༺༻🌹༺༻
࿙꧁꧂꧁꧂࿚
֍*🇧ᝪN ᝪN ᝪ...!*
[𝑹𝒖𝒇𝒆 𝑲'𝒐𝒇𝒂 𝒅𝒂 𝑩'𝒂𝒓𝒂𝒘𝒐]࿙꧁꧂꧁꧂࿚
֍
༺༻🌹༺༻*Տᴛ⌾ℛℽ & ᗯℛⅈᴛᴛℰℕ*
*ɮ̋ʏ̋✍*
෴ℛαвⅈ́'α𝙩 ѕвѕ෴
❨ცıɠ ɠᵃ̨ι❩*©®-'Yᴀʀ 𝓢𝓲𝓭𝓲 ✍🏻*
▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬
Jσเɳ ɱε σɳ ωαƭƭρα∂:@Bเɠ-ɠαℓ*🌹ℙaℊℰ❏☞5-6*
Misalin k'arfe d'aya da rabi na rana su Halima suka fara shirye-shiryen tafiya bayan sun gama taattaunawa tare da Salma kan cewar za su tafi tare, tun da da ma Halima ba sanin wajen ta yi ba, sai dai kuma Salma ta shaidawa Halima cewar muddin suna so su je a kan lokaci dole ne su tafi da wuri kamar misallin k'arfe biyu ko da mintuna sabida nisan wajen.
Jin hakan ya sa Halima ta fara k'ok'arin tashin Rumaisa dan ta ci abinci su d'auki hanya, ya yin da ita kuma Salma ta fad'a 'toilet' dan watsa ruwa, sai dai wani hanzari ba gudu ba duk da irin tashin da Halima ke yi wa Rumaisa a banza - an yi wa Jaki tsarki [In ji hausawa], dan babu alamar motsinta bare har ta farka.
Al'amarin da ya yi matuk'ar d'aga wa Halima Hankali kenan, ba shiri a gigice ta kwalawa Salma kira, wanka Salma ta ke amma jin irin kiran da Halima ke kwala mata ya sa ta hanzarin watsa ruwa ta fito a gigice.
A guje Salma ta nufi d'akin da Halima take, zaune ta tarar da ita ta had'a kai da gwiwa ta zuba uban tagumi da gaba d'aya hannayenta ta na kallon Rumaisa.
Zaune Halima take gaban Rumaisa fuskarta cike da tsoro da damuwa gami da taraddadin abin da zai je ya zo, tambaya Salma ta fara yi wa Halima "Halima lafiya?" Fuskar Halima cike da damuwa a gigice ta ce "na zo tashin Rumaisa sai na ga ba ta motsi, na tasheta tak'i farkawa Salma, ban san me ya ke faruwa ba", Salma ta tsuguna ta hau tab'a jikin Rumaisa tamkar wata likita ya yin da ta gama duba ta sai ta yar da Hannun Rumaisa ta ja da baya a tsorace.
Kallo Halima ta fara bin Salma da shi, bakinta bud'e kamar mai shirin furta wani abu, daga bisani kuma ta ce "me kike nufi?" Fuskar Salma cike da tsoro ta ce "Ba ta motsi ni kaina na ji ba ta motsi innalillahi...! yanzu ya za a yi?" A guje Halima ta fita tsakar gidan, ta hau dube-dube tamkar cikin gidanta can gefe ta hango wani k'aramin kofi ta d'ebo ruwa ta shiga ta hau yayyafawa Rumaisa tare da jijjigata, ita ma Salma matsawa ta yi dab da inda Rumaisa take tana jijjigata tana kiran sunanta Rumaisa!!!.
Gaba d'ayansu a gigice suke sun kuma d'imauce tunanin Halima d'aya ka da aikinsu ya koma baya.
