NA TAKO PAGE 2

116 5 7
                                    

✨✨✨ *NA*
             *TAKO*✨✨✨✨



               ✍️
    *AISHA GALADIMA*

'''Follow me on Wattpad
@Ayshagaladima666'''

              2️⃣






A  hankali ya dago kansa ya kalli gefen da kakus din ke nuna wa daga kasan kafafunta ya fara kallo Tana sanye da wasu talkamin roba ne  se dogon hijabin dake jikinta kallo Daya zaka Masa kasan   ba sabo bane Dan Babu alamar wata guga a tattare dashi , Wanda har kasa ya Kai mata haka yaci gaba da da kallonta har zuwa zagayayyar fuskarta  fara wadda ta Mata fayau Dan ba kwaliyya tayi Mata ba ,Yaji wani yam a ransa ,  tabe Baki yayi a ransa yace kazama kawai, ba kallonshi Maryam keyi ba Kai tsaye kakus ta tsura ma ido Tana mamakin Wai wane irin haline da kakar tasu ,ganin da kakus tayi Maryam batada alamar takowa yasa ta daga murya tace"ke mairo kizo Mana" se da ta dansha jinin jikinta kafin ta fara takawa zuwa inda kakus din take ganin mutanen da take tare dasu kamar wadda kwai ya fashewa a ciki a haka ta fara takawa ,shikam tuni ya dauke kansa tun kallon farko Daya mata Tana karasowa wurin magana take son ta fara taji mutumin dake gefen kakus ya fara magana"ke Baki da hankali ne ,Zaki bar wannan tsofuwar ita Daya bayan tare kuka zo  idan wani Abu ya same ta fa? Zata yi magana ya katseta yace "keep ur dirty mouth shut for me" Maryam duk inda ranta yake ya Kai kololuwar baci Dan ta tsani a Mata fada har dai irin Wanda ba'a Bata damar wanke kanta, ko Ina ruwanshi da ze wani tsareta da fada tsabar shishigi ko da yake ba laifin shi bane ga wadda ta ja Mata duk walakancin da aka mata, "Ai turance min ita da kyau Dan Albarka " cewar kakus , shi kanshi kaka dariya ta bashi ya dai kanne ne  ya fara tunanin wanna tsofuwar itama Bata da dama
Kakus tace " nagode mu bari mu wuce base mun shiga motar Nan ba Kar kafin mukai yarinyarnan tama bacci a mota tunda Basu taba shiga ba fa " yanzu Kam ya fara Jin haushin kakus din ammah ya Mata uzurin tsufa a ransa
Maryam dai na gefe idanunta tab da hawaye ,kudi ya ciro note Daya ya ba kakus yace to gashi mama se anjima ,karba tayi Tana washe Baki godiya take ta zuba Mai Maryam Kam juyawa tayi ta fara tafiya ,kakus ganin Maryam tafara tafiyarta yasa da sauri tabi bayanta har da hadawa da gudu ,shima motarsa ya shige ta cikin mota ya hangi yadda kakus ta fara  bin bayan Maryam har da su gudu "Allah ya kyauta " yace a ransa ya kula yarinyar nada Jin Kai yaso ta tanka maganar da yayi da ya koya Mata hankali , haka kakus tayi kokari ta cimma Maryam dake kokarin fita daga cikin masalacin ta rike Mata hijab juyowa Maryam tayi Tana kallon kakus ,"Innalillahi! Ni habi me zan gani haka badai kuka kike yi ba mairo yaushe kika fara min bakin ciki ban sani ba daga Kinga baturen can yaban bandir na din naira hamsin kike zubda hawaye "
Cewar kakus ,Maryam kwace hijab dinta tayi daga hannun kakus tare da goge hawayen da suka zubo Mata sannan  tace  " Allah ya tsare ni nayi bakin ciki Akan wadannan kudin da'a ka Baki ko fiye da hakan ya Baki wallahi ko sisi bana bukata daga ciki Ina godiya da Wanda mahaifina yake da shi ko kasa muke ci ni bazan iya bara ko rokon wani ya ban kudi ko wani abuba" da sauri kakus tace"Kinga mairo Kar muje gida ki hadani da salisu Nima ai ba rokonsa nayi ba shiya bani sannan Koda kika ji nace zan karbi sadaka ai ba Wanda nama magana  Kuma tunda kince bazaki karbi ko sisi ba se na adana abuna se aurenki na fitar nai shagalina " kallonta Maryam  tayi a ranta ta fara tunanin Anya kakus kanta Daya kuwa ,hanunta taji kakus ta rike tace " kinga Ni dai mutafi gida Dan Allah karki tada zancan Nan a gida " Maryam Bata tanka taba a haka suka fara tattakawa a kasa har suka Isa gidan nasu Wanda kallon farko za kama gidan kasan cewa su din talakawa ne sosai

