dana biyu Wanda baiyi girman na farko ba acikin palon na biyu Nan qofar qaton master bedroom dinsa yake ita Kuma lailah qofar bedroom dinta na tun a palon farko sukuma su afia din sukeda manyan bedrooms dinsu guda biya ata cikin Palo na biyu dake qasa ita daya farhat daya Amma a dakin AFIA din take kwana da farhat sbd tazama tamkar itace uwar farhat din duk da akwai tarin Nanny's da masu aikin dake kula dasu duk su duka din sbd Sam tun tashinta kafinma haihuwar farhat mum dinsu tabarwa masu renonsu dawainiyarsu Sam batada lokacin kantama bare na 'yayanta shi koyaushe tana gurin aikinda zata Gina sunanta duniya tasan da ita shiyasa acikin kadaici afia ta taso harsai bayan uwan farhat duniya tasamu sauqi sbd duk da akwai masu kula da farhat itakam Bata barmusu ragamar farhat din dukaba musamman da watanta goma cif aduniya lailah ta yayeta daga Bata nono tun afia Bata iya dawainiyar farhat ba harta iya shiyasa farhat din duk duniya tafi shaquwa da afia da dad dinta duk da tanason mum dinta Amma tafison dad dinta da afia itama afian sbd sanin mum ba lokacinsu takedashiba yasa girman dole yahau kanta duk da qananun shekarunta tazama itace madam din gidan dole masu aikin gidan kaf umarninta kawai suke jira sbd ita suka gani Matar gidan ko lokacin jininta tayi baresu masu aikin shiyasa basa Sonta bakuma su tsanetaba tunda batai lokacinsu bama bare musgunawa ko wulaqantawa da tozartawa 'yayanta dai Kam suna tsananin sonsu da qaunarsu tareda tausayinsu duk sbd mahaifinsu UBAYD MALEEK Wanda suke tsananin jin dadin aiki a qarqashinsa duk da tsananin miskilancinsa da ikonsa mulki dake jininsa Amma baida tsanani ko tsauri ko kadan.

Table din lunch aka gama gyarawa yaja 'yayansa suka isa dining room din farhat Kam harta sakewarta ganin ga dad dinta ga afia to itakam batada damuwa tunda dama haka suke rayuwa mum batanan koyaushe.
AFIA ce dai Saida qyar ta iya tuttura abincin Shima yacine kawai saidai Babu Wanda ya isa yace ya karanto kokuma ya fahimci halinda zuciyarsa da tunaninsa suke ciki cikin nutsuwarsa kaman koyaushe yaci abincinsa.

Ranar baisake fita ba yini yayi da yaransa cikin tsananin kulawa da qauna har dare sukai dinner sukaje sukai sallah da wanka suka kwanta AFIA na rungume farhat cikin jikinta sabbin hawaye masu zafi suna gangaro Mata.
Washe gari ma tare sukai breakfast da dad dinsu su suka fara wuce school da driver dinsu kafin shi daga baya ya fice.


Ahankali kwanakin suka fara tafiya damuwa tashigi afia sosai sbd yanda ta Sanya rabuwar iyayenta cikin ranta har abin ya tabata yafara taba karatunta komai Bata ganewa a makaranta tun Ana Mata mgn har Saida school din suka nema dad dinta sukai Masa bayanin kwata kwata Bata gane komai na karatu ko exams dinta gabaki daya Babu Wanda taci hakan yasa ya ragewa kansa aiki sosai sbd samun lokacin zama da yaransa Dan afia idan akai wasa zata iya samun matsalar qwaqwalwama.
Kullum takan Kira mum dinta Amma Bata wani Bata lokacin mgn she's always busy with aiki aiki aiki hakan yafara Sanya afian jin haushi musamman da ita mum din Bata taba kiraba saidai ita takira ta bangare daya ga dad dinsu Yana iya kokarinsa duk kasancewarsa me tarin abubuwan Yi Amma duk ya taqaita sbd su 'yayansa sai hakan yasa tafara dawowa hankalinta taji inama dad zaisamu farin ciki Kamar kowane mijin aure.
Ahankali ahankali trauma din rabuwar iyayenta yasaketa sbd watanni da aka 'diba tuni ta sakewarta yanzu suna rayuwarsu cikin walwala musamman Mum Sarah dake kulawa dasu sosai yanzu kamar itace ta haifesu matarda tun haihuwar AFIA Amman UBAYD ta Aiko musu da ita daga delah gizah gashinan haryanxu tana taredasu tana musu aiki danma ta zama Kamar kakarsu Amma Mum Sarah suke ce da ita sbd tun afia na qarama da farko ma ta dauka itace ta haifeta saidatai wayo tasan lailah ce ta haifeta Amma duk da haka qaunar kamr uwa da 'yace tsakanin afia din da mum Sarah,
Yanzu gidan rayuwarsu suke Kamar dama haka suke Basu taba rashin waniba agidan hakan yasaka hankalin dad dinsu kwantawa ya maida hankali kan harkokinsa musamman idan Yana dubin shekarun sauka mulkin NEGES ABDUL-SAMAD MUH'D KALEEB wato sarki na yanzu qanin mahaifinsa Kuma mijin mahaifiyarsa Wanda sbd Yana yarone mahaifinsa yarasu shiyasa akabada mulkin wa qaninsa kafin shi dansa ubayd ya girma Wanda Sam shi yanzu ba wani mulki dayakeso ko yake gabansa shiyasa bai taba sha'awar zama kusada mulkin ba yayi nesa dasu sbd ma kada son abin yasamu damar shigarsa Amma gashi lokaci na son qaratowa.

UBAYD MALEEKWhere stories live. Discover now