3

592 29 0
                                    

*_UBAYD MALEEK_*
_(Royalty versus love)_

*_Mamuhgee_*

*3*
Tafiya takeyi cikin nutsuwar datafi Kama da jin Kai da taqama musamman yanda jikinta ke girgizar daukan hankali shiyasa duk Wanda ta hadu dashi a hanya yake hadiye Mata yawu musamman wainda sukasan padima ai tafi karfinsu sbd kyanta da ikonta tareda sanin Wanda suke soyayya dashi din daga delah yake wato Dan babban sarkin fadawa bama Wanda yake Nanba na can gizah.
Daga gurin karbo baqin lallensu take sbd koyaushe ita mace ce da Bata rabuwa da qyale qyale shiyasa yanada wuya kaganta Babu lalle faratanta na hannu Dana qafa shiyane qarin banbancin tsakaninta da NURU wadda duk wannan ta daukesa Kamar bayyanarda kyawu ne Wanda ita tafi ganin burgewarsa idan kayi aure kayi acikin gidanka.

Daga bayanta taji anriqo hannunta ta tsaya cak tareda wani juya idanuwanta wani qayataccen murmushi na sauko Mata sbd sanin Babu Wanda yake iya riqota haka sai mutum daya saidai kafin ta juyo ta hango su NURU tafe da sauri ta juyo ta jasa da gudu suka boye bayan wata qatuwar bishiya tana Dora Masa hannun abaki qasa qasa tace"

Shihhh su NURU na zuwa.

Wani shu'umin murmushi ya sakar Mata Yana gyada Kai kafin ya juya ya zubawa NURU mayun idanuwansa dukkanin yawunsa na katsewa akan NURUn,
Meyesa ba NURU ce wadda Allah yabasa sa'a akantabane Dan wlh baitaba jin mugun kwadayin maceba Kamar NURU gashi padimanma tai Masa Amma da zaa basa zabi da NURU zai zaba Dan duk Wanda yagama samunta a Mata ko a abokiyar haihuwa yagama dacewa,
Mummunan faduwa gabansa yayi daya tuno da hadda abal dinsu acikin yan sauyin 'yanci take ya waiwayo da sauri ya kalli padima Yana girgiza Kai Dan wlh bazai yadda yabarta tashige zuriar delah ba tabarshi Dan har abada bazai taba samun kyakkyawar mace kamarta ba tunda dai NURUn yasan ba samunta zaiyiba Kuma dai dole cikin dayan biyun ne ko padima ko NURUn,.

Ina Ina ina""yafada cikin ransa da sauri Yana girgiza kafin ya maida kallonsa kan bayan NURU data wuce Yana tunano da kaf delah yanzu duk Wanda za'a kaiwa negestati Babu Dan yaro yaro sbd yara yara shekara daya kenan cif da aurarda yayan masarautar delah din su goma sha daya Kuma a qaida saikayi shekaru uku da aure zaka fara karban negestati sai wainda basuyi aureba sukuma baa Basu negestati sai sunyi aure.

Kallonsa padima tayi da manyan idanuwanta tana cewa"

Yaya dai?
Tunanin me kakeyi?

Wani murmushin bazata ya sakar Mata Yana sake jawota jikinsa Yana shafa hannuwanta Yana matsawa ahankali ya kashe ido Yana cewa"

Padi padi,
Padi nidai maganar gaskia zanje nasamu abal dinku yasan da maganarmu sbd so nake kafin kwana talatin dinsa tacika kinzama tawa mun wuce gizah..

Da wani kallo ta katsesa tana Dan zamewa idonta akansa tace"

Kwana talatin kamar dai wadda aka gaji da ita,
Amed nafada maka banason auren gaggawa sbd inason aurena yazama abinda zai burge kowa,
Banice baiwa ba abal dinane bawa Dan haka Ni inada damar yin bikin aurena kamar na kowanne 'yantacce,
Hakama Ina buqatan shiga boyon wankan ruwan madarar nono na tsawon sati biyu hakama Ina buqatan siracin nonon raqumi na tsawon sati biyun Shima sbd ranar dazan fito muka isa gizah aranar za'a tabbatarda nafi fiyeda Rabin matan sarautar kyawu.

Wani murmushin manufa tasaki tana sake riqe hannuwansa cikin kisisina Dan kuwa itadai babban burinta tasamu isa delah gizah inda asalin arxiki, mulki da sarauta suke
Kyawunta shine zai cika Mata burinta shikuma amed shine mukullun tafiyarta.

Cikin marairaice fuska yace"

Padima bazan iya Bari kwana talatin din abal dinku yacikaba sbd zai iya zamtowa kece zai bada bazan iya rasakiba padima mutuwa zanyi idan bake.

Wani kallon rashin fahimta take binsa dashi fuskarta na sauyawa tace"

Badawa Ina?

Gyara tsayuwa yayi Yana sake tamke hannunta yace"

UBAYD MALEEKWhere stories live. Discover now