Sallama Maryam tayi aka yi  shiru ba'a amsa ba se da kakus ta daga murya tace " Wai ko ba mutane a gidan ne " sannan fa aka daga wani yamusashen labule wata katuwar Mata ta fito zani daban Riga daban kamar ba sallah ba tace " Ahh ganinan ciki Innah kin dawo"  kakus tace "eh na dawo a kawo min abincina daki " Maryam shiga kicin ki dauko kwanon Innah na abinci ki Kai Mata kizo kiyi sharar gidan Nan " cewar matar "to" tace  ta wuce kakus Kam har ta Isa dakinta  abincin ta  dauka taje dakin kakus ta aje Mata har ta juya zata fito kakus tace " mairo dawo muci tuwon mana kafin kiyi sharar " kamar ta kyale kakus se dai cikinta har wani kuka taji Yana Mata dole ta juya ta dauko tuwon ta bude suka fara ci suna gamawa ta fice ta tafi wurin sharar tsakar gidan nasu

Motocin nata sharara gudu Basu zarce ko'ina ba se kofar wani babban gini kallo Daya zaka Masa ka tabbatarwa kanka wannan gidan sarauta ne tsayawarsu keda wuya aka bude kofar gaban mota wani mutum sanye da suit black hade da bakin glashinsa ya zo ya bude Dayar kofar baya ta motar , A hankali ya zuro kafar tasa dake sanye da rufaffin talkami Baki kasa ya fito ,a zahirin gaskiya shi din kyakyawane irin na bugawa a jarida ,koshi yasa kakus ta rude ta kirasa da bature a Dan iya saninta kenan ma, Wanda kallo Daya zaka Masa ka tabbatar da Yana da alaka da larabawa ,tattakawa yayi ya shiga cikin ainahin gidan, part part ne ,Daya daga cikin part din ya shiga da sallamarsa   Amsawa akayi ya shiga ,wata kyakyawar mace ce zaune a daya daga cikin hadaddin kujerun falon bayi zagaye da ita ,ko ba a fada ba tsananin kamar da yake da matar dake zaune zaka San cewa mahaifiyarsa ce ,bayin na ganin shine suka fara fita Daya bayan Daya ,bayan ya cire talkamin sa Kai tsaye wurin matar ya nufa ya zauna kusa da ita tare da Dora kansa Akan kafadarta  a hankali yace "Barka da Sallah mom" fuskarta cike da murmushi tace "barka my son har an dawo " daga kansa kawai yayi "kaje wurin mahaifin naka" cewar mom
"A'a be dawo ba ai can na barosa " ok kaje part Dinka bari nasa a kaima abinci
Kaga da kayi aure Shikenan na futa " Jin abunda tace da sauri ya Mike Yana Bata fuska   tare da ficewa daga dakin ,girgiza Kai kawai tayi Tanan mamakin yadda cikakken namiji kamarsa  duk lokacin da ta Masa maganar aure yanayinsa se ya canza  baya son a Masa magana ,Allah ya kyauta kawai tace

Aysha galadima ce............✍️

Vote
Comment
Share

NA TAKOWhere stories live. Discover now