༺༻🌹༺༻
࿙꧁꧂꧁꧂࿚
֍*🇧ᝪN ᝪN ᝪ...!*
[𝑹𝒖𝒇𝒆 𝑲'𝒐𝒇𝒂 𝒅𝒂 𝑩'𝒂𝒓𝒂𝒘𝒐]࿙꧁꧂꧁꧂࿚
֍
༺༻🌹༺༻*Տᴛ⌾ℛℽ & ᗯℛⅈᴛᴛℰℕ*
*ɮ̋ʏ̋✍*
෴ℛαвⅈ́'α𝙩 ѕвѕ෴
❨ცıɠ ɠᵃ̨ι❩*©®-'Yᴀʀ 𝓢𝓲𝓭𝓲 ✍🏻*
▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬
Jσเɳ ɱε σɳ ωαƭƭρα∂:@Bเɠ-ɠαℓ*🌹ℙaℊℰ❏☞7-8*
Kallon-kallo kowaccensu ta bi 'yar uwarta da shi, ya yin da wata bak'ar guguwa mai k'arfin gaske ta k'ara taso wa ji suke tamkar za ta k'washe su daga in da suke zaune, daddagewa kowaccensu ta rink'a yi suna k'ok'arin ruk'e juna.
Wa ta muguwar dariya da su ka rink'a ji yo wa me cike da kid'imewa, gami da kururruwa na kusanto su yasa su k'ara zare idanuwansu, musamman Halima wadda ba ta tab'a zuwa wajen ba sai a yanzu.
Ita kuwa Rumaisa da ke k'ara ma ce duk ta fi su rud'e wa da kid'imewa sabida abu ne wanda ba ta tab'a jinsa ko ganinsa a rayuwarta ba face a yanzu, kuka ne ya fara zuwar mata duk da ba ta san a inda ta ke ba.
Kafin k'iftawar ido sai ga wani mummunan mutum bak'i ya bayyana, fuskarsa cike ta ke da zane kala-kala na kowanne kalar fenti ban da tsagun da ke jikin fatar fuskarsa, zaune ya ke kan d'aya daga cikin shinfid'un da ke gaban bishiya me kogo.
Sai a lokacin k'arfin iskar da su ke ji ta fara raguwa tamkar ana janye ta ta na yin baya, hayaniya da kururuwar da ke kusanto su duk su ka rink'a ja baya, ji suke tamkar ana janye su, a hankali komai ya rink'a dai-daita tamkar wani abu bai faru a lokacin ba.
Boka Yankaru kenan, me kimanin shekaru hamsin da biyar ya yin da ya saki wata muguwar dariya me cike da d'imaucewar duk wani mai sauraronta, ya rink'a k'yak'yace wa da mahaukaciyar dariyar da ta cika ko ina.
Kallon su Halima ne ya koma ga wannan Boka, duk da cewa Halima a tsorace ta ke, ya yin da ita kuma Salma ta dake zuciyarta, tsoronta ya ja baya.
A tsorace Halima ta rink'a satar kallonsa, Rumaisa kuwa ji take tamkar ta rusa ihu sai dai kuma ba ta iya yin hakan ba ita ma ta danne zuciyarta, amma jikinta sai b'ari ya ke tamkar ana kad'a ma ta gangi, shuru suka yi suna sauraronsa bayan da ya gama kyakyace wa da mahaukaciyar dariya, sai kuma ya tsuke baki a lokaci guda ya yi shuru yana muzurai tamkar wani mahaukaci.
Nuni ya yi ga Halima tare da cewa "komai na ki ya iso gare mu ba ki da wata damuwa" nan ya k'ara jaddada ma ta maganar da dattijuwa ta yi ma ta tun a baya na cewar anan gaba za ta yi da ta sani, amma Halima ta ce ta ji ta gani ta kuma amince da duk abin da za a yi, ta ke Boka Yankaru ya kuma k'yak'yace wa da wata muguwar dariya ya juya ya kalli kogo, da sauri Halima ta ce "Na amince da duk abin da za a yi amma ba na son a kasheta inda...."
Da sauri ya dakatar da ita tun ba ta k'ara sa fad'ar abin da ta ke shirin furta wa ba, ta hanyar yi mata tsawa mai k'arfin gaske wadda ta sa har sai da suka tsorata gaba d'ayansu, sabida k'arfin muryarsa. Sannan ya ce "mu ne nan mu ke aiwatar da abin da ya dace, mu za mu yi aikinmu ba ke za ki fad'a mana abin da ya dace ba" ya k'ara shek'e wa da dariyar mugunta lokaci d'aya kuma ya tsuke bakinsa tamkar ba shi ya yi dariyar ba, Halima ta tsorata sosai dan haka ta ja baki ta yi shuru zuciyarta cike da tsoro ji take tamkar ta fashe.
Boka Yankaru kuwa hannayensa biyu ya d'aga sama, su Halima na kallonsa yana karanto wasu dalasanan tsafi ya yin da wani ruwa ya bayyana a gabansa me fad'i wanda daga wajen da su Halima su ke zaune suna iya hango cikin ruwan sai dai ba sa iya ganin abin da ya ke cikin ruwan. Wani makeken gida ne na alfarma me cike da k'awa, gefe guda kuma wani tsibirin dutse ne me tarin ciyayi, take Boka Yankaru ya tsorata ya k'ara fidda idanuwansa sosai yana kallon cikin ruwan, ya ci gaba da karanto wasu dalasanan sirrikan tsafi, bayan ya kammala ya shafa hannayensa a kan ruwan tare da wata muguwar dariya nan ta ke ruwan ya b'ace.