Sun d'auki tsawon lokaci suna k'ok'arin ganin sun shaho kan matsalar Rumaisa, wai shin ta mutu ne ko kuwa da sauran numfashi mak'alewa ya yi ta zama sumammiya?, tambayar da kowacce take wa kanta cikin zuciya, wadda ba su da amsarta.
Sun juma gaban Rumaisa suna sak'ar zucin da ba ta da hanyar kuncewa, Salma ta ce "Ko dai mu kaita asibiti?" da sauri Halima ta ce "Asibiti kuma? so kike asirin mu ya tonu, wanne irin asibiti,?, ni babbar matsalata shi ne a ce duk wannan wahalar babu biyan buk'ata?" sun jima suna jiran farfad'owar Rumaisa amma shuru ya yin da lokaci ya ke ci gaba da tafiya kowacce ta zuba uban tagumi na rashin samun mafita idan har aka ce Rumaisa ta mutu ya za su yi, ina za su kai ta?
Suna cikin zance da zuciyarsu suka ji alamar motsin farfad'owar Rumaisa, da sauri suka katse tunanin da suke yi, suka dawo gare ta ya yin da suka fara k'ok'arin mik'ar da ita zaune, suna kiran sunanta "Rumaisa tashi" Bin kowaccensu Rumaisa ta yi da kallo cikin rashin fahimtar abin da ya ke faruwa, suka yi murmushi bayan sun kalli juna, da sauri Salma ta mik'e ta shiga d'aki ba jimawa ta fito sanye da wasu kayan, Halima ta ce "ba sai ta tsaya cin komai ba idan mun dawo ta ci, mu tafi kawai.
Ba su sha wata wahala ba wajen samun abin hawa, suka d'auki hanya bayan Salma ta k'watantawa mai Keken Napep d'in.
Tafiya suke tamkar wanda za su bar gari duk da cewa daman k'aramin gari za su nufa, tafiya ya ke amma Halima cewa take ya k'ara sauri yana k'ara gudu, duk da haka ba ta daina magana akan gudun da ya ke ya yi k'aranci ba, har sai da ya kai k'arshen gudunsa.
Wani k'aton ice ne mai matuk'ar kauri tamkar an sare bishiya ta fad'o k'asa k'wance a hanyar, ya yin da mai keken Napep ya yi k'ok'arin take birki amma ina! Ya kufce keken Napep d'in ya juya ya k'ara juya wa saura kad'an ya kifa Allah ya taimake su suka zube k'asa gefe guda, da k'yar dai suka iya mik'e wa ba tare da wani ya samu wata matsala ba sai iya kujewa kawai, ita kuwa Rumaisa babu abin da ya same ta tun da daman a tsakiya suka saka ta, dan haka suka ci gaba da tafiya.
Tafiya ce mai nisan gaske, wanda akan shafe awa guda ana yi ko fiye da hakan, sun juma suna tafiya kafin a sauke su a dai-dai wata k'aramar rumfa ta langa-langa, Halima ce ta zuge jaka ta fidda kud'in da ta bawa wanda ya kaisu, sannan suka ci gaba da tafiya.
Waje ne wanda babu wani mahaluk'in da yake zuwa wajen face wanda imaninsa ya ragu, waje ne da babu motsin kowa face ciyayi da kuma dogayen bishiyun da suka dad'e a duniya, manya-manyan bishiyu ne wanda ganyansu sun yi yad'o da jijiyoyinsu sun fidda guraren zama dan hutawa, sai dai wajen babu wanda za ka gani bare har ya zauna a k'asan bishiyun ya huta.
Tun da suka isa wannan waje Halima take kallon inuwar bishiyun tana ji tamkar ta je ta zauna ta huta, Salma ce ta fara ba ta labarin wajen, wajen ne da aljanu kad'ai suke iya zama sai kuma wasu hatsibiban mutanen da imanainsu ya yi k'aranci, da mutanen da suka kafe kansu da tsari ta ko ina, muddin ba ka d'aya daga cikin wad'annan mutane in ka je ka zauna toh za a iya rasaka ba tare da wata alama ko dalili ba, ko kuma halittarka ta canja zuwa tsuntsu ko Akuya ko Tinkiya.
