4

599 34 2
                                    

*_UBAYD MALEEK_*
_(Royalty versus love)_

*_Mamuhgee_*

*4*
Cikin tsoro da rawar murya NURU tace"
Padima kidena cewa mutuwa kina bani tsoro sosai kidaina kuka menene Dan Allah ki dena kina bani tsoro.

Ganin yanda NURU duk ta firgice cikin tsananin tsoro yasa tadan sassauta tayi tunanin amfani da tsoron NURU sbd dama can ita abu kadan yake Bata tsoro saita sake marairaice fuska tana faso wani kukan tace"

NURU idan Banga amed mukai magana ba akwai babbar matsala wlh komai zai lalace zamu rasa komai da iyayenmu duk mutuwa zamuyi.

Zaro manyan fararen idanuwanta NURU tayi jikinta na daukar rawa tana sake padiman takasa magana tana neman yin baya ta fita a rude padima ta riqota da qarfi tana cewa"

NURU wlh dagaske nake idan bangansa munyi magana ba komai zaifaru Dan Allah kimin hanya naganshi idan nadawo zan fada Miki komai Amma wlh rayuwata na cikin hadari danasu abal ma..

Kasa fahimtarta NURU tayi sbd firgici sai rawa da jikinta keyi ganin hakan yasa padiman taja wani qaramin tsakin takaici tareda girgizata da qarfi ta jawota ta direta zaune tafara shafa bayanta tana hura Mata iska tana kiranta ahankali ahankali hartafara nutsuwa tana dawowa hayyacinta saidata rarrasheta tadawo hankalinta tsaf tukuna ta janyota ta kwantarda kanta kan cinyarta tafara Sabin hawayen samun yaddar NURUn tasake fada Mata abinda tafada Mata da farko NURUn daketa ajiyar zuciyar ta qanqame padima cikin tausaya Mata murya amatuqar sanyaye tace"

Padima idan kikaga amed din shine zesa bazaki kashe kanki ba ko?

Eh NURU bazan kashe kainaba Ni sbd ma kune nakeson ganinsa na nema mafita.

Haka ta lallaba NURU taringa marairaice Mata da kuka hartayi nasarar cika tunanin NURU da tausayinta akan alamarin shiyasa washe gari da za'aje wankan ruwan Madara saita lullube fuskarta taje amaimakon padima bayan tayi Mata hanya sunyi sauyin kaya ta fitar da ita gidan masu wankan dasuka ganta saisuka tambaya tace ai yanzu ita za'a ringawa ba padima ba dayake bayin qasane gabaki daya saisuka yarda sbd manyan bayi basa fitowa delah bare akawo musu irin wannan.

Dama Shima NURU taje ta sanar dashi padima zata fito tanason ganinsa shiyasa yaje inda suke haduwa Yana jiranta danshima a mugun qage yake da ganinta Dan wlh Shima be shirya mutuwaba tunda yasamu labarin ita aka bayar yasan qaryarsa taqare kashesa zaayi duk ranarda akaji shine yafara kwanciya da ita.

Kamar munafuka haka take tafiya tana waiwaye tana boye fuska harta iso Yana ganinta da gudu ya qaraso yakama hannunta suka nufi can nesa da gidajensu cikin wani lambu bayan bishiyar ayaba ya rungumeta Yana cewa"

_Ya Allah Padima nafekushi_
(Ya Allah padima Nayi kewarki sosai)

Kuka tafashe dashi tana turesa daga jikinta tace"

Amed duk mutuwa zamuyi
Banason mutuwa guduwa zanyi da qasarnan zanshiga duniya bazan tsaya akasheni ba...

Riqota yayi da sauri Shima cikin firgicin yake yace"

Padima ki nutsu musamo mafita Nima angaya Miki na shirya karban wannan hukuncin ne?
Bazan iyaba nikaina mafitar nake nema.

Zamewa tayi qasa tayi zaman dirshan tana cewa"

Amed kayi gaggawar samo mafita kokuma kawai mu gudu.

Mu gudu muje Ina padima?
Idan muka gudu burirrikanmu fa damuka Dade muna....

Cikin masifar tashin hankali ta katsesa da cewa"

Burin banza tunda Saida rayuwa zamu cika burin,
Ni kaga kawai musan abinyi wlh na cikin masifa wannan wane irin balai ne nasaka kaina aciki amed ka cuceni...

UBAYD MALEEKWhere stories live. Discover now