Ya kalli Salma da Halima ya ce "Za ku iya tafiya! za ku iya tafiya!!, yana fad'a yana maimaita wa da k'arfi, cikin 'yan dak'ik'u suka neme shi suka rasa ba tare da sanin inda ya nufa ba, ba shiri su ka mik'e tsaye, Halima ta rik'o hannun Rumaisa, ta ke suka ji yo wani k'ara mai k'arfi tamkar tsawa, dube-dube suka hau yi musamman Halima da yau shi ne zuwanta na farko, da sauri suka fara k'ok'arin barin wajen, ji suka yi tamkar suna tafiya a sararin samaniya, sai dai kuma ba su gansu a saman ba, kuma ba su ga suna tafiyar ba, sai dai wata hajijiya da suka rink'a ji, ya yin da suke ganin garin na juya wa.
Cikin k'ank'anin lokaci kamar k'iftawar ido suka daina jin duk wasu abubuwa da su ke ji, komai ya d'auke cak! garin ya dawo musu dai-dai, ba tare da sun yi tsamanin ganin hakan ba sai ga su a dab! da bakin titi wanda hakan ya yi matuk'ar bawa Halima mamaki.
Halima ta kasa yin shuru har sai da ta tambayi Salma "amma fa wannan Bokan yana da abubuwan ban mamaki da yawa a wajensa, na ga bai ba mu komai ba, ban kuma ji ya ce ga wani magani da za mu yi amfani da shi ba, kuma na ga ga shi mun dawo da Rumaisa, sannan kuma na ga daga mik'ewar mu har mun iso bakin titi, kai! gaskiya al'amarin bokan nan da ban mamaki, kuma kina ganin za a yi nasara, ba iya wad'annan abubuwan kawai ya iya ba na siddabaru?" ta k'arashe maganar da jinjina kai suna tafe suna hira.
Dariya Salma ta yi "hmm ai ki daina mamaki kin ganni nan ni kaina ba zuwana na farko kenan ba, na kai mutane da yawa wajensa, kuma sun ji dad'in aikinsa, shiyasa ma na ce miki ta wajensa ne kad'ai za mu iya samun nasarar da mu ke so, har yanzu ba na iya daina tsorata da wajen nan da kuma abubuwan da ya ke yi, kin san an ce tsoro halak ne ko?, toh! abin da ba ka san zai faru ba ka ga ya faru, ba ka yi tsammanin gani ba sai ka ganshi kin ga dole mutum ya tsorata.
Shi fa ba Boka bane irin wanda kika sani, ya girmi boka domin kuwa shi tsafi ya ke yi, shi matsafi ne, sai dai yana tafiyar da komai nasa tamkar irin na bokaye yanayin aikinsa ya bambanta da na sauran Bokaye, domin zai yi miki aiki ba tare da ya dank'a miki komai a hannu ba, kar ki yi mamakin cewa wannan aikin idan an ce miki har ya gama yinsa, ke dai kawai ki saka ido za ki sha mamaki na fad'a miki.
Kuma kin ga duk wanda ya zo muddin zai koma gida shi zai kawo mutum kan hanya shiyasa ma kika ganmu a hanya toh! shi ya kawo mu kan hanya" Halima ta jinjina kai sosai kafin ta ce "ni kaina ina mamaki, amma kuma ina tsoron wannan yarinyar kar ta sanar da komai?" ta yi nuni ga Rumaisa wadda ta galabaita sosai sabida yunwa.
Murmushi Salma ta fara yi kafin ta tambayeta cewa "ki fara ba ni labarin yadda kuka yi da Dattijuwa, tun ina gida na so ki sanar da ni" nan Halima ta kwashe labari kaf! ta zayyane wa Salma, ya yin da Salma ta k'ara wani murmushin bayan ta d'an yi jimm.. kad'an na wasu 'yan dak'ik'u sannan ta ce "Kar ki wani damu ni daman na san dole hakan ta faru"
Salma ta numfasa kafin ta ci gaba da cewa "Zan baki labarin komai game da dattijuwa da kuma shi wannan matsafin da mu ka je wajensa wato Boka Yankaru, na san za ki fi fahimtar komai ki kuma gasgata abin da na ke fad'a miki, yanzu kin ga yamma ta yi ko na ce magariba, dare ma za mu ce tun da kuwa kafin mu je gida duk da an rage mana hanya na san dai gari ya yi duhu, mu samu mu je gida zuwa gobe sai mu had'u, ga wannan yarinyar ma ta galab'aita sabida rashin abinci, zuwa goben zan sanar da ke komai", duk wannan maganar iya su kad'ai su ke yin ta ba tare da sun d'aga murya ba.
Ta na gama magana sai ga keken Napep kamar an je fo shi daga sama, nan take su ka tsayar da shi su ka shiga ciki ba tare da sun sanar da shi inda zai kai su ba, har sai bayan da su ka shiga ciki su ka zauna tukunna su ka sanar da shi inda zai kai su, ba tare da ya yi musu ba ya ja keken ya tafi.............✍🏻
*_𝐘𝐚𝐰𝐚𝐧 𝐂𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭 𝐘𝐚𝐰𝐚𝐧 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠.......👌🏻_*
🌹☞ℬıɠ ɠᗅ̨ι *¢ɛ✍🏻*
YOU ARE READING
BONONO...! [𝑹𝒖𝒇𝒆 𝑲'𝒐𝒇𝒂 𝒅𝒂 𝑩'𝒂𝒓𝒂𝒘𝒐]
Short StoryRayuwa mai cike da ban al'ajabi gami da hargitsi, ya yin da sharri ke juya wa ya koma wajen mai shi.