Take Halima ta fara wani sak'e-sak'en na daban, ji ta yi ranta ya yi matuk'ar dad'i amma dai ta fi gane wa da zuwa inda za su je, tun da shi magana ne baki da baki.
Suna cikin tafiya can suka hango wani babban kogo wanda yake tsakiyar wasu bishiyu biyu tamkar tagwaye, domin kuwa girmansu da tsayinsu da yanayin ganyen da ke jikinsu duk yawansu d'aya kuma irinsu d'aya, haka ma k'asan jijiyar zubewarsu d'aya, sai dai wani abun ban mamakin bishiyar da ke tsakiya kad'ai ita ta ke da wannan kogon babu ganye jikinta ko guda d'aya sai dai kararen da ke tsaye a jikinta tamkar an zuge ganyen jikinta, sauran bishiyu biyun da suka fidda ganye suka yi yad'o su ne suka rufe ta har wajen ya ba da inuwa mai ban sha'awa da birge wa gami da k'ayatarwa.
Tun da suka hango wannan waje Halima ta kasa d'auke idonta daga kan wajen har suka k'araso dab da wajen, sai a lokacin ma ta lura da abin da yake k'asan bishiyar, daga gaban bishiyar waje ne a rairaiye a shimfid'e tamkar an shinfid'a dadduma ko tabarma.
Ya yin da b'arin hangun wajen ya ke da makamanciyar shinfid'a irin wadda suka fara gani, shinfid'a ce da aka yi ta da k'asa ba tare da an zuba siminti ko wani tab'o ba, gajerun bishiyu ne a kowanne b'angare na wajen wanda suka kewaye wajen dama da hagu suka kuma lullub'e shi ya zama inuwa.
Halima ta bi Salma da kallo, bayan ta yi mata nuni da ta cire takalmanta su shiga su zauna akan shimfid'ar da ke gefen hagun.
Ba tare da b'ata lokaci ba Halima ta yi yadda Salma ta umarce ta ita ma Rumaisa ta cire takalmanta suka shiga ciki suka zauna akan shinfid'ar da ke hagun.
Zamansu ke da wuya suka jiyo wata guguwa me k'arfi ta taso, iska ko ta ina, ji suke tamkar za a k'washe su daga zaune sabida k'arfin guguwar, wani irin sauti mai matuk'ar rud'ar wa suka rink'a ji yo wa tamkar dariya-dariya da wani irin gurnani mai rikitar wa, kalle-kalle suka rink'a yi ta ko ina cikin tsoro tare da dube-dube suna k'ank'ame jikinsu.
Wani sauti mai k'arfin gaske ne ya k'ara k'aruwa ya yin da sautinsa ya rink'a matsowa kusa, ji suke dab da kunnuwansu ba tare da sun shirya jin hakan ba, zuciyar Halima cike da tsoro gabanta ban da fad'uwa babu abin da ya ke yi, ji ta ke da ma ba ta zo wajen ba, ko dai shi ma wajen ba a zamansa Salma ta yi b'atan hanya ne?.............✍🏻
*_𝐘𝐚𝐰𝐚𝐧 𝐂𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭 𝐘𝐚𝐰𝐚𝐧 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠.......👌🏻_*
🌹☞ℬıɠ ɠᗅ̨ι *¢ɛ✍🏻*
YOU ARE READING
BONONO...! [𝑹𝒖𝒇𝒆 𝑲'𝒐𝒇𝒂 𝒅𝒂 𝑩'𝒂𝒓𝒂𝒘𝒐]
Kısa HikayeRayuwa mai cike da ban al'ajabi gami da hargitsi, ya yin da sharri ke juya wa ya koma wajen mai shi.