༺༻🌹༺༻
࿙꧁꧂꧁꧂࿚
֍*🇧ᝪN ᝪN ᝪ...!*
[𝑹𝒖𝒇𝒆 𝑲'𝒐𝒇𝒂 𝒅𝒂 𝑩'𝒂𝒓𝒂𝒘𝒐]࿙꧁꧂꧁꧂࿚
֍
༺༻🌹༺༻*Տᴛ⌾ℛℽ & ᗯℛⅈᴛᴛℰℕ*
*ɮ̋ʏ̋✍*
෴ℛαвⅈ́'α𝙩 ѕвѕ෴
❨ცıɠ ɠᵃ̨ι❩*©®-'Yᴀʀ 𝓢𝓲𝓭𝓲 ✍🏻*
▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬▬
Jσเɳ ɱε σɳ ωαƭƭρα∂:@Bเɠ-ɠαℓ𝐼𝑛 𝑠ℎ𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ𝑢 𝑤𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑙𝑖𝑡𝑡𝑎𝑓𝑖 𝑛𝑎 𝐵𝑂𝑁𝑂𝑁𝑂 𝑦𝑎 𝑑𝑎𝑤𝑜 𝑧𝑎𝑛 𝑐𝑖 𝑔𝑎𝑏𝑎 𝑑𝑎𝑔𝑎 𝑖𝑛 𝑑𝑎 𝑛𝑎 𝑡𝑠𝑎𝑦𝑎.
*🌹ℙaℊℰ❏☞3-4*
Tafiya suke amma Halima tunani take da wasi-wasi cikin zuciyarta game da yadda Tsohuwa ta iya gane su ba tare da ta jira ta yi ma ta bayanin komai ba. 'Toh! me yasa Laure ta ce in na je na sanar ma ta cewa ita ta turo ni, alhalin kuma ta san cewa matar za ta iya gane mu ko da kuwa ban yi mata bayanin komai ba?' tambayar da ta rink'a yi wa kanta kenan wadda ita kanta ba ta da amsarta.
Mamaki ne ya k'ara cika mata zuciya bayan da ta tuno yadda ta iya gane matsalolinta da gaggawa, da kuma isowarsu tamkar an sanar da ita, sai dai wani abin ban mamakin da Halima ta kasa fahimta wanda shi ma ya tsaya mata a zuciya har ta kai da tana tuna wa game da wannan tsohuwa shi ne; furucin da ta yi mata cewar ka da nan gaba ta zo ta yi da ta sani, 'toh! Dana sanin me zan yi?', ta fad'a a zuciyarta kafin ta tab'e baki.
Nan ta ke ta kawar da wannan tunani suka ci gaba da tafiya hannunta ruk'e da Rumaisa.
Waje ne a baud'e wanda ko mai basira sai ya yi da gasken gaske zai iya ganewa, k'wanonin sun yi yawan da mutum ba zai iya k'idaya yawansu ko kuma gane su a lokaci d'aya ba, ita kanta kawai tafiya ta ke ba tare da sanin hanyar da za ta b'ullar da su kan hanya ba, sai dai wani wajen takan kula ne da yadda shi me Keken 'Napep' ya taho da su amma ba wai dan ta gane hanyar ba, tun da ba waje ne da ta tab'a zuwa ko ta saba zuwansa ba. Har mamaki ta ke yadda shi me keken 'Napep' d'in ya iya gane kwatancen da ta yi masa, ta kuma yi mamakin yadda aka yi har ta iya ruk'e kwatancen da Laure ta yi mata ba tare da ta manta ba, cikin zuciyarta ta ce "Bar abin da kake muradi dole ka ruk'e".
Sun yi tafiyar k'afa mai nisan gaske kafin su iso wajen da za su iya samun abun hawa, sai a lokacin Halima ta k'ara gane cewa wajen ba k'aramin nisa ne da shi ba, dan dai a abin hawa kawai suke shiyasa a zuwa ba su ga nisansa sosai haka ba.
Rana kawai ake k'wallawa, Rumaisa kuwa layi kawai take kamar wadda za ta fad'i, da sauri Halima ta dubeta ta tallafota ta mik'ar da ita sosai "Rumaisa maza bud'e idonki kar ki ce za ki zauna ki huta dan ak'wai sauran tafiya a gaba" abin da take fad'a kenan wanda ita Rumaisan ba ta san ma tana yi ba.
Da k'yar ta ga wani me Keken 'Napep' ta tsayar da shi cikin hanzari ya dakata, sannan ta yi masa bayanin inda zai kai su, ba tare da b'ata lokaci ba ya ce su shiga nan ya ja abin hawansa ya fara tafiya.
☻☻☻☻☻
A can d'aya gefen kuwa wani Gida ne me k'aramin 'gate' daga waje, daga ciki kuwa yana d'auke da d'aki hud'u da falo guda d'aya wanda shi wannan falon sai ka shige shi za ka iya shiga kowanne d'aki na cikin gidan.
Ak'wai 'toilet' a kowanne d'aki bayan guda d'aya da yake waje, abin dai sai wanda ya gani, domin gida ne da ba za a ce an rasa ci ko sha ba, rufin asiri dai suna da shi.
YOU ARE READING
BONONO...! [𝑹𝒖𝒇𝒆 𝑲'𝒐𝒇𝒂 𝒅𝒂 𝑩'𝒂𝒓𝒂𝒘𝒐]
Historia CortaRayuwa mai cike da ban al'ajabi gami da hargitsi, ya yin da sharri ke juya wa ya koma wajen mai shi.